← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 64

Sashe 22

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fita tayi daga motar ta tsaya jikin ƙofar dake buɗe har lokacin tana facing su Hameedah dake tsaye kusa da ita, congratulations suka shiga yiwa juna na sauƙin da test ɗin ta musu kafin suka dinga thanking ɗin ta, murmushi kawai take musu batare da ta amsa ba dan tana cikin damuwa sosai, Meenah ce ta fara lura da hakan ta matsa sosai ta ruƙo hannun ta

"Kina cikin damuwa Kissy I can read it on your face, me ke damun ki pls".

ÆŠan ajiyar zuciya ta sauke tana sake danne raunin ta

"Kema kin sani, me ze sani damuwa bayan CON005, wallahi har yanzu na kasa fitar da assignment ɗin nan, dama na daɗe da sanin malamin nan ya tsane ni shiyasa ya tsiro da Wannan assignment ɗin ɗan ya samu damar laƙabin carryover, ko Baki ji wai shine matsayin C.A da test gaba ɗaya ba?".

"Nikaina na kasa gane damuwar malamin nan da ke Kisnah, amma me ze Hana kiyiwa Deen magana nasan dole ze saka ya fita hanyar ki".

"Bana buƙatar connection a karatuna Leekha, I want to earn my certificate with my brain ba money ba, Dan haka ba wanda zan faɗa wa, Allah See's everything and will surely give me a way out".

"Then Goodluck Mrs brain". Hameedah ta faɗa kamar cikin wasa but cike da isgilanci da farin cikin yau dai ta ƙarewa uwar iyayin basira, murmushi kawai Kisnah tayi dan ba tun yau ba tasan Hameedah is jealous of her sedai bata damu ba dan tasan tuni ta yiwa Hameedar zarra nesa ba kusa ba.

"Hope you guys duk kun gama naku?".

"Just some little corrections". Meenah ta faÉ—a
"Already finished". Leekha itama ta faÉ—a
"Since yesterday". Inji Hameedah, gyaÉ—a kai Kisnah tayi kafin ta juya dan shiga mota
Wy
"Wish all of you success, will be going, see you tonight a cinema".

"See yha dear, byee". Suka haɗa baki wajen faɗa, ita kuma tai  ya nasu tare da rufe murfin tana gyara zama.

'So wannan ce damuwar ta kuma the reason behind her tears, so this is how she loved her studies, he pray she get an alternative, ko ba komai she's doing good here'.

Tashin motar yayi tare da yin reverse ya fice daga makarantar haka ma Meenah da Leekha Hameedah kuma tace she get something to do..............✍️

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 15 (8/7/2022 9:41 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                         Page 1️⃣5️⃣

_______________________📖 "Kai ni K&S drinks".
"You show me the way". Nodding tayi ta shiga nuna masa hanya har suka ƙarasa, horn yayi security dake bakin gate suka fito dressed in blue black uniform of theirs, ko da sun ga motar tace basu fasa checking ɗin motar ba sannan aka basu hanya suka wuce first gate, ko a second and third gate ma seda aka sake duba su kafin a basu hanya suka wuce.

Ƙaton building ne da girman sa ya zarce misali da ba ma zan iya misalta shi ba, just ku auno shi a idanun ku.

Da sauri ɗaya daga cikin securityn ya ƙaraso ya buɗe mata ƙofar ta fito sannan ya maida ya rufe ta tunkari main building ɗin Company ɗin.

A hankali Saraki ya juya ya dubi litattafan ta da ke ajiye kan seat É—in da ta tashi kafin ya sa hannu ya janyo su ya buÉ—e ya shiga dubawa, sannu a hankali yake bin rubutun yana karantawa kafin ya fara flipping through pages É—in, bin paper É—in da ta faÉ—o yayi da kallo kafin ya É—auka ya warware, question É—in assignment É—in da take batun ta kasa ce dan gashi nan bayan sunan ta, admission number, department, course code da kuma question bata rubuta komai ba,

Sunan ta ya koma sama yana maimaitawa cikin tunani to ya akayi ya canja ya koma Kisnah, to kodai nickname É—in ta ne Kisnah kamar yadda yaji ana kiranta?".

"Sakeenah Safwan".

Ya sake maimaita sunan kafin ya maida hankali kan question ɗin, ƙaramin cute smile ya saki ganin question ɗin ba wata me wahala bace amma har take kuka akai, kamar wanda ake controlling ya samu kan sa da ɗaukar pen ya ɗora kan plain sheet ɗin ya soma rubutu, sosai ya maida hankali kan rubutun da yake yi, seda ya cika plain sheet ɗin gaba da baya ya kuma zarar wata da ta ɓullo ta cikin textbook ɗin ta, wasa wasa seda ya cika plain sheet uku sannan ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya, bin rubutun yayi da ido yana karantawa har ya kai ƙarshe kafin ya ninke takardun ya maida mata cikin ƙaton exercise book ɗin ta kana ya cigaba da karanta textbook ɗin.

Sosai ta ɗauki lokaci supervising all the workers kafin ta fito dan tafiya gida cikin gamsuwa da aikin da suke yi, tun daga nesa da ya hango ta ya rufe littafin ya ajiye mata inda ya dauka tare da kunna motar, shigowa tayi tana karɓar file hannun ma'aikacin da ya rako ta dasu Sannan ta rufe ƙofar.

Jan motar yayi zuwa waje wanda a nan ma seda aka sake checking É—in motar tasu kafin bar su su wuce, yanzu kam gida suka yi yayi parking a lot É—in su ta fita, har ta fara tafiya se kuma ta tsaya har ya fito shima

"Kaje wajen Khamees me kula da ma'aikata ya nuna maka É—akin ka".

GyaÉ—a mata kai yayi taci gaba
"Help me with these files please, sun min yawa ga books again".

Karɓar files ɗin yayi a hannun ta ita kuma ta riƙe littattafan suka nufi ƙofar falo, yanzu kam ta tadda su Mommy har ma da ƙawayen ta biyu a falon gaban su cike da drinks da kayan snacks hakima Maigado a gefe riƙe da waya ta maƙala earpiece a kunnen ta, shiga tayi falon without excuse kamar yadda ta saba yayinda Saraki ya dakata bakin ƙofar yana jiran ta kai books ɗin hannun ta ta dawo ta karɓi files ɗin, jin bata ji takunsa a bayan ta ba yasa ta juyo ta dube shi yana tsaya ta masa izinin shiga

"Come in Mana, ya ka tsaya a nan".
Ɗan shiru yayi se kuma ya shiga thinking ta sanar da na ciki za'a shigo, shiru duk suka yi Mommy da ƙawayen ta suna binta da kallo har ta kai tsakiyan ɗakin tana niyyar ƙarasawa saman ta sannan ta juyo, ganin Saraki tsaye yasa ta dakata tare da dawowa kusa da ƙawayen Mommy

"Excuse me, join those two a three sitter É—in ki bashi wajen ya zauna, ya gaji so baze iya tsayuwar har na hau sama na sauko ba".

Sosai fuskar matar ya nuna ɓaci rai sedai kafin tayi magana Mommy tayi saurin tarar ta

"Haba Kisnah, ai se ya zauna a kan rug ko ko bashi ne sabon driver É—in ki ba?".

"Yes shine se aka yi yaya?".

"He supposed to wait outside, ba daraja bace ace muna zaune sama jere driver ma na zaune, its so disgracing, hakan ze iya sa ya dinga girman kai kalla fa ya shigo muna zaune amma ko gaida mu be yi ba".

"So sannu Nana, Nace sannu Nana Asma'u uwa ta, to yaƙi ya tsaya a wajen kinji akwai abinda zakiyi ne, kina wani maganar ba daraja bace to hell with the daraja, ke har wani daraja gare ki, to bari kiji wallahi Ya Saraki da kike magana akai ya fiki daraja nesa ba kusa ba ya kuma fiye min ke da duk abinda ya shafe ki so dubu, in bazaki iya zama inda yake ba You better pack your belongings and move back to where you return from dan nan gida nane bana gyatumin wani bane haka ba na mijin wata ba so I have the right nayi yadda naso a kuma lokacin da naso, da zaki wani ce be gaishe ku ba to ya gaida ku yace ya gaida wa, gayyar munafukai?, Mtsww, Ya Saraki have a seat please".

Ta ƙarashe looking at Saraki da har lokacin ke tsaye, without saying a single word ya zauna inda waccan ta tashin bisa dole, farko be yi niyyar zama ba sedai kalaman Mommy kan shi yasa yaji Yes se fa ya zauna duk da response ɗin da Kisnah ta mata ya burge shi sosai, dukkan su seda suka sake kallon shi lokacin da yakai zaune, ba Mommy ba har Kisnah da Maigado da se lokacin ta ɗago kanta daga pressing phone ɗin da take.

Zama ne irin na cikakku Kuma gawurtattun ƴaƴan da jinin sarauta ke circulating through their veins, tsantsar izzar dake tare dashi da kwarjinin da zaman ya ƙara masa yasa duk suka kau da kansu a kanshi kusan a tare, juyawa tayi ta haye saman ta yayinda su Mommy duk sukai wani irin shiru kafin ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta ƙawayen ta na rufa mata baya.

Barin dannar wayar Maigado tayi ta maida full attention É—in ta kan Saraki da yake nan zaune idanun sa a lumshe, ko da be buÉ—e ido ba yana jin yawon idanu cikin jikin sa hakan yasa ya buÉ—e idanun towards direction É—in da yake jin gaze É—in, a bazata hakan ya zowa Maigado shiyasa har ya kamata dan bata tsammani ze buÉ—e ido lokacin ba, kallo É—aya yayi mata ya janye idanun sa ya sake lumshe su itama kuma da sauri ta maida naga kan waya sedai ta kasa cigaba da abinda take.
Chapter 22 · 0% Book details