← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 64

Sashe 45

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki sosai ya kalle ta
"Kin taɓa gani na ina kallon Film bare ma irin wanda kuke kalla, I don't have that time to waste, ke dai kije ki kalla abin ki, kuma ai ba yau na fara zama ni kaɗai na jira ki ba ko?".

"Yaa ba fa romantic film bane it's a sport movie, Dan Allah kaji".

"Ki dena haÉ—a ni da Allah fa dan ba inda zani, am here zan yi night azkhar É—ina, you go and watch se ki bani labari later".

Duk magiyar da tayi masa ƙi yayi yakan yasa tayi fushi ta fice tana banging Masa ƙofar, murmushi yayi dan yasan haushi taji, shikam be taɓa shiga cinema ba wai kallo kuma baze fara yanzu ba, gwara a gida yana kallo sosai amma cinema ba da shi ba.

Kwantar da kujerar yayi ya kishingiɗa sosai a kanta ya shiga tasbih ɗin sa a hankali patiently waiting for her...........................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 30 (8/21/2022 10:31 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                           Page 3️⃣0️⃣

________________________📖 Ƙarfe sha ɗaya suka fito a tare su biyar ɗin suna tafe suna mata ƙorafin dena fitowar da tayi dan rabon ta da party da club tun kafin su je resort which is three weeks da dawowar su yanzu, har Gara cinema tun da gashi yau ta zo.

"Ni fa tun kafin tafiyar mu resort na fahimci wancan driver É—in nata ya É—auke mata hankali, ban san wane irin asiri yayi mata ba wai ta bashi aiki a Company kuma a office É—in ta ta yadda kullum suna tare, ban sani ba ko kin soma irin halin Surayya ne shiyasa ne ko kuma meye oho".

Sosai maganganun Hameedah suka yi wa Kisnah zafi, wato a wasan dare take so tace mata ta fara bin maza shine ta wani dake, da alama dai zargin ta take da Saraki, da ƙyar ta samu tayi controlling kanta dan kar tayi something stupid wa Hameedar, cikin irin wannan ƙorafe ƙorafen na su suka ƙarasa wajen motar ta ta ɗan jingina tana kallon su

"Am sorry guys, Kuma kusan dole ce zata sa na bar zuwa partying da clubbing, am sorry to say na bar clubbing, har abada ne ko kuwa ban sani ba se abin da gaba ta haifar, for partying da zuwa cinema kuwa rashin lokaci ne yasa bana zuwa, abubuwa da yawa sun faru a Company da dole ana buƙatar attention ɗina, as you can see sabida yawan abubuwan dole se da na samo me taya ni dan ni kaɗai bazan iya ba, amma cinema kam insha Allah ko next movie da ni za'a kalle shi".

Jijjiga kai Surayya tayi cikin yarda da abinda ta faÉ—a kafin suka haÉ—a baki ita da Leekha wajen faÉ—in

"I believe you dear, Allah ya taimaka ya bada Nasara, worry not okay?".

Dariya duka suka saki ganin yadda suka haÉ—a baki kafin Meenah itama ta dafa kafaÉ—ar Kisnah

"All the very best dear, Allah ya taimaka, we all are with you kinji".

Gyaɗa kai Kisnah tayi cikin farin cikin irin yadda suke nuna mata ƙauna, ɗan siririn smile Hameedah ta saki saying

"Wishing you lots of lucks". Murmushi itama tayi mata tare da nodding head alamar amsawa.

Jikin ƙofar side ɗin da take zama ta matsa ta shiga knocking a hankali, shiru be buɗe ba, ɗan ƙara ƙarfin knocking ɗin tayi nan ma shiru, matsowa Meenah tayi ta saka key ɗin motar ta ta shiga ƙwanƙwasa glass ɗin tsawon lokaci kafin yayi unlocking car ɗin ya fito hannun sa riƙe da gorar ruwa, zagayo wa wajen sa Kisnah take ƙoƙarin yi dan ganin ko lafiya yake suke ta Knocking ko kuma bacci yayi sedai tuni Hameedah ta riga ta isa wajen ta fara magana cikin sigar rashin mutunci tana watsa masa wani kallon banza

"Wannan wane irin wulaƙanci ne malam zaka kama ka wani rufe ƙofa ka bar ta a waje se faman bugu take kamar wani taka, ko kuwa dan kaga ta danƙa maka keys ɗin motar ne yasa kake feeling taka ce or what, ban da tsabar rashin iya samun guri irin na talaka har kai ka isa ka bar mu tsaye tsawon wani lokaci kamar wasu bayin ka ko masu yi maka maula, me kake dashi, waye kai, waye baban ka kuma waye ya tsaya maka, ko da yake ba laifin ka bane ita ce ta sake maka har kaga damar ta shiyasa ka rai nata, banda tsabar rashin ilimi da.............".

Razananniyar tsawar da Kisnah ta sake mata cikin kiran sunan ta ce ta dakatar da ita daga cin mutuncin da take wa Saraki da ya gama wanke fuskar sa da ruwan robar hannun sa sedai be kai ga mayar wa ba ya jingina jikin motar yana sauraren É—ibar albarkar da Hameedah ke masa sedai be ko É—ago kai ya kalle ta ba yana dai sauraren ta.

Da wani irin zazzafan taku Kisnah ya ƙara so inda Hameedar take tsaye tare da ɗaya hannun ta cikin son sauke mata kyakkyawan mari sedai a karo na farko Saraki ya riƙe hannun ta, da sauri ta waiwaya ta kalle shi tana son ƙwace hannun ta sedai be saki ba sema girgiza mata kai da yayi alamar kar ta mare ta tare sake mata hannun,

"Ƙyale ta, kar ki dake ta".

Ya faɗa xan ƙasa cikin murya irin ta wanda be daɗi da tashi daga bacci ba, juyawa tayi ga Hameedah da ta tsaya speechlessly watching at Kisnah kamar ta sami TV

"Da ka bar ni na koya mata hankali yaa, na daɗe ina tolerating iskanci da baƙaƙen maganganun ki gare ni amma ke baki gane ba, danne rai na nake kar nayi miki rashin mutunci amma You keep pushing me to the wall, to tau na kai ƙarshe da iya shegen ki ko kin ɗauka ban da hankali ne ban fahimci zagin da kika gama yi min ba yanzu, ko kin zata ban fahimci nufin ki we have an illegal dirty affair da ya Saraki bane a kalaman ki, na daure na share ne kawai saboda ƴar uwar ki gata nan.......". Ta faɗa pointing at Meenah dake nan tsaye kamar an dasa ta saboda tsabar tashin hankali

".......if not sabida ita wallahi da tuni nayi maganin ki, and ki sani Yaa da kike kira da driver ya fi mun ke sau adadin da za'a kuma bani zaɓi, je mau be mere driver a wajen ki amma ni a wajena shine mutum na farko da nake ganin matuƙar girma da darajar shi dan haka duk wadda a cikin ku take ganin ba zata iya girmama shi ba to na haramta ko magana tayi masa ehe, zulwajahaini kawai ƙaramar ƙwaruwa, ke iskancin ki na gangan ne yarinya, da ace kin isa kin cika kin kuma tumbatsa ba soka min magana da hassada a ɓoye zaki yi min ba fitowa zaki yi gaba da gaba ki tare ni ki faɗa min ni karuwa ce, ko an gaya miki dan kin yi hakan zan damu ne, ko kin manta ba yau na fara jin an dangan ta ni da sunan ba, kuma tun da ake faɗa kin taɓa ganin na damu, eh ni karuwa ce amma me aji dan ni maza da kan su suke bina bani nake bin su ba, na san abinda kike wa hassadar ke nan kuma dai se haƙuri na riga nayi miki nisan da ko hange na ba zaki iya ba balle ki kamo ni, mara mutunci kawai".

Zuwa yanzu hawaye kawai ke kwarara a fuskar Hameedah cikin baƙin cikin irin cin fuska da tozarcin da Kisnah tayi mata amma fa a ganin ta dan duk da dare ne seda aka samu masu tsayawa kallon abinda ke faru cikin waɗanda suka fito daga gidan kallon.

Ita kuwa Kisnah tana gama faÉ—ar abinda ta ga dama wa Hameedah ta shige mota tare da maida murfin ta rufe, batare da ya dubi kowa ba shima Saraki ya shiga side É—in da ya kamata ya rufe, cikin kankanin lokaci ya tashi motar suka fita daga cinema É—in suna barin su Surayya da suka zama so speechless tsaye kuma daskare a wajen.

Tafiya yake a hankali kamar baya so time to time yana kallon gefen da take zaune tana fidda huci har lokacin kamar wadda zata ci babu.

"Relax, kwantar da hankalin ki pls, ni ban ma ga abin tashin hankali a maganar da ta faÉ—a ba, kema kin san gaskiya ta faÉ—a am just a mere driver to you Kuma be kamata na rufe mota na bar ki waje kina Knocking ba alhalin kina matsayin mamallakiyar motar, uhm to meye ta faÉ—a da zafi kuma".

A hanzarce ta juyo ta kafe shi da ido tana jefa masa kallo me kama da harara cikin jin haushin abin da yace

"To da kake driver ita ta É—aukar min aikin, ko ita take biyan ka, ina ruwan ta in ma kwana nayi ina knocking da zata wani kama zagin ka, motar ta ce ko mun haÉ—a kuÉ—i da ita mun siya ne".

"To shikenan baku haÉ—a kuÉ—i kun siya ba, amma ni a ganina da baki kula ta ba, mace me class bata faÉ—a any how Kuma bata tsayawa ihu da kowane kalan mutane, wanda suka isa da wanda basu isa ba, and pls ki rage saurin marin da kike yi, da an miki abu se ki hau kai mari hakan ma is not good most especially ga maza, ba class É—in ki bane".

Ajiyar zuciya ta saki fushin ta na É—an raguwa saboda yadda yake magana cikin kwantaccen harshe da taushin murya
Chapter 45 · 0% Book details