← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 64

Sashe 24

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

________________________📖 Sallar Isha ya idar a masallaci amma be dawo ba se da ya gama duk tasbih ɗin da ya saba, fitowa yayi a hankali ya saka takalmin sa ya nufi komawa gidan yana me duba agogon hannun shi, its 8:45 pm.

Yana shiga compound wayar da aka kawo masa É—azu me kyau da ita madaidaiciyar Android kamfanin Samsung matsayin wayar da ake bawa kowane ma'aikaci da sim da komai ta fara ringing, É—an kallon screen É—in yayi kafin yai sliding ya amsa

"Ya Saraki ka fito da motar gani nan fitowa"

"Okay" yace yana ending call ɗin tare da ƙarasawa ɗakin sa ya ɗauki key ɗin motar da kuma kuɗin da ta bashi ɗazu dan yana son yin siyayya.
Warming up motar yayi kafin ya matsa da ita kusa da flat É—in nasu ya kashe yana jiran fitowar ta.

Cikin wata dark blue ɗin guntuwar gown iya ƙasan gwiwa kaɗan ta fito, rigar tasha adon silver stones masu matuƙar kyau se ɗaukar ido take tana walwali, gashin kanta parke cikin blue ribbon se ta sake shi ta baya kana ta ɗora p-cap akai, kyakkyawar farar ƙafarta kuwa sanye take cikin dogon blue Hill shoe da igiyoyin sa suka kai har kusan rabin ƙaurin ta, kyawawan hannun ta saye da agogo shima dari blue se ɗayan da ta sakawa siririyar sarƙar hannu ta kuma ƙawata yatsun ta da zobuna.

Tun da ta fito ƙamshin ta ya cika ko ina a harabar gidan har ya kai ga hancin Saraki da ya saukar da glass ɗin side ɗin sa, girgiza kai kawai yayi yana mata addu'ar shiriya dan tabbas saka irin waɗannan turaren dole ya haddasa fitina a ban ƙasa.

Tun a ɗazu da ta kira shi da Ya Saraki yaji wani irin abu ya tsarga masa, ba abun da yazo ransa a lokacin face ƙanwar sa ɗaya tilo da ita kaɗai ce mace dake kiran sa da sunan, hakan yasa yaji a ransa kamar ita ɗin ce ta kira shi sedai yasan ba itan bace, tun a lokacin yaji a ransa wata ƙanwar ce ya samu, ƙani, ƙanwa, yaya mace, wa namiji kai har ma iyaye ana iya samun su a duniya base wanda kake da blood relation ne kaɗai family ba, a hadisai da ayoyi da dama Allah da Manzon sa sun nuna mana so da ƙaunar juna, sun nuna mana duk wani musulmi ɗan uwan musulmi ne dan haka ya amshe ta as ƙanwa kamar Miemie da suka fito ciki ɗaya da baze iya barin any harm yaje gate ta ba, haka baze so yaga rayuwar ta ta lalace ba, he'll treat her as an elder brother that will protect his little sister ko ta wane hali sedai yasan for now ba komai zece dole ze yi magana kan se ta gyara ba dan abun ya riga ya shiga jikin ta da dole se an bi a hankali.

Cikin wannan tunanin yayi nisa da har be san ma ta ƙara so har ta shiga ba se da ta bubbuga bayan kujerar da yake kai tana kiran sunan sa

"Yaa Saraki mana, am late fa".

BuÉ—e ido yayi a kanta kafin ya bi shigar jikin ta da ido sannan ya janye ya maida fuskar ta da ba wata kwalliya banda lip balm se mascara da eyeliner, kauda Kai yayi ya maida gaban motar yasa hannu ya kunna sannan ya nufi gate suka fice, seda suka hau titi sosai kafin ya É—an kalle ta a kaikaice

"Zaki makara? Makaranta zaki je?".

"Wane irin makaranta a wannan late hours É—in, clear screen cinema za muje".

Jijjiga kai kawai yayi ganin bata ma fahimci baƙar magana ya faɗa mata ba, be kuma cewa komai ba har suka ƙarasa, be shiga parking lot ba ya tsaya a gefe kaɗan da gurin dan fita yake son yi

"Ya ka tsaya a nan, kaga fa zan daÉ—e kawai ka shigar da ita parking lot kar muyi blocking wasu".

Hakan da ta faÉ—a se ya tuna mata dasu Abeed da gaba É—aya ta manta da batun su wanda ta san for sure suna nan a kulle dan in har bata sake su ba ba wanda ya isa yasa a sake su, dole yau insha Allah zata sa a sake su dan badan ta manta ba da tun kwana uku da ka masu zata sa ayi freeing din su.

"Zan je Mall in dawo, ko ba daÉ—ewa zaku yi ba?". Ya faÉ—a mata

"Gaskiya zamu daɗe ina tunanin ma se to 1 Film ɗin ze ƙare, kasan fa Film biyu zan kalla, Film ɗin sharukhan me suna Ra one se kuma na Ajay devgan shikuma sunan sa Action Jackson".

Yadda take maganar cikin farin ciki ze shaida maka she drive pleasure talking about Hindu films talkless of watching it.

"You enter, Bari inje in dawo".

"Safe drive". Ta faɗa tana fita daga motar bayan ta buɗe safe ɗin ciki ta ɗau ledar crackers biyu, juya motar yayi ya fita daga cinema ɗin yana bin titi hopping to see a nearby Mall dan baya so yayi nisa, wani madaidaicin mall da ya gano yasa ya ƙarasa yai parking tare da shiga, ɓangaren takalma ya fara shiga ya zaɓi masu kyau guda biyar kafin ya koma ɓangaren turare nan ma ya zaɓi madaidaita dan wanda yake amfani dashi da is worth 350k duk ɗaya shiyasa yanzu sedai manage.

Kayan ƙamshin toilet ya siya ya haɗa kafin ya siya sabulan wanka da mayukan kai, a taƙaice dai 2k ce kawai tai ragowar cikin 100k ɗin da ya fito da ita.

Payment yayi aka masa bagging kayan security suka kai masa mota ya shiga ya koma cinema, Yana yin parking ya duba watch É—in sa only to see 9:50, he's wandering how he'll be waiting cikin mota har to one kamar yadda tace.

Rufe glassan yayi gaba ɗaya kafin ya ƙure ƙarfin Ac ɗin motar ya saukar da kujerar sa baya ya kwanta sosai bayan yayi connecting wayar sa da Bluetooth ɗin motar ya saka karatun Alkur'ani mai girma in low tune, tun yana bin karatun har bacci ya sace shi .

A can cikin cinema kuwa kallo suke yi hankali kwance oganniya a tsakiyar da'ira tana taunar crackers ɗin ta har aka kusa gamawa aka zo waƙar kusan ƙarshe, sedai me tace bata san zance ba lokacin da waƙar ta ƙare ai se a dawo da ita baya ta kuma kalla, kusan gaba ɗaya mutanen wajen sukai mata caaa kamar zasu cinye ta da baki suna faɗin bata isa ba suna da abun yi, sosai in charge ɗin cinemar hankalin sa ya tashi dan yana samu da Kisnah ba kaɗan ba ga kuma ƴan kallo da suka customers ɗin sa ne, ko da aka kira shi rarraba ido ya hau yi tsakanin su dan be san side ɗin wa ze ɗauka ba.

"500k". Kisnah ta faÉ—a as the sum da zata biya in aka maida mata baya, da sauri wani matashi yace

"1mil".

"2 mil". Ita ma ta faÉ—a, shiru wancan yayi se wani É—an magidanci da ya tashi da sauri

"2.5 mil". Ya faÉ—a ganin yadda wancan yayi shiru

"3 mil". Ganin kowa yayi shiru alamun ya sallama yasa dole aka maida mata baya ta kuwa miƙe ta hau cashe rawar ta ba tare da ta damu da mutanen dake wajen ba, wayar ta ta miƙawa Meenah tace tayi wa managern wajen transfer ɗin 3 million ɗin sa shikuwa se washe baki yake cikin farin ciki, irin haka na cikin dalilan da yasa suke son zuwan Kisnah wajen.

Ana gama Ra one aka fara Action Jackson, kamar dai yadda ta faÉ—a basu tashi ba se five mins after one, ita kanta a lokacin a gajiya take sedai tana cike da farin cikin kallon da tayi da ma na sa'insar da suka yi da mutanen.

"Amma Kisnah 3 million sabida kawai maimaita kallon waƙar 5 minutes? Haba this is way too much".

Hameedah fa ta fara kaita ƙarshe da iskancin da take mata fa, bata manta jiya yadda ta ringa kushe Ya Saraki ba har da wani kiran shi mere driver, dole ma ta taka mata birki wallahi.

Ƙanƙance golden brown eyes ɗin ta tayi cikin duban Hameedah

"Meke damuwar ki da rayuwa ta ne Meedah, batun yau ba fa kike min shisshigi da rainin hankali ba, ko dan kinga ina ƙyale ki shiyasa kika sami guts ɗin faɗa min kowace banzar magana tazo bakin ki, yanzu da na biya 3 million nawa kika cika min, nawa nai maula ina kuka Hajiya Hameedah me kuɗi taji tausayi na ta bani na cika, kin san i hate nonsense ko, to wallahi tun yanzu ki shiga hankalin ki dan ina raga miki ne being my friend if not ke in an ce kiyi dering Kisnah You won't even start, mtsww".

Da sauri Leekha da Meenah suka fara bata haƙuri yayinda baƙin ciki da ɓaci rai ya cika Hameedah, ganin ta dan Kisnah ta fisu kuɗi da kyau yasa take musu rashin mutunci yadda ta ga dama sedai ba yadda zata yi haka ta bata haƙuri itama kafin ta juya wajen motar ta tashi ga ta wuce gida.

Tsaki Kisnah ta raka bayan motar Hameedah dashi kafin ta É—agawa su Meenah hannu alamun bye, da sauri Leekha ta tare ta

"Amma dai zaki wajen Surry gobe ko, kinga duk yau baki leƙa ta ba".

"Munyi waya da ita É—azu kin san tana da fahimta so i brief her about that assignment, dole ba inda zani gobe saboda wuni zanyi kan shi in gani in Allah zesa in iya yi".

"Hakane, Allah ya sa ki iya É—in".

"Ameen bye, Meenah ki gaida Momma, Leekha ki gaida Adda".

"Za su ji insha Allah, sweet dreams Queen".

Murmushi ta sake musu kafin ta ƙarasa wajen motar ta, knocking tayi ta ji shiru, ta sake yi nan ma shiru, wannan karon dagewa tayi ta ƙwanƙwasa da ƙarfi da yasa Saraki farkawa daga baccin da yake yi da ba wani daɗin sa yake ji ba dan a takure yake.

Zama yayi sosai hana gyara rigar jikin sa da ta tattare kafin yayi unlocking motar yana tada kujerar da ya kwantar, jin ƙarar buɗewa yasa ta buɗe murfin ta shiga tana faɗin "sannu". Which he answered using body language.
Chapter 24 · 0% Book details