Sashe 47
Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Se lokacin ta saki wani Gwauron numfashi kafin a gigice ta kalli bayan su lokacin tazarar dake tsakanin su da babbar motar Ba wata me yawa bace, hannu na rawa ta shiga ƙoƙarin saka belt ɗin wanda se da ƙyar ta iya saka shi, aikuwa take ya ƙure gaba ɗaya speed ɗin motar ya shiga tsufa azababben gudu, fit fit haka motar take wucewa kamar walƙiya hakan yasa nan da nan suka yi wa babbar motar ɗan nisa duk da alamu ya nuna shima matuƙin ta ya ƙure nasa gudun, haka suka ringa shige dajijjika kamar ba zasu ƙare ba amma ba su da alamun tsayawa, to su tsaya yin me ma.
Zaro ido yayi cikin sabon tashin hankali lokacin da ya kula da tankar mai da ta tare titin da alamu ta lalace ne a tsakiyar hanya kuma be lura ba se da ya zo daf, cikin ɗimuwa ya shiga ƙoƙarin ganin ya tsayar da motar amma inaa taƙi tsayawa saboda mugun speed ɗin da ya ƙure, hasbunallah wani'imal wakeel kawai ya shiga maimaitawa dan ya tabbatar se sun haɗu da wannan tankar haka kuma da sauri ya sa hannu ya fisgo Kisnah cikin jikin shi ya rungume cikin son kare ta ko yaya ne.
Wani irin ƙara ce ta tashi lokacin da motar su ta daki wannan tankar haka kuma tayi baya kamar wadda aka tura da mugun gudu kafin ta shiga hantsilawa tayi gefen dajin dake Wajen, seda ta jujjuya sosai kafin ta tsaya, mintuna ƙalilan Saraki ya fara ƙoƙarin ganin ya fito daga motar cikin dauriya da son ganin mutanen cikin waccan motar basu iske su a wajen ba dan yasan yin hakan tamkar ƙarshen rayuwar su ne yazo.
Da ƙyar ya iya fita daga cikin motar kafin ya samu yin dabarar da murfin ɓangaren sa ya buɗe ya zaro Kisnah da take a sume jini na bin fuskar ta, kallon ta ya tsaya yi cikin tunanin yadda de yi da ita dan tabbas baya tantama hannun sa na dama a karye yake dan yana iya jin yadda yake masa lilo haka kuma yayi masa nauyi sosai, ƙarar dosowar babbar motar wajen su yasa da sauri ya saka hannun hagun sa ya ciciɓata da ƙyar ya saɓa ta a kafaɗar sa kafin ya shiga gudu da ita ta cikin duhun ciyayi da bishiyun gonar da suka faɗa, be ko yi wani nisa ba motar su ta kama da wuta hakan yasa ya dakata gami da juyowa ya kalle ta.
Yadda take ci da wuta ya saka shi furta alhamdulillah dan yasan ba dan rahamar Allah ba da tuni suna cikin motar yayinda wutar zata tashi ta cinye dukkan wata tsoka da ƙashi na jikin su.
Jin kamar sautin Muryar mutane yasa ya juya da sauri ya cigaba da tafiya da ita cikin tsananin dauriya dan ba ƙaramin jin jiki yayi ba, wani irin jiri jiri yake ji sanadin dokuwa da kan sa yayi lokacin da motar ke tumble sedai aka ce wai shi gudun ceton rai da ban ne wanda hakan ne yasa har yake iya daurewa dan ganin sun tserewa magautan su.
*****
Can ɓangaren ƴan hirer killers ɗin da kawu ya turo kuwa suna ƙarasowa gab da wannan tanka suka tsaya tare da firfitowa dan sun hango ta tunda nesa, wajen da motar su Kisnah ke ci da wuta suka ƙarasa don tabbatar da su ne ɗin ko wasu ne sedai number motar su dake kan ci da wuta ta tabbatar musu da sune dan ga tambarin KS nan dake bayan duk wata mota tata, duk da ganin motar na ci da wuta basu fasa bincika gonakin dake gefe gefen hanyar ba dan tabbatar da sun mutu basu sami kuɓuta ba.
Ganin basu ga wani alama dake nuna sun kuɓuta ba yasa suka koma motar su suka zauna har se da gaba ɗaya motar ta ƙone ƙurmus kafin suka juya bayan sun ɗauki hotunan motar lokacin da take kan ci, number motar da kuma lokacin da ta gama ƙonewa gaba ɗaya.
*******
Gudu sosai yayi kafin ya fara tafiya a hankali kan sa na juya masa saboda tsabar jirin da yake ɗiban sa, tun yana iya tafiya har ya kasa ya nemi ƙarƙashin wata bishiya da yake ganin ta dishi dishi ya kwantar da Kisnah tare da zama kusa da ita yana maida numfashi ɗai ɗai cikin tsananin azaba da jigata.
Da hannun sa me lafiya ya dafe kan sa da yake jin kamar ana masa ihu a ciki, tun yana gani dishi dishi har ganin sa ya É—auke gaba É—aya ya daina gani da fahimtar komai.
*********
A hankali ta fara buÉ—e idanun ta tana yi tana rufewa tare da buÉ—e wa saboda yadda take gani uku uku har ganin ta ya daidai ta.
Cikin mamaki take bin wajen da take kwance da kallo, jar ƙasa ce sosai akayi ginin da ita dan gata nan a fili ana iya ganin ta, haba ɗaya ginin da akayi da ita be fi kamu biyar ba se kuma wasu karare ko yayi zata ce ne da aka haɗa aka tashi ɗaki dashi, a ɗan tsorace ta nemi miƙewa sedai da sauri ta dafe kanta tana faɗin
"Wash". Saboda zafin da ya ziyarci kan nata a daidai lokacin ne kuma komaɗaɗɗiya kuma yamutsattsiyar mata ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da wani ƙoƙo, wata irin zabura Kisnah tayi da har yasa taji kamar kanta ze faɗo saboda nauyi ga kuma zafin da ya ziyarce ta sedai bata ko kula hakan ba ganin wannan aljanar tana nufo ta.
Da sauri matar ta ƙara sa matsowa wajen Kisnah tana ajiye ƙoƙon hannun ta kan wani ɗan tudu dake gefen su, da hanzari ta saka hannun ta da ƙashi ne kawai da fata ba ko ɗigon tsoka (a ganin Kisnah ) ta ruƙo ta ganin tana neman fita daga ɗakin, wani irin ihu Kisnah ta saki jin matar ta riƙe ta haka kafin ta sami zarafin magana matar ta shiga yi mata magana cikin wata gurɓatacciyar Hausa da ba wani ganewa take ba
"Kayi haƙuli yalo, baka da lashiya magani nak kawo maka kashi".
Ai ina Kisnah bata ma tsaya ta saurare ta ba balle ta fahimci me take son cewa se ƙoƙarin ƙwace hannun ta kawai take tana zarar idon tashin hankali, cikin zuciyar ta kuwa bata bar tunani ya akayi ta zo hannun wannan aljanar ba, ganin fa bazata tsaya ba gashi maganin na neman bushewa yasa matar ta ɗan ɗaga murya ta ƙwala kiran
"Bingel".
"Na'am". Wata ƴar matashiya ta amsa tana shigowa cikin ɗakin, kallon ta mayar tayi kafin tayi mata maganin cikin wani irin yare aikuwa da sauri yarinyar ta ƙaraso ta kai nata hannuwan da bambancin su dana tsohuwa zance ko dattijuwa ce kaɗan ne, aikuwa se gashi sun danne Kisnah ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi, sosai mamakin yanda waɗan nan matan masu matuƙar siran ta kamar me suka iya danne ta haka har takasa motsi.
Ƙwaryar da matar ta shigo da ita ta janyo ta dangwalo wani koren abu cikin wata leda kamar mai kamar kuma ruwa me ɗan kauri ta shiga shafawa Kisnah kan goshin ta zuwa cikin kan ta kaɗan, runtse ido kawai Kisnah ta ke yi cikin tsananin zafi dan yarinyar da aka kira da Bingel ta danne mata baki da tafin hannun ta ɗaya saboda tsabar ihun da ta ke kurma musu.
Seda suka gama shafa mata maganin kafin Bingel ta cire hannun ta a bakin Kisnah, da sauri kuwa ta tofar da miyan da ta tara jikin rigar Bingel ɗin sedai ko kallon ta bata yi ba balle ta nuna ta ji haushi se ma wata ƙwarya da bata san yaushe aka shigo da ita ba da Bingel ɗin ta miƙawa matar nan suka kuma matse mata baki suka ɗura mata kafin suka sake ta, a tamanin ta duro daga kan abinda suka kwantar da ita da bata ma tantance mene ne ba ta shiga kakarin amai sedai ko ɗigo hasalima wahalar da kanta kawai tayi dole haka ta haƙura ta koma ta zauna tana hararar Bingel dan ita dattijuwar suna gama ɗura mata maganin ta fice.
Murmushi Bingel ta sake ma Kisnah da yasa tayi kamar wata zombie a idanun Kisnah duk da kuwa Bingel kyakkyawar bafulatanar daji ce sedai a idanun Kisnah ita bata ga wani kyau ba se ma tsorata ta da take yi.
A can wajen É—akin kuwa dattijuwar na fita ta tadda wani yamutsattsen farin bafulatanin daji sedai yafi matar nan kyan gani sosai, murmushi ta sake masa da dole wanda be saba ganin su ba ya tsorata sedai a wajen su su murmushi ne hakan, da É—an sauri dattijon ya matso kusan matar
"Nene Ina fatan kin shafa mata kuma tasha maganin".
Ya faɗa cikin cikakkiyar Hausar sa da tafi ta su matar da ya kira Nene nesa ba kusa ba, gyaɗa masa kai Nene tayi tana nuna masa ƙwaryar hannun sa
"Ƙin sha yalon can yayi sheda muka masa danna ni da Bingel, na shafa ma mun sha masa, aradu yalon kwai ƙarfin kai arɗo".
Ɗan murmushi arɗo yayi cikin fahimtar matar tasa, taurin kai shine ƙarfin kai a wajen su, kallon ta yayi yana faɗin
"Tun da ta sha ai da sauƙi, yanzu ki haɗo min wani na bawa yaron can dan shi har yanzu be farko ba kuma da alama ya fita shan wahala".
"Tau arÉ—o".
Ta faɗa tana shiga wata bukka nan gefen inda suke tsaye, tsawon lokaci tana ciki kafin ta fito da ƙwaryar da ta shiga a hannun ta ta miƙa wa arɗo, karɓa yayi ya juya ya shige wata bukka da ke ɗan nesa da wadda Kisnah ke ciki seda ya duƙa sannan ya iya shiga ciki, itama kamar waccan an yi mata ginin jar ƙasa kamu biyar kafin aka ƙara sa da asabari da kuma ya yume ya yumen su.