← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 64

Sashe 61

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka shiga gyaran ɗakin bayan ya share ita kuma tayi mopping duk da ba wai yayi bane dan bata wani iya ba, ba laifi ɗakin yayi kyau sedai babu labule babu kuma risho ko gas na girki haka babu kayan plates da spoon ga uwa uba kuma tukunyar da food flask, dole yace ta Masa list ɗin abin da babu ta kuwa yi bayan ta aro pen da paper wajen matar gidan ta tace sunan ta Saudah, haka ya karɓi list ɗin ya kuma fita siyowa ita kuma ta zauna tana bin ɗakin da kallo cikin jin haushin rashin toilet a ciki, gidan madaidaici ne da ke da soro biyu babba da ƙarami se tsakar gida me ɗan faɗi, kitchen a gefen dama se toilet a kusa da ƙofar shigowa se kuma nasu ɗakunan da ke jere sedai da ɗan tazara kaɗan tsakanin ƙofofin su kasancewar ɗakunan da girman su, daga jikin ɗakin Kisnah akwai ɗan ƙaramin corridor da tun da ta ganshi tasa a ranta nan zasu ajiye kayan ruwan su.

Be dawo ba se yamma suka kuma shiga gaganiyar saka curtains É—in masu matsakaicin tsada se dai suna da kyan su ba laifi.

Yana gamawa yace ta sa masa ruwan ɗumi a ƙaramin gas ɗin su me kai uku da ya siyo fitar sa ta ƙarshe yayi wanka, bata ƙi ba ta fita ta cika ɗaya daga cikin sababbin pots ɗin d aya siyo da ruwa ta matsa dan kunna gas sedai yaƙi kamawa, da ta gaji se kawai ta koma ɗakin ta faɗa masa yaƙi kamawa, seda ya fito ya gwada mata yadda ake kunnawa sannan ta gane akwai banbanci da nasu na gida...................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, Comment and share fisabilillah.

Ouummey 40 (7/28/2022 3:05 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 4️⃣0️⃣

_______________________📖 Ruwan na tafasa ta shiga ƙoƙarin juye shi cikin bucket sedai ta kasa kuma bata san kiran shi dan taga yadda ya gaji sosai, tana ta kokawa da tukunya har ruwan ya zubo mata a ƙafa bata lura ba se zafin da taji ya ratsa kwanyar ta, ai ba tasan sanda ta saki tukunyar da ta ɗauka ba tana sakin ihu at the same time, a gigice ta fito daga ɗaki jin ihun ta haka ma maƙociyar ta saudah, inda take durƙushe riƙe da ƙafar ya ƙarasa da sauri tare da kaiwa tsugunne yana ƙoƙarin riƙo ƙafar tata dan ko be tambaya ba tukunyar da ta faɗi can gefe da kuma ruwan da suke malale a ƙasa ya shaida masa abinda ya faru, fatan sa Allah yasa ba ta ƙone sosai ba.

Se da ƙyar ta cire hannun ta daga kan ƙafar da tayi jaa sosai na azaba, hawaye kawai take yi dan ko sautin kukan babu dan bata taɓa cin karo da irin wannan azabar ba a kaf rayuwar ta se yau, gefe saudah ta tsaya tana mata sannun da bata iya ta amsa ba se Saraki ne ya amsa mata kafin ya tayar da Kisnah tsaye ya saka a gefen jikin sa suka shige ɗakin su.

Duk da suna cikin tashin hankalin ƙonewar da tayi amma hakan be hana wani baƙon yanayin kasancewar Kisnah cikin jikin sa ziyartar sa ba sedai be maida hankali ga hakan ba buƙatarsa kawai ya zaunar da ita ya duba mata ƙafar, Allah ya taƙai ta dan fatar bata tashi ba sedai ƙafar da ta yi jajur, duk da gajiyar jikin sa haka ya kuma miƙewa ya fita yaje ya siyo mata ointment da zata shafawa wajen da kuma pain killers da zata sha dan kashe zugin.

Kallon sa take yi tana jin wani shauƙi da farin ciki ganin sa duƙe gaban ta yana shafa mata ointment ɗin a ƙafar ta cikin kulawa da takatsantsan, tausayin sa ne ya kama ta ganin duk yau be zauna yana ta zirga zirgar ganin komai nasu ya kammala, wankan da ze yi yaji daɗi ma be samu ba ga abin da ya faru, duk se taji tana jin haushin kanta, yanzu da tana shiga kitchen sosai ai da ta iya juye ruwan zafi da kuma bata ƙara sashi ya wahala ba.

Yana gama shafa mata ya ajiye man ya ɗau pain killers ɗin ya miƙa mata biyu, dafe gaban kansa yayi tuno ba ma su da ruwan da zata sha maganin, suna da ruwa a drum ɗin su da ya kira me ruwa ya zuba musu sedai yasan baze yiwu ta sha magani da shi ba, to amma ai a Bina ruwan da suke sha wannan sedai a kira shi ruwan roba a kan sa, tuno hakan yasa ya miƙe ya ɗau cup ɗaya cikin kayan su ya fita ya wanke sannan ya zubo mata ruwan a cikin sa ya dawo, bata yi musu ba ta karɓa duk da tsanar da take wa magani amma haka ta rufe ido ta shanye dan bata san ƙara masa wani gajiyar na ƙin shan maganin ta kan wadda take tattare dashi.

Ajiye cup ɗin yayi a gefe ya fita wajen da incident ɗin ya faru ya tarar har saudah ta gyara wajen ta ajiye musu tukunyar a gefe haka ta goge wajen, godiya yayi mata a ransa sannan ya kuma zuba wani ruwan ya ɗora da kansa, ruwan na tafasa ya juye ya sirka ya kai toilet ɗin, tsayawa yayi yana kallon toilet ɗin cikin ɗan ƙyanƙyami dan a rayuwar sa yaƙi jinin toilet mara inganci, a ganin shi gwara toilet ɗin su na Bina dan shi ƙasa ce haka kuma da kansa yake gyara shi kullum so biyu a rana kuma hankalin sa a kwance yake sanin su biyu kawai ke amfani dashi akasin wannan.

Sam ji yayi baze iya shiga ba se kawai ya ɗau bucket ɗin ya maida ƙofar ɗakin su ya shige tare da zama kan katifar su nesa da inda take zaune.

Bata kawo komai ba ganin ya zauna a tunanin ta someone is using the bathroom shine yake jira sedai ganin har ya fara bacci yasa ta bubbuga katifar tana kiran sunan sa

"Baccin ai ze fi daÉ—i in kayi wankan, nasan ma zuwa yanzu na cikin toilet É—in ya fito".

"Na fasa". Cikin mamaki ta dube shi cikin son dalilin fasawar

"Amma saboda me, kalla fa ka gaji da yawa You need to take  a warm bath se ka fi jin daɗin jikin ka, ko kuma dan incident ɗin da ya faru ɗazu ne, kayi haƙuri Please Allah ban iya bane amma naga yanda kayi and next time zan yi daidai, an sorry please".

"The toilet is not clean". Ya bata amsa yana lumshe idanun sa, bata ce masa komai ba se miƙewa da tayi ta ƙarasa inda ya ajiye musu detergents da su toilet wash da ya siyo musu ta ɗau robar wasu ɗin, disinfectant da kuma toilet freshener ta fita, be san ta fita dan baccin da ya fara ya ci ƙarfin sa.

Duk yadda take jin zafin taka ƙafar haka ta daure dan bazata iya kallon shi ya zauna da tarin gajiyar da yake ciki ba bayan all he's going through is because of her, Kai abubuwan hannun ta tayi ta ajiye gefen toilet ɗin kaɗan sannan ta koma corridor ɗin da drums ɗin su ke ajiye ta ɗau empty bucket ta zuba ruwa sosai ta fara ƙoƙarin ɗauka sedai nauyin da ta ji yasa ta ajiye tana yarfe hannun ta, kwaɓe fuska tayi dan all these are new to her, bata Saba da irin wannan rayuwar ba sedai bata jin zata fasa wanke toilet ɗin, da ƙyar ta iya kai bucket ɗin bakin door na toilet tana sauke numfashi tare da kallon palms ɗin ta da suka ɗan yi ja, numfashi ta sauke cikin faɗa wa kanta zata iya ta juya zuwa ɗakin su ta ɗauko daya daga cikin brooms ɗin da ya siyo ta ɗauko me ƙwari ta jujjuya a hannun ta (tsintsiyar kwakwa), banɗakin ta koma ta tura ƙofar, yamutsa fuska tayi itama dan itama ta ga rashin clear ɗin da ya faɗa, tunani take ta ina zata fara wanke wa se kuma tunanin kar ta ɗebi germs a kayan ta yasa ta ajiye broom ɗin ta tsugunna ta tattare ƙasa wandon fakistan ɗin jikin ta har zuwa kusa da gwiwar ta sannan ta ɗaure rigar a ƙugun ta se kuma ta tsaya kallon broom ɗin kamar zata fashe da kuka dan siri sirin saman ta san baze iya wanke toilet ɗin nan ya fita ba.

Saudah dake tsaye ta window ɗin ta tana kallon ta ce ta fito kamar zata yi wani abu, motsin ta yasa Kisnah kallon wajen suka haɗa ido se ta ɗan sake mata ƙaramin murmushi, maida mata saudah tayi tana ƙarasowa kusan ta

"Lafiya kike tsaye bakin banÉ—aki haka".

"Ehm ina son wanke toilet É—in ne but nasan wannan broom É—in won't clean anything, ya zan mata pls".

Ƴar dariya saudah tayi kafin ta shiga ɗakin ta ta fito da wata wuƙa kana ta karɓi tsintsiyar hannun Kisnah ta shiga datse ta a ranta tana mamakin yadda zata ce zata wanke toilet ɗin da bata ko daɗe da gama wanke shi ba, tana rage ta tana tambayar Kisnah yayi amma se tace a'a a sake datsewa har seda aka kai tsintsiyar kusan rabi kafin tace yayi mata ta karɓa tare da yiwa saudah godiya ta wuce toilet ɗin ita kuma saudan ta shiga gyara wajen .
Chapter 61 · 0% Book details