← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 64

Sashe 52

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa tayi da sauri ta ƙarasa bukkar tare da shigewa dan tun ɗazu take cikin jimiamin rashin farkawar tasa kasancewar tun da suka zo ƙauyen ya farfaɗo bata taɓa ganin yayi nauyin bacci irin wannan ba.

Bata lura da kallon da yake mata ba ta ƙarasa gaban gadon karar da yake kwance ta kai zaune

"Yaa lafiya kuwa yau irin wannan bacci haka, Allah har kasa hankali na ya tashi".

Ko kallon ta be yi ba ya sake yin gyaran murya shi a dole yana neman arÉ—o

"Yaa arÉ—o fa baya nan, yau tun sassafe ya fita gona, ya shigo baka tashi ba so se ya tafi".

Se a lokacin ya kalle ta, arÉ—o baya nan to wa ze taimaka masa yau gashi yana son zagayawa dan fitsari yake ji saboda magungunan da baffa arÉ—o ya bashi ya sha a can da kuma wanda ya taho dasu yasha kafin ya kwanta.

"Bari in kawo maka ruwa kayi alwala se kayi sallah".

Ta faɗa tana miƙewa zata fita, da sauri ya tsayar da ita dan ji yake kamar marar sa zata yi bombing

"Zan yi fitsari tukunna". Tsayawa tayi tare da juyowa ta kalle shi, ze yi fitsari tabÉ—in, to ita yaya zata yi mishi ga baffa baya nan.

"Bari in faÉ—a wa Nenne in ji ko za'a sami wani da zai taimaka maka to".

Wani banzan kallo ya watsa mata jin wani wai se ya tsaya an samo wanda ze taimaka masa, kawai tace so take ya saki fitsarin a nan mana

"Malama in zaki zo ki taimaka min na je bayi ki zo in Kuma ba so kike na sake shi a jiki na ba, salon gulma kawai".

Dariya ce ta ciyo ta ba kaɗan ba ganin yadda yake magana yana ɓaɓɓata fuska at the same time yana mutsu mustu da alamu dai da gaske fitsarin ya matse shin.
Gaban gadon ta matsa tare da miƙa masa hannun ta, se ya gama hararar hannun kafin ya kama da nashi ya fara ƙoƙarin miƙewa ita kuma ta saka ɗayan hannun ta tallafe nasa me ciwon, da ƙyar ya samu ya iya miƙewa dan ba wani ƙwari gare ta ba har kusan faɗo masa tayi.

A hankali yake taka ƙafar sa me ciwon yana bada ƙarfin sa ga mara ciwon ita kuma ta saƙalo hannun ta a ƙugun sa yasa hannun sa me lafiya ya zagaye wuyan ta har suka ƙara sa wani ɗan ƙaramin sabon makewayin da aka yi musu shi jiya wanda duk aikin baffa arɗo ne, ba kamar nasu arɗo ba nasu ginin jar ƙasa ne gaba ɗaya se asabarin da aka rufe saman dashi haka kuma a gefen bukkar su aka yi shi da ke da ɗan nisa da tasu Nenne.

Se da ta shigar dashi banɗakin kafin ta fita bayan ya zauna kan wani ƙaton dutse dake ciki sannan ta koma ta zubo masa ruwa a gwangwani ta tura masa ta koma gefe tana jiran sa.

ÆŠan gyaran muryar da yayi ya shaida mata ya gama dan haka ta shiga ta kama shi suka fito se wani hahhaÉ—e rai yake kamar wanda aka doka ko aka zage shi, se da ya zauna sosai kan gadon sa kafin ta kalle shi cikin tsokana

"Yaa ya Zamuyi ina kashi ya matse ka kuma baffa baya nan?".

Ta faɗa tana saka yatsa a baki irin wai tana tunanin kamar dai yadda yara suke yi, kunya ce ta kama Saraki ganin yadda yarinya ƙarama take neman raina shi, dariya tayi ganin yadda ya sake matse fuska kafin kuma ta haɗiye kayar ta saboda mugun kallon da ya jefa mata

"Am sorry Yaa, Kai ne kake ta wani haÉ—e rai bayan fitsari kawai kayi kuma ai nima ina yi ba, to meye abin ma damuwar bari in kawo maka ruwan alwalar".

Tana faÉ—a ta fice da sauri fuskar ta É—auke da murmushi dan Allah ya sani ya bata dariya ba kaÉ—an ba.

Inda yake zaune ta kawo ƙatuwar ƙwaryar da yake alwala a ciki tare da wani gwangwanin cike da ruwa, a hankali ya matsa bakin gadon ya tara hannun sa ta shiga zuba masa ruwan yana alwala, yana gamawa ta ɗauka ta fice dashi ta zubar kana ta dawo ɗakin, ganin yana Sallah ta juya ta fita wajen Nenne.

Ko zama bata yi ba Nenne ta tura mata madaidaiciyar ƙwarya rufe da faifai tare da mata alamun ta kaiwa Saraki, ɗauka tayi ta koma bukkar su inda ta tarar ya idar yana zaune yana azkhar, ajiye masa tayi tare da neman guri ta zauna nan kusa da shi, tana zaune ya ƙarasa azkhar ɗin tare da yin addu'a sannan ya dube ta

"Meye kuma?".

Da ido ta nuna masa ƙwaryar da ta ajiye a gefen sa

"Nenne tace in kawo maka".

"Bakin kawo ba, to me kuma kika tsaya jira".

Kwaɓe fuska tayi tana fatan Allah yasa ya yarda dan ita fa bata ƙoshi ba, su Fulani haka suke da ƙauron hannu, ƴar fura da nonon ma da za'a bata ba za'a bata a wadace ba kamar ta wani roƙa.

"Rage min zaka yi Please Yaa, Allah Ni kam ban ƙoshi ba".

Bece mata komai ba ya miƙa hannun sa na hagu da yake da lafiya ya ɗau ƙwaryar tare da buɗe wa ya ɗau ludayin ciki ya ɗebo ze Kai Baki se kuma.ya dakata yana kallon ƙwaryar da hannun sa, a jiye ludayin yayi ya zubawa furar ido kafin ya ɗago ya kalli Kisnah dake zaune tana bin shi da kallo, shi kam Allah ya jarrabe shi a kwanakin nan, hannun dama a karye ko da wanne ze ci abinci yau oho, dama arɗo ke zama ya bashi gashi kuma yau baya nan.

"Lafiya yaa, ko hannun ne yake ciwo?, Ka fama ƙafar ka ne?".

Ta jero masa tambayoyin ganin yadda ya tsaya yana kallon ƙwaryar hannun sa kamar me neman wani abu a ciki, be amsa ta ba se ƙwaryar da ya miƙa mata ta sa hannu ta karɓa kafin ta juyo Muryar sa very low

"Feed me". ÆŠan zaro ido tayi tana buÉ—e baki, ganin abinda yayi yasa shima ya zaro mata nasa kyawawan idanun

"Hannun dama na akwai ciwo I can't eat or drink with left hand, is haram in Islam, so Mrs is not as you think".
Ya ƙarashe yana tsuke baki kamar ƙaramin yaro abin kuwa ba ƙaramin burge Kisnah yayi ba, hannu ta sa ta dafe bakin preventing herself bursting into laughter.

GyaÉ—a kai tayi tare da É—aukar ludayin ta É—ebo furar tare da nufar bakin sa saying
"Haaa, oya buÉ—e bakin".

Seda ya harare ta kafin ya buÉ—e bakin sa ta saka masa ya shiga sha, É—ebo wa tayi ta kai bakin ta itama ta sha tana lumshe ido dan se taji kamar tasa ta fi daÉ—i kan wadda aka bata, sanin neman magana take yasa be ko kalle ta balle yayi mata maganar sha masa da take yi.

Haka suka cigaba da sha su biyu, in ta bashi ta bawa kanta har suka shanye kafin ta sa harshe ta lashe lips É—in ta, da sauri Saraki ya kawar da kai ganin abinda take yi ya nemo wani É—an tsumma a gefe ya goge bakin sa kafin ya jingina jikin jan bangon su.

Fita tayi da ƙwayar ta ajiye kana ta dawo da maganin sa da Nenne ta bata ta kawo masa, be yi musu ba ya karɓa yasha ya koma ya jingina yadda yake kafin ta kawo maganin ya rufe idanun sa ya shiga tunani, shikam ya gaji da zaman nan da yake yi waje ɗaya, gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa saboda zaman ga kuma son barin garin da yake yi saboda yanayin cimar su da kuma wajen zaman su, yasani ciwon jikin sa baya rasa nasaba da kwanciya kan gadon karar da yake yi kullum ga kuma wuni zaune waje ɗaya, taya jikin sa baze yi ciwo ba.

Abincin su, hmmm wani daban shima kenan, be ga laifin Kisnah ba da tace ba zata iya cin komai na cimar su ba se fura da nono wanda dama shi ne main food ɗin su, se ku ganyayyaki, zogale, rama, kai abubuwa dai da bai taɓa sanin akwai su ba balle ya san sunan su, bawai ya raina musu bane ba, ya sani suna iya ƙoƙarin su wajen kula dasu, ko ɗauko su da arɗo yayi wani abu ne dan a yadda yanzu duniya ta lalace ba kowa ne ze iya kasadar ɗaukar su ba batare da yasan ko su waye su ba, mugaye ne ko mutanen kirki, kawai dai basu saba da wanann yanayin rayuwar ba adopting ɗin shi cikin sauƙi abu ne me wuya a gare su, addu'ar sa ɗaya Allah ya bashi lafiya da gaggawa su bar garin dan ko a wajen shi ba'a samu matsala ba ya tabbatar a wajen ta se an samu.

Nauyin da yaji a ɓarin hangun sa yasa ya buɗe ido yana kai duban sa wajen, itace kwance a jikin sa kan ta a gefen kafaɗar sa ragowar jikin ta kan gadon shi tana bacci, sosai yake mamakin saurin baccin da take yi yanzu sedai daga baya ya dena, to in bata yi bacci ba me zata yi, ita ba waya ba balle ta danna, ita ba abokin fira ba gashi tun jiya ya gargaɗe ta da kar ta kuma fita, dole kuwa ta yi bacci ai.

Zame ta yayi ya kwantar ya cigaba da tunanin sa har be san lokacin da shima baccin ya É—auke shi ba.

Muryar Nenne dake ta magana a bakin ƙafa ya farkar dashi dan bashi da nauyin bacci, motsawa yayi yana gyara zaman sa tare da yamutsa fuska jin hannun ya sake saboda nauyin da ya bashi da yana bacci, gyaran murya yayi saboda har lokacin Nenne bata dena magana ba, ajiye kwanon hannun ta tayi tana faɗin

"Nashe ga nan abinshin ku bakin danga".

Da toh ya amsa mata dan ya gane me take son cewa, ga abincin su nan a bakin ƙafa, hannu yasa ya shiga bubbuga kafaɗar Kisnah dake kwance dan taje ta ɗauko kwanon da Nennen ta ajiye, buɗe idanun ta da suka sauya kala saboda bacci tayi a kansa tana bin sa da su dan son jin dalilin tashin ta
Chapter 52 · 0% Book details