← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 64

Sashe 21

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta faɗa tana durowa daga gadon da sauri har tana neman faɗuwa ta dai samu bata faɗin ba, bathroom ta faɗa a gurguje dan It's 5 mins to eight, wardrobe ta buɗe ta janyo wata straight English gown kusan similar to ta jiya sedai wannan bata kamata sosai ba kuma ta kai mata ƙasa sedai tana da tsaga sosai ta baya dan ya kai har wajen gwiwar ta, da sauri ta zura rigar bayan ta saka bra da pant ɗin ta, faɗin yadda silver gown ɗin ta mata kyau ma is a total waste of time, scarf ta janyo silver me ƙyalƙyali ta ɗaura saman kanta sedai gashin ta ya fito ta tsakiyar sa duk da ta nannaɗe shi amma seda yakai ƙasan wuyan ta.

A gurguje ta ɗebi wayoyin ta da kayan rubutun ta ta fice ko breakfast Bata iya tsayawa yi ba dan shirinta kaɗai ya cinye fiye da 40mins, bata sami kowa a falon ba ta wuce compound cikin sauri wanda takalmin ƙafarsa silver color me tsini be hana ta yi ba, tsaye tayi tana bin compound ɗin da kallo sosai ganin bata ga Saraki ba, wajen da ma'aikata ke zama in sun gama aikin su, gurin yasha grass carpet me kyau ɗauke da tables manya da kyawawan kujeru gefen su flowers ne masu kyau da ke fitar da sassanyan ƙamshi, tun da Khamees shugaban ma'aikata ya hango ta ya miƙe da sauri har ta ƙaraso, gaishe ta ya soma sedai bata kula hakan ba ta shiga tambayar sa

"Ehm wannan sabon driver É—in be zo bane?".

"Wai Saraki? Yazo amma ya É—an fita yana amsa call yanzun nan".

"So sunan sa Saraki kenan?".

"No baba me gadi ya kirashi da hakan dan yace abubuwan da yake kaman tafiya,magana, miskilanci da izzar shi kaman na yaran sarauta shi yasa masa Saraki amma sunan shi na gaskiya Ahmad ne".

"I see". Kawai tace ta juya daidai lokacin Saraki ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo, da ɗan sauri ta ƙarasa tana masa alamun ya fito da mota.

Farar mota ya É—auko ganin kayan jikin ta is way related to farin, da sauri ta buÉ—e ta shiga kana yai hanyar gate da kafin ya kai ma gate É—in ya buÉ—e kansa É—an tuni nasu gadi suka saka password É—in ganin fita zasu yi, seda suka hau kan titi sosai kafin ta É—an dube shi a kaikaice tace

"Good morning".

Ya ɗan yi mamakin jin ta gaida shi sedai ya dake ya amsa da "morning" batare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tuƙin sa, itama bata kuma cewa komai ba ta buɗe littafin kan cinyar ta ta cigaba da dubawa.

Bakowa yasan halayen Kisnah sosai ba se close friends É—in ta dake tare da ita kusan ko yaushe wato su Meenah, ba wani abu bane gare ta gaishe da wanda ya girme ta tun bare ma in ya kama girman sa, eh tana da tsiwa da rashin kunya amma fa ga wanda ya siya da kuÉ—in sa ma'ana wanda ya takale ta ko ya zubar da girman shi.

"Where are we heading to?".

Batare da ta É—ago ba ta bashi amsa dan karatun ya sha kanta

"Federal University, Manyan".

Cikin ƙaton gate ɗin school ɗin ya wuce wanda tun ɓullowar motar ta security suka buɗe amma mamaki suke na yadda yau bata yi horn ba kamar yadda ta saba ga kuma yanayin driving ɗin cikin nutsuwa.
Bakin department ɗin da ta dinga kwatanta masa har suka ƙara so yayi parking tare da kashe motar, buɗe side ɗin ta tayi ta fice bayan ta kwashi litattafan ta, rufe ƙofar da ta bari a buɗe yayi yana lumshe idan sa cikin karanta suratul Kahf da be samu yayi ba yau saboda baccin da yaci ƙarfin sa.

Tun daga nesa ta hango su Meenah wannan karon su uku dan babu Surry da ke asibiti, ƙarasowa sukayi gare ta suka amshi books ɗin hannun ta suka jera tare zuwa cikin theatre ɗin, row ɗin tsakiya suka shiga kuma layi na farko suka zazzauna kafin suka fara gaisawa a tsakanin su, karɓar littafin hannun Meenah tayi ta shiga yi musu bayanin abinda tayi researching jiya wanda take tunanin za'a iya tambayar su, sosai tayi musu ƴar ƙaramar tutorial Wanda har se da lecturern ya shigo sannan ta rufe littafin ta miƙawa Leekha, karɓar Leekha tayi ta haɗa da nata da nasu Meenah ta fitar dashi can gaban theatre ɗin sannan ta dawo, miƙewa duka suka yi jin malamin na faɗin each line mutum biyu yake son gani dan gurin akwai girma sosai, fita Kisnah da Leekha suka yi suka bar Meenah da Hameedah na sake spacing tsakanin su.

Tunawa da Surayya yasa ta fasa budar saman theatre É—in ta wuce wajen malamin dake tsaye yana jiran su gama gyarawa

"Good morning sir". Juyowa yayi ya dube ta yana amsa gaisuwar Tata

"Good morning, fatan dai lafiya".

"No sir, nazo yin report ne concerning Surayya kabeer da ba zata samu damar zuwa yin test ba saboda rashin lafiya, yanzu haka tana kwance gadon asibiti sir".

"And where's her relatives da basu zo sun yi reporting ba se ke".

"Her brother is presently in Canada for business Kuma ba ta da kowa bayan shi, matar sa kuma hate...oh Is just personal sir, but you can confirm, tana Gare well hospital, room 13, Dr Ibrahim nura ne ke handling case É—in ta".

GyaÉ—a kai yayi cikin yarda da batun nata kafin yayi wa Surayya fatan samun lafiya da tabbatar mata da zai organizing team É—in bincike aje a dubi Surayya a kuma tabbatar da in bata da lafiya da gaske, nodding kanta tayi tare da masa godiya ta juya neman inda zata zauna.

Bin bayan ta sir Kashim yayi da ido cikin yaba kyan ta tare da mata fatan shiriya, if not sabida ayyukan ta he would have marry her fan sosai take da kyau take kuma burge shi sedai yasan ko hauka yake baze kai ta gidan su sunan wadda yake so ba duk da shiÉ—in ba saurayi bane dan yana da mata har da Æ´aÆ´an su biyu.

Cikin jin daɗi take ta amsa questions ɗin cike da nutsuwa dan alhamdulillah ba abinda bata sani ba cikin wanda aka tambaya, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama ta sake bi through kafin tayi submitting ta fita, da idanu majorityn ƴan class ɗin suka bita da ido har ta fice, su fa har yau gani suke bata da wani ƙoƙari kawai tana siyan marks da jikin ta a wajen malamai though yawancin su zasu bada shedar ita bame zuwa office ɗin malamai bane se in ta zama dole.

Duk wani abu related to karatu lokacin ta take bashi cikakken shiyasa bata wasa da zuwa makaranta, ƙarya kaga ta makara dan tun fara karatun ta har zuwa yanzu da take 400l zata iya irga iya makarar da tayi haka bata yadda rashin fahimta ya shiga tsakanin ta da wani malami shiyasa kawo yanzu malami ɗaya ne suke ƴar tsaka dashi, shikuma haka kawai ya ɗau karan tsana ya ɗora mata, tun tana kau da kai da ido a kanshi dan bashi girman shi na malami har ya ƙure ta tayi masa rashin mutunci shiyasa shi kuma duk hanyar da ke disga ta ko ya kayar da ita a course ɗin ita yake nema, yanzu haka akwai assignment ɗin da aya bayar Wanda individual ne kowa da questions ɗin sa, har zuwa yau da za'a yi submitting jibi ta kasa fitar da amsar, tayi tayi har ta haƙura ta cigaba da normal routine ɗin ta sedai deep down abin na mintsinin ta a rai, bata taɓa samun wata matsala ta carry over, spill over ko resit ba se gashi yanzu ƙarfi da yaji malamin na neman kai ta ƙasa.

Cikin wannan tunanin ta ƙarasa ta shiga motar se dai bata rufe ƙofar ba, jiran su Meenah zata yi sedai bazata iya tsayuwar cikin ranar da ake yi me zafi sosai ba shiyasa ta shiga motar, hannu takai ta ƙara ƙarfin AC ɗin kana ta kwanta cikin kujerar ta ta shiga tunanin ta wace hanya ya kamata ta ɓullowa malamin.

Tayi nisa cikin tunanin har bata ma san tana hawaye ba dan ita kam kacokan fari cikin rayuwar ta ta ɗora shi ne kan karatun ta, shine number one priority a rai da zuciyar ta shiyasa yanzu da matsala ke neman Kunno Kai duk hankalin ta ya tashi, bawai bata da yadda zata yi da malamin bane dan ko yanzu taso ya bar makarantar tabbas za'a masa transfer haka kuma ko A tace tana so tana da yadda zata samu ko da baya so kuwa se ya bayar sedai tana da wani principle ɗaya, sam bata son alfarma a karatun ta, bata son hanya ko wani abu, tana so ne ta bugu ƙirji tace ta sami kwalin ta ne da ƙoƙarin ta da zufar ta, wannan shine aƙidar ta shiyasa ba ta tunkari kowa da batun ba.

A kaikaice Saraki ke kallon yadda take hawayen wanda alamu ya nuna koma meye ya sata kuka ba ƙaramin matsayi gare shi ba a ranta haka kuma ba ƙaramin so take wa abin ba, to ko dai malpractice tayi aka koro ta daga hall ɗin ɗan be ga wanda ya fito ba har yanzu bayan ita, taɓe baki yayi yana ayyana hakan ne ma dan yadda wannan take yasan ba wani abu ta iya ba balle ta tsinana dole seda satar amsar.

Ƙarasowar su Meenah ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi ta maza ta saka hannu ta share hawayen idon ta dan bata  taɓa nuna karaya ba gaban su yanzu ma kuma bazata fara ba shiyasa bazata bari suga hawayen ta ba, ɗan kallon Saraki tayi ta gefen ido hopping be ganta tana kuka ba se ma taga idanun sa a kunshe suke hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya.
Chapter 21 · 0% Book details