← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 64

Sashe 60

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cold shower ya sake kansa na tsawon lokaci har se da yaji ya koma daidai kafin faruwar abin, bathrobe É—in da ya cire ya sake maida wa kafin ya gimtse fuska ya fita dan ma kar ta ga fuskar dawo masa da abinda ya wuce.

Bata lura da yanayin fuskar sa ba ta shiga lissafa masa abubuwan da ta aika a siyo musu, da kai kawai ya amsa mata tambayar da tayi masa na ko hakan da tayi yayi daidai.

Be daɗe da fitowa ba matar da ta aika ta dawo ta kuwa miƙe da saurin ta ta nufi ƙofa with minding cewa towel ne kaɗai a jikin ta, bai san me yasa ba haka kuma be san tunanin da yake ba a lokacin da ya sha gaban ta cikin sauri yana faɗin ta koma shi ze amshi saƙon cikin kau da kai, ɗan tsai tayi cikin mamakin me ze sa ya hanata karɓar aiken se kuma ta matsa baya ta koma bakin bed ta zauna yayin da shikuma ya karɓo ledar ya zo ya ajiye mata a gaban ta kana ya sunkuya ya buɗe ya ɗebi nasa ya wuce toilet Dan shiryawa.

Itama nata ta fitar ta shiga sanyawa cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin kar ya fito bata gama ba, doguwar rigar bacci ce me ɗan kauri da ta kai mata gwiwa se wandon ta iya cinya, gaban madubi ta ƙarasa ta ɗau ɗaya daga cikin turaren dake wajen ta shiga fesawa a jikin ta duk da ba taste ɗin ta ba ne amma ta ji daɗin ƙamshin dan rabon ta da yi tun ranar da ta bar gida suka haɗu da wannan accident ɗin.

Fitowa yayi shima sanye da nasa kayan baccin, dogon wandon bacci da rigar sa me gajeran hannu, ba ƙaramin kyau kayan suka yi masa ba da har yasa Kisnah kasa janye idanun ta a kan sa ta shiga bin shi da kallo duk inda yayi, yana sane da kallon da take bin shi sedai yaƙi kallon inda take balle yace ta daina dan baya son kallon ta tun bayan kallon farko da yayi mata bisa kuskure lokacin da ya fito daga toilet ɗin, sosai tayi masa kyau sedai yana kallon ta incident ɗin ɗazu ne ya dawo idon sa shiyasa yake gujewa kallon ta.

Knocking ɗin da aka sake yi yasa ta kalli ƙofar sedai bata yi ko yunƙurin tashi ba, wannan karon ma shi yaje ya buɗe ya karɓi abinda bata san me ne ba dan rufe yake cikin leda, godiya yayi wa wanda ya kawo ya rufe ƙofar sannan ya dawo cikin ɗakin ya janyo Centre table ɗin dake ajiye ya ɗora ledar hannun sa kafin ya zauna bakin bed ɗin ta ɗaya side ɗin.

"Ki buÉ—e ki É—au abinci ki ci".

Iya abinda ya faɗa mata kenan ya tashi ya nufi wata kusurwa ta ɗakin tare da shinfiɗa daddumar da bata san inda ya samo mata ba ya tada sallah, buɗe ledar tayi ta ɗan leƙa take away biyu ta gani alamun ita ɗaya shima haka.

Nata ta ɗauka ta buɗe ta shiga ci tana lumshe ido, fried rice ce da aka wadata da veggies, da a da ne cewa zata yi taste ɗin abincin be mata ba dan a zahirin gaskiya ba wani daɗi ke gare ta ba sedai yanzu dake ta daɗe rabon ta da irin cimar se ta ji duk duniya ba abincin da yakai na gaban ta daɗi, sosai taci ta ƙoshi dan takeaway ɗin irin me biyun nan ne so abincin da yawa, tana gamawa ta far wa rabin gasasshiyar kazar dake kan abincin sannan ta kora ruwan roba, hamdala tayi ciki godiya ga Allah karo na farko a rayuwar ta, wani irin mutuwa jikin ta yayi taji ba abinda take buƙata a lokacin kamar bacci sedai sanin bata isa tayi shi batare da tayi sallah ba yasa bata ko kwatanta kwantawa ba ta jira har ya idar kafin ta ciri hijab ɗin dake cikin ledar wanda ita ta saka aka siyo shi ta hau kan pray mat ɗin ta tada Sallah.

Da wannan damar yayi amfani ya buɗe nasa pack ɗin abincin ya shiga ci a nutse, kamar yadda Kisnah taji like bata taɓa cikin n abincin da ya kai wannan daɗi ba shima haka, they spent good 3 months five days suna shan fura da nono se ko zogale da yaɗiya se kuma fruits sanda suka samu, to ba dole yanzu su having this feeling ba.

Ko kafin ya gama ci ta idar haka kuma ba wani azkhar ko tasbih ta cire hijab É—in ta bar shi a wajen dan tsananin baccin da ke rinjayar ta, can tsakiyar bed É—in ta haye tana sakin ajiyar zuciyar missing this kinda laushi da taushi da tayi ta shige blanket kafin ta iya ce masa good night.

Baya san abinda ze sa shi kallon ta balle har wancan ƙaddararren scene ɗin ya dinga dawo masa shiyasa be kalle ta ba balle yaga wajen da ta kwanta ya amsa mata da night kawai.

Se da ya gama cin abincin ya tattare wajen ya shiga toilet ya ɗauraye bakin sa ya fito ya nufi kwanciya sannan ya ga yadda ta raba gadon biyu ta kwanta a tsakiya, sororo ya tsaya yana kallon ta dan shi duk a tunanin sa ta ɗau blanket ne ta kwanta a ƙasa, rasa ma wane irin tunani ze yi yayi dan shima baccin yake ji gashi babu ko ƴar kujera a ɗakin balle ya kwanta, tsurar tiles ne a ƙasan se ɗan ƙaramin carpet a bakin gadon wanda ko ƙafar mutum huɗu baze ɗauka ba, haka dai yayi ƙarfin halin janye blanket ɗin da ta lulluɓa ya shimfiɗa a ƙasan ya kwanta sedai be ko yi mintuna goma ba ya miƙe jin kwanciyar ƙasan fa bazata yiwu ba saboda sanyin tiles ɗin ga blanket ɗin ba wani me kauri ba to a bikin da middle class hotel.

Sake kallon ta yayi kafin yayi ƙundunbala ya runtse idanun sa ya hau gadon yasa hannu ya tura ta one edge na gadon yana kiran Allah a ransa kamar wanda se taɓa aljana ko wata halittar daban.

Har wata ƴar ajiyar zuciya yayi ganin ya matsar da itan sannan shima ya kwanta can ɗaya edge ɗin gadon yana haɗe tafukan sa ya shiga karanta addu'ar bacci, yana gamawa ya shafe jikin sa gaba ɗaya sannan ya ɗan zura ƙafafun sa cikin blanket ɗin da ya maida mata, tsaki yayi ya miƙe ya zauna tare da karanto sabuwa addu'ar bacci sannan ya ɗan matsa kusa da ita kaɗan ya ɗaga blanket bayan ya rufe idanun sa ya tofa mata dan sam baze yi kuskuren kai hannu jikin ta wai shafa mata addu'a ba.

Mintuna kaÉ—an kuwa bacci yayi gaba dashi shima, kiran farko na sallar asuba ya farka dan akwai masallacin gefen hotel É—in kasancewar gurin na musulmi, seda ya É—aura alwala kafin ya tashe ta ta hanyar bubbuga gefen gadon sannan ya fita, yana fita ta koma ta kwanta abinta har aka idar da Sallah ya dawo ya tadda ta haka, aikuwa toilet ya shiga ya É—ebo ruwa ya watsa mata, ta kuwa tashi a firgice tana zare ido, ganin sa tsaye kanta ya sa ta tashi da sauri dan zuwa toilet dan tasan dalilin hakan.

Tana alwala tana gungunin ya takura mata har ta fito sannan tayi shiru tare da É—aukar hijab É—in ta da yake kan daddumar da ta ajiye shi tun jiya ta tada Sallah.

Tana idarwa ta kuma neman gado, be hana ta ba dan yasan sun kwaso gajiyar da suke buƙatar baccin sedai shi baze samu damar yi ba dan yanzu haka ya tambayi ɗaya daga cikin securities na hotel ɗin inda ze samu ɗakin haya ya kuma sanar dashi ɗaki baze gagara ba a garin dan haka se haɗa shi da ɗaya daga cikin dillalan da ya sani ko za'a dace shine da ze fita anjima kaɗan.

Ƙarfe tara ya fita daga ɗakin yayinda har lokacin take kan barci, be tashe ba se kawai ya kulle ta ta waje bayan ya ajiye mata breakfast ɗin ta, gida kusan huɗu suka je da dillalin kafin a dace da samun wanda yake so wato mara mutane da yawa, ɗaki ne ɗaya sedai da ɗan girman sa haka kuma su uku ne a gidan ba kamar ragowar da ke da mutane sama da biyar ba, seda ya tabbatar wajen yayi masa sannan suka fita suka ƙara sa wajen P.O.S ya cire kuɗin hayar shekara dubu talatin da biyar ya biya shikuma ya bashi key ɗin.

Daga nan machine ya tare ya hau bayan ya faɗa masa ya kai shi nearby kasuwar robobi, suna zuwa ya sallame shi shikuma ya shiga siyan ƴan kayan robobi da yasan zasu iya buƙata, butoci, buckets, drum, cups, Parker and dustbin, mopper da broom dan tiles ne a ƙasan ɗakin.

Seda ya siya duk abinda yake ganin zasu nema na roba a wajen kafin ya biya kuɗin ya sami me napep ya ɗaukar masa ya kai gidan sannan ya kuma komawa kasuwar Kayan abinci nan ma ya siyan musu me ɗan yawa sannan ya biya ta ƴan katifu ya siya guda ɗaya ƙatuwa dan in yace ze siya biyu to ze ci ƙarfin kuɗin bankin nasa alhalin kuma yana son ya smai ɗan jarin yin sana'a.

Yana kai wa gidan ya koma hotel É—in ya É—auke ta dan ya samu tayi wanka ta karya tana kwance ne kawai, suna shiga tabi gidan da kallo a lokacin ne kuma mata É—aya da suka tarar ta fito suka gaisa sannan ta koma bayan ta faÉ—a musu É—ayar tayi tafiya amma gobe zata dawo.
Chapter 60 · 0% Book details