Sashe 23
Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙarar takalmin Kisnah yasa Maigado kai kallon ta can, har tayi wanka ta canja rigar jikin ta zuwa wando three quarter da t-shirt mara nauyi ta saki gashin kanta da bata samu zuwa saloon yau dan gyarashi ba, ɗauke kanta tayi zuciyar ta na ɓaci ta maida kan wayar ta sedai ta kasa haƙura hakan yasa ta shiga satar kallon dukkan su biyu dan sosai taji baƙin cikin fitowar Kisnah da wannan shigar da haka kawai zuciyar ta ke faɗa mata zata iya burge Saraki da ita.
Zama kan one sitter gefen Saraki Kisnah tayi kafin ta saka hannu ta É—auke files É—in da ke kan cinyar sa da yasa ya buÉ—e idon sa kan ta, ajiye files É—in tayi gefen ta kafin ta É—auko bundle É—in 1k ta É—ora masa inda ta É—au files É—in, kallan kuÉ—in yayi kafin ya maida kanta cikin sigar kallon tambaya
"Gashi nan ka siya kayan amfanin da babu a ɗakin ka ka kuma ƙara kaya, haka ake bawa kowani sabon ma'aikaci da ze Fara aiki a gidan nan, ba wai dan raini ko wani abu ba se dan kyautatawa".
Da farko so yayi yace baya so sedai yadda ta ƙare bayanin yasa ya fasa hakan wanda da alama ta fahimci yana son rejecting shiyasa ta ƙarasa a tausashe.
"Thanks". Ya faɗa yana miƙewa bayan ya ɗau kuɗin itama ta ce masa "thanks also for the drive".
Fita yayi yana mamakin ta a ranshi, jiya ma haka tace masa thanks yau ma gashi ta kuma, to akan me zata gode masa bayan aiki yake mata kuma biyanshi zata yi, a karo na biyu ya kuma ganin hali me kyau tattare da ita.
Khamees ya samu da batun ɗakin kamar yadda yace ya kuwa rakashi part ɗin ma'aikata har ƙofar da aka saka tag ɗin sunan sa Ahmad dake can nesa da part ɗin su Kisnahn.
Bin ɗakin yayi da kallo cikin yaba tsarin ɗakin, ƙatuwar katifa ce me matuƙar taushi sabuwa dal cikin ledar ta se three sitter sofa daga gaban katifar kalar ash ita ma me kyau da ita, madaidaiciyar wardrobe me murfi biyu itama kalar ashe da ratsin fari a kusurwar ɗakin se curtains Suma Ash color se ƙaramar plasma TV dake jikin bango tare da kayan DVD da DSTV a ƙasan ta kan kyakkyawan ƙaramin glass TV stand, sosai yaji daɗin ganin har da Ac akwai a ɗakin dan baya shiri da zafi ko kaɗan.
Ƙarasawa yayi ƙofar toilet da ya hanga acan gefe ya buɗe ya shiga, fari tass ɗin tiles ne a banɗakin tun daga ƙasa har jikin bangon sa gaba ɗaya sedai na ƙasan manya ne na jikin bango kuma madaidaita, ba wani tarkace bane cikin toilet ɗin illa hand shower, water closet, tap, sink, mirror, bucket se ƴar cupboard me ɗauke da towels masu kyau, sabon brush and new sponge, se cleaning apparatus a gefe.
Ƙaramar low cut broom ɗin ya ɗauka ya zuba car wash me ƙamshi da ya gani cike cikin jarkokin faro manya har uku a ƙasan ya shiga sake wanke toilet ɗin duk kuwa da cewa a wanke yake, seda ya tabbatar yayi masa yadda yake so kafin yasa ruwa ya ɗauraye sannan ya tuɓe ya yi wanka da ruwa dan be siyo soap ba kuma babu sabulu a toilet ɗin, ɗaure da ɗaya daga cikin sababbin towel ɗin ya fito ya zauna kan sofa, wani ƙaramin towel da ya ware yanzu dan goge jiki yasa ka ya tsane ruwan jikin sa kafin ya maida jeans da rigar da ya cire ya ɗau key ya fita zuwa motar da suka fita jiya da ya kwaso kayan sa a ciki.
Fito da kayan yayi da gaba É—aya yayi wa leda biyu dan basu da wani yawa, kala goma ne gaba É—aya se toothpaste É—in sa da sabulai da mayukan sa ya kai É—aki kafin ya dawo dan rufe motar idanun sa suka sauka kan shopping bags biyun da ta bari cikin mota ta kuma ce masa nasa ne, kamar ya bar su ya maida mata se kuma kalaman Mami suka dinga dawo masa kan sa kamar lokacin take faÉ—ar su
"Ka Dena irin haka Saraki, sheɗan kawai ke maida alkhairi in an masa, ko mai ƙanƙantar abun da aka baka ko kuma girman shi ka karɓa ko dan wanda ya baka yaji daɗin baka raina shi ba balle abin hannun sa ko da bazaka yi amfani dashi ba kuma kayi godiya dan ya tabbatar kaji daɗi kuma ka yaba, ita kyauta tana zuwa ne da kyautatawa bawai raini ba kamar yadda kai kake gani, wanda ya baka kyauta bawai ya raina ka bane a'a yayi appreciating wani abu da kayi masa ne ko kuma dan ƙauna kawai dan akwai mutane da yawa a gari amma be bawa Kowa ba se kai , ka min alƙawarin zaki dinga karɓar kyauta indai bata zo ta sigar raini ko isgilanci ba".
Be manta kalaman da ya faÉ—a wa Mami ba a lokacin which is "I promise you Mami nah".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaukan bags ɗin ya nufi ɗakin dan be ga raini ko isgilanci tattare da Kisnah ba, wardrobe ɗin ya buɗe ya shiga jera kayan sa wanda be daɗe ba dan set goma ne, jeans da t-shirt ya cira ya saka kafin ya koma ya fara jera kayan da Kisnah ta siya masa, ko bai faɗa ba Allah ya sani kayan sun burge shi dan irin su ya saba sawa da ma wanda suka fisu, designer Kaya ne masu matuƙar tsada da kyau ta siya masa har kala sha biyar se wrist watch guda uku, silver, golden se black.
Godiya da addu'a yayi mata sosai a zuciyar sa tare da mata fatan shiriya daga dukkan abinda take aikatawa na ba daidai ba, kan katifar ya kwanta bayan ya shimfiɗa bed sheet ɗin da ya gani cikin wardrobe which is so clean se ƙamshi ma yake.
Kwanciya yayi cikin tunanin Mamin sa da ya saka shi gaba da yake ta faman dannewa sedai yanzu kam ya kasa, shaƙuwar sa da Mami daban ce da ba kowa ze gane ba, ƙaunar da yake mata bazata faɗu, itace ƙawar sa, yar sa, ƙanwar sa, haka kuma mahaifiyar sa shiyasa yanzu duk wanda ya sanshi a baya ya ganshi yanzu yasan ƙarfin hali ne kawai yake yi amma he's not well.
Haka ya cigaba da kwanciya har lokacin da akai knocking ƙofar shi ya tashi ya buɗe, ma'aikaci ne sanye da uniform ya ɗora rigar girki a kai se apron a kansa da zata shaida ɗaya daga cikin cooks ɗin gidan ne, miƙa wa Saraki plate ɗin hannun sa yayi yana sakin masa murmushi, karɓa yayi yana sakin masa murmushi shima kana ya koma ɗakin tare da rufe ƙofar.
Kan sofa ya zauna hannun sa riƙe da plate ɗin yana bin abincin da kallo kafin yasa hannu ya janye foil paper da aka rufe plate ɗin dashi, fried rice ce da ta yi kyau sosai a ido se rabin kaza a gefe da spoon shima nannaɗe cikin tissue, ɗaukar spoon ɗin yayi tare da ajiye plate ɗin gefe bayan ya maida foil ɗin ya rufe, toilet ya shiga ya sake wanke spoon ɗin thoroughly kafin ya koma ya zauna ya ɗau plate ɗin, bisimilla yayi ya fara cin abincin a nutse wanda yake nan ba yabo ba fallasa, wato dai ba wani daɗi gare shi sosai ba amma fa baza ace bashi da daɗi ba, ƙarar waya da yaji yasa yayi pausing hannun sa riƙe da spoon ɗin da ya ɗebo abincin, jin ƙarar sosai a ɗakin yasa ya ajiye spoon ɗin ya miƙe tsaye ya fara neman inda wayar take dan ba tasa bace take ƙarar dan ita tana gefen sa.
Can gefe ya hango landline kan wani ƙaramin fridge da be lura dashi ba tun da ya shigo, ƙarasawa yayi ya ɗau wayar tare da yin sallama, Muryar Kisnah yaji cikin maganar da ta sa ta kira shi batare da ta amsa masa sallamar ba.
"You get ready we're going out tonight, pls help me check if one dark blue car of mine is clean".
Ajiye wayar yayi bayan ya gama sauraren ta batare da ya amsa mata ba dan shima bata amsa masa sallamar da yayi ba ai, komawa yayi ga abincin sa ya ƙarasa cin iya yanda ze iya dan shi kam a dole yaci abincin dan shi fa be san wani abinci related to foreigners, yafi ganewa natural traditional dishes ɗin mu na Hausa shiyasa Mami da kanta take masa girkin sa.
Fridge É—in ya buÉ—e ya É—au bottle water da ya gani batare da ya kalli drinks É—in wajen ba sannan ya fita duba motar da tace, its clean amma dai yace a sake goge ta kar tace ba'a yi mata daidai ba.
ÆŠakin ya koma ya zauna a sofa looking at he's watch dan ganin ina lokacin sallah yayi, sedai to his utmost surprise se ma yanzu Æ™arfe É—aya yayi, alwala ya shiga toilet yayi kafin ya fita zuwa masjid É—in da ya gani gaba da gidan, sallar Azahar yayi tare da azkhar É—in bayan sallah kana ya dawo gidan, bacci yake son yayi sosai kafin la'asar dan kansa wani irin ciwo yake masa wanda yasan ba komai bane yaja illa damuwar da yake ciki da yawan tunanin da yake ga kuma ayyukan da jikin sa be saba da su ba duk da wata kusan biyu kenan da yake yin wasu kafin wasu su Æ™aru jiya...................âœï¸.
Â©ï¸ Ouummey 📚âœï¸.
☑ï¸Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 16 (8/8/2022 6:49 PM )
💠💠💠💠💠💠💠ðŸ’
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠ðŸ’
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.Aâœï¸*
_________________________________
              Page 1ï¸âƒ£6ï¸âƒ£