← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 64

Sashe 27

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 1️⃣8️⃣

______________________📖 Kamar yadda yace haka ta sake shi a main garden ɗin gidan by 3pm suka soma karatun, ba ƙaramin yabawa ƙoƙarin ta yayi ba a zuciyar sa ganin duk abinda ya koya mata take ta ke kwashe shi dama akace kabar abinda zuciya ke so.

Itama a nata ɓangaren haka tai ta yaba yadda yake mata bayani dalla dalla cike da ƙwarewa da sanin malamar karatu, sosai ta kasa daurewa har ta kai ga furta masa abinda yake yawo a ranta

"Yaa wai ya akayi ka iya karatun mu haka sosai, ko dai kaima law ka karanta?".

Shiru yayi mata a lokacin dan be san amsar da ze bata ba, be shirya sanar da wani asalin sa ba haka ne shirya tattauna personal life É—in sa da outsider ba Kai koma insider É—in ne he's not interested balle kuma ita da yanzu ne yake kan sanin wacece ita.

"Amma kuma me yasa baka nemi aiki ba tun da nasan ka gama karatun ka da alama".

Ta sake faÉ—a dan ta É—au shirun sa as yes eh law ya karanta

"I was withdrawn from the school". Ya  sami bakin sa da faɗa dan alamu sun nuna Yes cikakkiyar lawyer ɗin za'a yi a wajen, shikuma ba ya san duk abinda ze kawo ta zarge shi kan abinda ba haka bane.

"Eyya, so sad amma akan me?". Ta sake tambaya further Dan dai tasan baze yiwu ace akan bashi da ƙoƙari bane se dai something different da take son sani dan daga yadda yake mata bayani ta tabbatar a lokacin da yana makaranta ba za'a rasa sashi cikin gifted and talented students ba.

"Don't wanna talk about it now".

GyaÉ—a kanta tayi cikin nuna fahimta kafin tace

"I understand, maybe later ko?".

Ɗaya mata gira kawai yayi dan ya fahimci in ba haka yayi mata ba ba ƙyaleshi zata yi ba alhalin taɓo maganar makaranta da karatu da tayi yasa yaji incident ɗin da ya faru ya dawo masa sabo Dan if not because of it da tuni i yanzu yana zaune in his own office handling office stuffs.

Ba su tashi daga karatun ba se da aka kira Asr prayer hakan ma dan ya tashi ne ba yadda zata yi dashi dan in ta ita ne  bata ƙi sukai har magrib ba yana koya mata tana kuma ƙiriniyar tambaye tambaye abinda babu ruwan ta be kuma shafe ta ba.

Kashegari har bakin ƙofar lecture hall ɗin su ya kai ta tare da mata addu'ar fatan nasara abinda ya saka Kisnah dakatawa ta ƙura masa ido for a while kafin ta gyaɗa masa kai idon ta na kawo ƙwalla, abu ne tunda ta taso zata ce ba wanda ya taɓa damuwa da yi mata wato fatan alkhairi da nasara in zata yi assignment, test ko exam.

To wa ma take dashi bayan kawu da family ɗin sa? Se ko abokan Abbu da ta manta rabon da ta taka ƙafarsa gidan su haka suma tuni suka dena damuwa da neman ta tun bayan wani cin mutunci da kawu ya yi musu lokacin da ya kaita England karatun primary ita kaɗai shikenan duk suka zare hannayen su a kanta.

Kawu da matar sa Mommy kuwa.. hmmm.....bata masan ya zata kwatan ta su ba, ta wani ɓangaren the two are perfectly synonyms of each other, in other views Kuma su ɗin antagonist wa juna.

Suna da matuƙar close similarities ta ɓangaren tsananin son kuɗi da kwaɗayi sedai suna da bambanci wajen tsananin son ƴaƴa da Mommy ke dashi da kuma hassadar da bata ma iya ɓoye ta, munafunci da baƙin ciki kuwa wajen Mommy har na siyarwa akwai, to taya ma zata yi wani tunanin samun fatan nasara ga matar da a kullum so take taga bayan ta ko kuwa ga kawu da kullum hankalin sa na kan yadda za sami kuɗi ta kowace hanya.

Bayan su waye a cikin rayuwar ta? Ƙawayen ta, yes ƙawayen ta, taya zata fassara su? Da wa zata fara a ciki? Meenah da ba inda ta dosa a rayuwar ta ban da son holewa, ita dai tayi ta watsa ƙwayar da indai da ita to fa bata da matsala, ko kuwa da Leekha da tsabar shan giya har ya taɓa mata hanta seda akai mata aiki ko kuwa Hameedar da ƙiri ƙiri take iya fahimtar ƙyashi da hassadar ta cikin ido da Muryar ta har ma da ayyukan ta, dama dama Surayya, duk da mugun son mazan ta tana son karatu haka ta kan yi magana ta cikakkun masu hankali in taso bayan ita gaba ɗaya ragowar ukun ita ce ta sauya rayuwar su kan son karatu, a dole suke yin shi ba dan sun so ba shiyasa basa taɓa damuwa da wata matsala a karatun nasu wanda duk aka samu akasi ita ke yin tsayin daka har se ta tabbatar komai ya koma daidai kuma yana tafiya yadda ya kamata.

Ajiyar zuciya tayi kafin ta saka yarda ta ɗauke ɗigon hawayen da ya sauka daga idon ta tana ƙarasa shigewa hall ɗin, sama sama ta gaida da ƙawayen nata kafin ta maida hankali kan littafin da ta shigo dashi wanda ta fara rage karatun exams ɗin da zasu fara ne next week insha Allah, tana jin su suna hira sedai bata ma maida hankali ba balle ta fahimci akan mene suke hirar.

Cikin haka halitta ɗaya da zata iya kalla tace ta tsana a duniyar ta ya shigo cikin hall ɗin, ita bame damuwa da shiga shirin mutane bace shiyasa kafin kaji ta furta ƙi ko so abu ne da ake daɗewa sedai wannan ta furta masa kalmar ƙi da tsana so adadin da harshe baze iya ƙirgawa ba kuma ba dan komai ba se dan yadda yake nuna mata tsananin ƙiyasta ta ban mamaki da shigar da bawa ruɗani dan ko kallon banza bata taɓa gwada yi masa ba har se da shi da kansa ya siya da kuɗin sa, MALAM SAMINU kenan, shine malamin da ke ɗaukar su course ɗin CON005 haka kuma mutumin da ya ƙirƙiro wani assignment dan kawai don ganin ya kaita ƙasa sedai Allah Alhakeem baze taɓa bashi nasara ba a kanta.

Cikin haɗa murya ɗaliban duk suka shiga furta gaisuwa a gare shi, be amsa ba se da ya ƙare musu kallo har idon sa ya sauka a kanta kafin ya ɗauke kai ya amsa musu, cikin ƙankanin lokaci suka shiga aiwatar da abinda ya tarasu wato lecture, ko da ya dakata shiru yayi yana bin su da kallo kafin ya fara jefo tambayar da kusan rabin ɗaliban suka ɗaga hannu sedai gaba ɗaya ya tsalle su ya nuna Kisnah da kanta ke ƙasa, taɓo ta Leekha tayi tana mata magana a hankali da yasa ta ɗaga kan ta ta dubi Leekhar sannan ta maida kan malamin, sake maimaita mata question ɗin yayi cikin son ganin ya tozarta ta takowace hanya.

Miƙewa tayi ta fara magana amma mutumin nan yace baya ji dana haka ta fito gaban board, bata ƙi ba dan hakan a wajen ta ba sabon abu bane, takawa tayi cikin yanayin tafiyar ta yayinda kusan duk wani ido ya dawo kanta, doguwar riga ce me kamar baya sedai wannan anyi shaping ɗin ta ta yarda ya ta kamata tsam haka kuma me makon ta ɗaura ɗan kwali kan gashin ta da tayiwa bun se kawai ta naɗa shi in v style ta yadda tsakiyar ke waje kuma ba ƙaramin fito da fuskar ta ɗaurin yayi ba.

Gaban board ta tdaya kamar yadda yace kafin ta fara bayani cikin nutsuwar ta har ta kai ƙarshe sedai ko kafin ta rufe bakin ta ya sake jefo mata wata haka yai tayi mata cikin son dole se ya ruɗa ta sedai har yanzu wannan mutumin be san wace Kisnah ba, ta kuma ji daɗi sosai dan yawancin tambayar da yake yi jiya sunyi makamantan su da Ya Saraki jiya shiyasa dole ya haƙura ransa a jagule da ɓacin ran rashin nasarar da yayi.

Ko da ze fita nan ya fara karɓar assignment ɗin da ya bayar kafin yasa kai ya wuce cike da fatan samun damar ta a nan ɓangaren.

Da farin ciki sosai a fuskar ta ta fito suka wuce theatre É—in da zasu yi test wacce take opposite da hall É—in da suka gama lecture, cikun taimakon Ubangiji shima be bata wahala ba tayi ta gama ta bayar ta fice.

Buɗe ƙofar motar tayi ta zauna yanayin ta kaɗai ya isa bayyanar da farin cikin da take ciki a lokacin, batare da ya tambaye ta ba ta shiga sanar da Saraki duk yadda komai ya wakana daga test ɗin har yadda suka yi da M. Saminu a lecture hall, shi kansa yaji daɗin yadda ta fita kunyar jama'a dan mutane irin su Kisnah da suka yi ƙaurin suna idon kowa a kansu yake.

Cikin kwanakin da suka biyo baya sosai ta ajiye partying dasu clubbing dan fuskantar exam É—in ta wadda daga ita se project da zasuyi shikenan sun gama degree É—in su gaba É—aya se zama jiran result da zasuyi shiyasa gaba É—aya bata son jin wani abu me sunan matsala dangane da karatun nata.

A kwanakin sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Saraki da Kisnah saboda kusan kullum tare suke wuni suna karatu wanda shima ba ƙaramin pleasure yake driving cikin hakan ba dan kina komai hakan na tuna masa da memories ɗin karatun sa.

Ranar da zasu Fara exams ɗin sosai ya saka ta ta kusan kwana a pray mat dan ba ta sassafe bace se ƙarfe sha ɗaya tukunna shiyasa ta sami damar yin Bacci ta Sami peace of mind.
Chapter 27 · 0% Book details