← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 64

Sashe 64

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ÆŠauraye pot É—in tayi ta maida É—aki sannan ta koma ta shigar da flask É—in ciki ta ajiye tsakiyar carpet É—in su, cups ta É—auka ta fita ta É—auraye suma ta kai kusa da flask É—in sannan ta É—auko gwangwanayen kayan madara da ya siyo jiya da dare tare da bread ta ajiye, cup É—in da ya fi girma ta É—auka ta tsiyaya masa tea É—in ta saka cubes É—in sugar huÉ—u ta zuba masa madara da bournvita sannan ta kai masa gaban sa da yake zaune kan carpet kusa da katifar su ya shirya cikin jeans dogo da t-shirt.

Duk abinda take yi yana kallon ta haka kuma mamaki ne ya hana shi magana na yanda ta haÉ—a tea daidai, tambayar kan sa ya ringa yi a ina ta koya kafin kuma ya bawa kansa amsa da ai ba wani wahala zata iya haÉ—awa dan alamu sun nuna ita ke haÉ—awa kanta.

Nata ta haɗa ta koma gefe ta shiga sipping a hankali zafin shi na ɗan ƙona ta sedai ko kaɗan ba wannan zafin ne a gaban ta ba dan zafin maganganun da ya faɗa mata ɗazu sun ninka wannan so ba iya ka, ko rabi bata yi ba taji shayin ya fita a kanta ta ajiye dan dama haka take, indai ranta a ɓace yake bata iya cin abinci shiyasa ba ta ko kalli gefen da bread ɗin yake saboda tasan ba zata iya ci ba.

Tunanin rayuwar ta ta shiga yi da yadda ta taso ba wani me kwaɓa, komai tayi kawai daidai ne a wajen kowa, bane ce mata yi, bari, gyara  ko makamancin haka shiyasa take duk abinda taga yayi mata daidai a ranta, yanayin shigar ta kuwa abu ne da yabi jinin ta, tun da tayi hankali da masu irin shigar ta buɗi ido ta kuma rayu a tsakiyar su under supervision ɗin Mrs Andrew Smith Wanda itace matar shugabar makarantar da kawu ya danƙata a hannun sa, bata san meye al'adar ta ba, bata san meye daidai da ba daidai a addinin ta ba tunda bata da wani ilimi a kai shiyasa tayi adopting gaba ɗaya culture ɗin su da ma wasu da yawa daga cikin ra'ayin su da yanayin rayuwar su, sallah ce kaɗai ta banbanta sunan ta da kasancewa kafira wanda da za'a bi diddigi ita kanta sallar ba tabbas ɗin tana amsuwa dan kwata kwata ko kusa ko alama ba ta yinta yadda Annabi ya koyar, to bata da ilimin hakan shiyasa kawai dai tana yin ta ne.

Hawaye ne suka cika idanun ta dan tasan da iyayen ta basu rasu ba da bata kasance cikin irin wannan rayuwar ba balle har ya ringa samun damar yi mata gori da baƙaƙen maganganu.

Cin bread ɗin yake yana korawa da tea kamar a ɗan gaggauce dan yana so ya zagaya yaga wace irin sana'a ze kama da zata fisshe shi, har ya gama tana zaune inda take cikin rashin daɗin rai, seda ya ajiye cup ɗin hannun sa ya miƙe sannan itama ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauke cup ɗin ta fitar waje ta dawo ta shiga gyaran ɗakin cikin sanyin jiki, katifar ta fara gyarawa ta karkaɓe bedsheet ɗin ta maida ta gyara sannan ta mai da kowane abu inda ya kamata kafin ta ɗau tsintsiya ta shiga shara, seda ta gama ta kwashe da ƙyar dan bata iya ba haka kuma bata jin ko son Kiran sunan sa balle tace ya koya mata, ruwa ta kawo tayi mopping floor ɗin iya yanda ta iya sannan ta maida carpet ɗin da ta naɗe tare da fesa room fresheners kala biyu.

Seda ta gama komai sannan ta ɗauko ƙaramin jotter da biro da ta karɓa jiya wajen saudah ta shiga rubuta masa duk abinda basu dashi na girki da ragowar amfanin yau da gobe, miƙa masa paper ɗin tayi bayan ta duba taga komai yayi, be tambayi ta me ce ba ya karɓa ya bi abubuwan da kallo kafin ya gane na meye.

Da "adawo lafiya". ta bishi da ze fita daga ɗakin duk da bece mata fita ze yi ba alamun fushi yake da ita, yana ficewa ta tura ƙofar ɗakin amma bata saka lock ba ta koma kan katifa ta shiga share hawayen da ta ke ta  dannewa kar su fito a gaban sa..........................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
Chapter 64 · 0% Book details