← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 64

Sashe 59

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kashegari da wuri suka shirya dan akwai tafiya sosai kafin su shiga cikin gari, basu ɗau komai ba da yake sunan nasu dan ba abinda zasu yi dashi ko sun ɗauka ɗin, se a lokacin ne kuma arɗo ya kawo wa Saraki kayan sa da ya tsince shi da su a jikin sa, be yi zaton kayan zasu sake amfanuwa ba se gashi an kawo masa su a wanke, faɗar farin cikin da yayi a lokacin ɓata baki ne, kayan ya koma ɗakik su ya canja yana yiwa arɗo godiya yana fitowa kuwa se suka ga kamar bashi ba dan se ya canja musu sosai a cikin shigar, ita kanta Kisnah se taga yayi mata wani irin kyau dan har ta fara sabawa da ganin sa cikin shigar fulanin dajin.

Nata kayan Nenne ta bata suma an wanke har da ɗin ke guraren da suka yage sedai a idon ta ba zasu sawu a jikin ta ba dan haka kimonon kawai ta ɗauka ta ɗora kan saƙin jikin ta tare da scarf ɗin ta duk da shima ya sha ɗinki.

Cikin matuƙar kewa Kisnah tayi sallama dasu Bingel da Nenne kamar kar su rabu, shaƙuwar kenan, amalanken da arɗo ya tarar musu suka hau aka shiga loda musu tsarabar da su arɗo suka basu, ƙwaryar zuma me kyau guda biyu haka fresh sabon nono ƙwarya uku se curin fura dake cikin wata ƙwayar daban.

Haka me amalanken yaja suna ɗagawa juna hannu dasu Nenne dan shi arɗo se ya kaisu tasha, seda suka fara biyawa gidan baffa arɗo suka yi masa sallama shima ya basu tasa tsarabar ta kayan fruits har buhu biyu sannan suka tafi, duk inda suka bi haka ake ta ɗaga musu hannu dan kaɗan kaɗan ne basu san Kisnah ba kasancewar ƙauye kowa ya san kowa har suka yi nisa da mutane suka fara shiga dokar daji.

Kamar yadda arɗo ya faɗa tafiyar ba kaɗan bace dan se da rana ta ɗaga sosai sannan suka kai tasha, akori kura ne da yawa a wajen matsayin motocin tafiya, dole haka su Kisnah suka ɗane bayan ta aka loda musu kayan tsarabar su, anan suka yi sallama da arɗo bayan ya sanar dasu sunan kauyen nasu wato Bina, haka kuma yana can cikin jihar Makwan ne, daga Kisnah har Saraki ba wanda yasan wani gari wai shi Makwan sun dai amsawa arɗo da sun gane ne kawai, da motar zata tashi kuwa Kisnah har da kukan ta na rabuwa da arɗo kafin motar ta tashi suna ɗagawa juna hannu su dashi har suka ƙule.

Tafiya ce mata daɗi dan hanyar duk kwazazzabai ne bata da kau dama kuma ba wai kwalta ce ba a wajen birji ne, se kusan yamma kafin suka sauka a wani babban ƙauye da a can cikin sa ne ƙauyen su arɗo yake wato Bina, nan ma sallah kawai suka yi suka sake neman tasha suka hau Mota zuwa cikin garin Makwan da ɗan guzurin da arɗo ya bashi da kuma wanda baffa arɗo ya ƙara musu.

Basu shiga cikin garin Makwan ba se karfe shida na yamma a yadda yaji direban motar na faɗa, ko da mota ta tsaya rasa ina zasu nufa suka yi tunda basu san ko ina ba a garin hasalima wannan ne karon su na farko na jin sunan garin da ma kasancewa a cikin sa..............................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, Comment and share fisabilillah.

Ouummey 39 (8/27/2022 9:32 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                           Page 3️⃣9️⃣

________________________📖 wani tunani yayi kawai ya tsayar musu da napep yace ya kai su nearby hotel amma ba me tsada ba, beso kashe kuɗaɗen hannun sa ba sedae ba yadda ze yi dan ba su da wajen zuwa in ba can ɗin ba.

Kamar yadda yace wa me napep ɗin haka ya kai su wani middle class hotel, room ɗaya me ɗan girma ya kama musu ya karɓi key suka wuce.

Suna shiga ta wuce toilet da sauri, ruwa ta tara ta shiga wanke jikin ta kamar me wadda ke shirin canja fata, se da tayi kusan saɓi biyar kafin ta haƙura ta fito shima dan knocking ɗin da Saraki ya dame ta da yi ne, ɗaure da towel me matsakaicin girma ta fito abinta se kanta da yasha wanki shima naɗe a ƙaramin towel, da sauri ya kau da kansa tare da bata hanya ta wuce ko a jikin ta, da sauri ya faɗa toilet ɗin ganin ta zauna kan dressing mirror gyara jikin ta, mayukan da ta gani ta dudduba ta ɗau wasu biyu ta shafa ɗaya a jikin ta ɗayan kuma a gashin ta sannan ta ɗau set ɗin comb ta tashe kanta bayan ya ɗan sha iska dan gurin basa ajiye hand dryer, seda ta gama shirya wa kuma ta tuno bata ma da kayan da zata saka dole haka ta koma ƙaton bed ɗin ta zauna jiran ya fito ya samo mata kayan da zata saka.

Shima a ta can wankan yayi har round uku dan tsabar dauɗar da ya tara a Bina jikin sa har wani ƙaiƙayi ƙaikayi yake masa, bathrobe da ya hango yasa ya ajiye towel ɗin da ya ɗauko dan ɗaurawa ya ɗau ledar sabuwar bathrobe ɗin ya farke tare da zurawa ya ɗaure sannan ya fita bayan ya goge sumar sa ya ajiye towel ɗin a nan.

Be lura da ita ba ya ƙarasa kan mirror ya fara neman man da ze shafa, ganin be ankare da ita ba yasa ta kira sunan sa a hankali

"Yaaa".

Juyowa yayi ya dube ta at the same time ya kawar da sauri ganin ta É—aure da towel har lokacin, towel É—in da a ganin sa be rufe komai na jikin ta ba,

"Meye haka kike zaune ba kaya?

"Ba ni da kayan da zan saka yaa, nawa kasan masu dauÉ—a ne I can't wore them again".

Shiru yayi dan.yasan gaskiya ta faɗa, shaf ya mance da batun kayan da zasu canja shiyasa be ko yi batun siya ba, ajiyar zuciyar rashin mafita ya saki kana ya miƙe zuwa toilet inda ya ajiye kayan da ya cire ya fito dasu yana lalubar aljihun sa dan ya ɗebo ragowar kuɗin da suka rage musu da baya tunanin sun wuce 6k.

Sak yayi jin hannun sa ya taɓo wani card me ɗan kauri kamar ID kamar kuma complimentary card know Kuma................!

Kai baya ma tunanin the last one, zaro kuÉ—in yayi gaba É—aya tare da card É—in, abin da ya gani ne ya daskarar dashi a tsaye, ganin yayi tsaye yana bin kuÉ—in hannun sa da kallo yasa ta kiran sunan shi har kusan so biyu amma be san tana yi ba, seda ta É—aga murya sosai sannan yayi firgigit ya juyo ya kalle ta, hannun sa ta kalla sannan ta maida kan fuskar sa

"Yaa meye a cikin kuÉ—in da ka kafe su da ido har baka ji kiran da nayi maka ba kusan so uku?".

Da sauri kamar wanda ta tunatar dashi ya sake maida idon sa kan kuɗin, ganin har lokacin card ɗin na nan yasa ya kai hannu ya ɗauka jikin sa na ɗan rawar murna, taso wa tayi cikin son ganin abinda ya ɗauka da shine yasa ya kafe kuɗin da kallo cikin tunani, zaro ido tayi ganin atm card ne a hannun nasa haka kuma bata yi wata wata ba ta fisge da iya ƙarfin ta, ATM card ɗin sa ne wanda suka je bank tare ya buɗe take saka masa albashin sa a ciki, tsabar ruɗewa da farin ciki bata san sanda ta faɗa jikin sa ta ƙwaƙumeshi cikin bashi zazzafar runguma ba, wani irin shock ne me azababben ƙarfi ya ratsa jinin saraki, a daidai wannan lokacin baya tunanin in an tsaga jikin sa za'a ga jini tsabar daskarewar da yanayin yasa yayi.

Gaba ɗaya kuɗin hannun sa zubewa suka yi a ƙasa dan ba shida wani sauran ƙarfin riƙe su yayinda rawar da jikin sa ke yi ta tsanan ta kamar wanda aka jonawa wutar lantarki, to her kuwa ko a jikin ta, tana gama murnar ta ta sake shi ta tsugunna tana tsince kuɗin da ya zubar, har ta gama tsincewa yana nan daskare be ko iya ya motsa ba seda ta miƙe sannan ya iya ƙarfin halin juya mata baya da sauri dan baya son ko kaɗan taga damar sa.

Drawer dake gefe taje ta zauna tare da janyo landline ɗin wajen ta danna kiran customer care tunda ba waya a hannun ta balle tayi online shopping, ma'aikaciyar customer care ɗin ta zo ta bata kuɗin hannun ta 6k ɗin ta lissafa mata abubuwan da zata siyo musu na kayan sawa sannan ta nemi guri ta zauna bakin bed ta juya da nufin yi masa magana sedai wayam taga wajen ba kowa se ATM card ɗin da ke ƙasa, cikin rashin damuwa ta ƙara sa ta ɗau card ɗin ta koma wajen ta ta zauna.

A cikin toilet kuwa ya daɗe tsaye dafe da mirror ɗin wajen kafin ya iya dawowa hayyacin sa, he's totally out of word, be San me ze Kira recent scene ɗin ba, yanayin da ta shiga some minutes back was so unpredictable, be San da wane yanayi ya akaƙanta shi ba haka be san da sunan da ze Kira what he just experienced some minutes back ba, yanayin baƙo ne a gare shi dan ze iya rantse wa be taɓa samun contact da mace kamar yadda ya faru a tsakanin su ɗazu ba, it happened so sudden and unexpected, Kai baya jin ko yayi bayani akwai wanda ze fahimci abinda yaji a jikin sa ɗazu.
Chapter 59 · 0% Book details