Sashe 44
Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nazari ya zauna yayi dan neman hanyar ɓullo musu tsawon lokaci kafin ya saki dariyar farin cikin samun wani solution ɗin, da sauri ya ɗau wayar sa ya shiga kiran Kawu da ringing ɗaya tayi ya ɗauka kamar dama jira yake.
"Kana ji ko Sama'ila, yanzu abinda za'a yi maza ka tafi Company ɗin furnitures, Zan turo mutane na da fake currency zasu siya set ɗin full three bedroom flat, amfanin da zuwan ka ze yi shine tabbatar da an karɓi cash ba transfer ba, na sani duk da haka ba durƙusar da gurin ze yi ba amma dai ai asara asara ce kuma ina da wanda zan tura wa kayan ya saye su daraja dan kayan gurin duk latest ne kuma ba ƴan ƙasar nan ba".
Shima Kawu washe baki yai duk da ba haka yaso ba, yaso ace wancan maƙudan kuɗaɗen kwangilar ne suka shigo account ɗin su sedai ba komai sa rage zafi.
Haka kuwa akayi, mutanen Alh Haladu suka yi shiga me kyau suka ɗau manyan motoci da kana gani kasan sun cika sun timbatsa, tarba me kyau manager ɗin wajen yayi musu aka gaggaisa kafin suka kawo batun siyan kayan da ya kawo su wanda a daidai lokacin Kawu ya ƙaraso.
Ciniki aka yi suka zaɓi kaya masu matuƙar tsada da kyau kafin akayi lissafi kuɗi ya tashi kusan miliyan 50 dan fa set ɗin 2 parlor and 3 bedrooms suka zaɓa, ana gama lissafi babban Alh cikin su yace yana zuwa ya koma mota ya ware adadin kafin ya ɗauko jakar da kuɗin ke ciki zuwa gasu Kawu, manager ya so yin magana sedai ganin yadda Kawu ya karɓe kuɗin da sauri yasa dole ya rufe bakin sa, buɗe jakar Kawu yayi gaban kowa ya fito da kuɗin aka ƙiƙƙirga aka tabbatar sun kai kafin aka shiga loda musu kayan cikin babbar motar da suka zo da ita.
Ana gamawa suka yi sallama da kowa suka É—au hanya Kawu na ta washe baki haka shima manager yaji daÉ—in cinikin dan sun tabbatar musu da suna dawowa nan da two days akwai mansion É—in su da zasu sawa furnitures Kuma a wajen su za'a siya komai.
Manager Kawu ya bawa kuÉ—in kan yaje yakai bank in ya tashi aiki shi ze wuce K&S couture, da haka yabar manager ya fita daga building É—in yana dariya a ranshi ga kuma farin cikin kuÉ—in da zasu samu har miliyan 50, ko ba komai yasan ke tashi da twenty five millions.
**********
Ƙarfe biyar ya tashi daga aiki ya wuce wajen Kisnah tare da kiran ta ya shaida mata yana waje, ba ɓata lokaci ta fito suka wuce, sun kusa ƙara sawa take faɗa masa
"Yaya yau ina da zuwa cinema by 8pm, za'a haska Film É—in jarumi sharukhan Chennai express".
ÆŠan kallon ta yayi ta gefen ido yaga yadda take ta washe baki tsantsan farin ciki rubuce ka fuskar ta, be san ta wace hanya ze sami damar hana ta zuwa cinema ba ayanzu Amma he pray Allah ya kawo masa wata damar da ze yi hakan ko da nan gaba ne.
Gyaɗa mata kai yayi tunda bashi da wani option se hakan, gaban wani suya spot tace ya tsaya, atm ɗin ta ta miƙa masa tana lissafa masa abinda take so ya siyo ɗin, fita yayi bayan ya gama sauraren ta batare da ya karɓi atm ɗin ba, komai da ta lissafa se da ya siyo ya kawo mata sannan ya shiga motar ya cigaba da tuƙin sa, kaɗan kaɗan take kallon sa tana sakin murmushi, kusan so huɗu kenan indai zata siya abu se ya siya mata batare da ya bi takan kuɗin ta ba kuma tana jin daɗin hakan.
Suna ƙara sawa gida ta ɗauki ledar ta tare da yi masa godiya ta fice daga motar cike da farin ciki, bata ƙarasa flat ɗin ba suka haɗu da Awwaf, bata ko kalle shi ba kamar yadda ta ke masa tun da taga ya fara neman raina ta wai har ze kalle ta yace yana son ta, gaba tayi ta bar shi a wajen sedai kafin ta ƙara taku uku taji an janyo ta an rungume, fisge jikin ta tayi daga gare shi tare da ɗagowa cikin zafin rai da tsananin baƙin ciki da takaicin abinda yayi mata ta haske fuskar sada kyakkyawan marin da se da ya ɗauke masa jin sa na wasu sakanni.
Ƙara masa take ƙoƙarin yi se kuma ta fasa ta shiga nuna shi da yatsa ta fara masa masifa da cin mutuncin da duk wanda ke compound ɗin ke iya jiyo ta dan dama suna tsaye a compound ɗin ne ta hanyar shiga flat ɗin su
"Wane irin ɗan akuya ne kai da har rashin kunyar ka takai ka kai ƙazamin hannun ka jikina da wata manufa, nace waye kai da har kake da wannan guts ɗin ko an gaya maka ni ɗin sa'ar kace ko kuwa sake war da ka samu ce tasa har kake tunanin ni ɗin daidai nake da kai bari ka kawo min raini, to bari kaji wallahi wanda ya isa da kai ma be isa ba balle kuma wani banza kamar ka, an warning You for the first and last time, na rantse da Allah duk sanda ka kuma gwada irin haka se ranka ya ɓaci fiye da yadda kake zato, wannan ɗin ma Sa'a kaci na dubi matsayin mahaifiyar ka wajen ƙanin uba na if not wallahi matakin da zan ɗauka kan ka ko da kuɗi aka baka akace ka kuma trying this nonsense ba zaka kuma ba, pathetic peace of trash kawai, mtseww".
Ta ja tsaki kafin tayi gaba cikin ɓacin rai, Mommy dake tsaye tana kallon komai ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba sedai sanin ba abinda zata iya yi ko cewa yasa bata ƙarasa wajen ba ta juya ta shige falon ganin Kisnah tayo hanyar.
Ko kallon Mommyn bata yi ba ta nufi steps zata wuce É—akin ta se kuma ta dawo ta tsaya gaban Mommyn tana jijjiga jiki tsabar bala'in da yake cinya dan ji take kamar ta koma in da ta bar banzan ta rufe shi da duka
"Haleema ki jawa ɗan ki kunne akaina, be san wace ce ni bane da alama shiyasa har yake ƙoƙarin kawo haukar iskancin sa kaina,to salin alin tun kafin in bayyanar masa a ainihin Kisnah ta ya fita a hanya ta in Kuma ba haka ba wallahi zan bi takan sa, har shi waye da ya isa ya kai ƙazamin hannun sa jikina, waye shi waye ya tsaya masa eye, ke kin San ni kin San abinda zan iya dan haka zaki iya gargaɗin sa, dan in ya kuma ban san iya abinda zan aikatawa banza ba".
Tana ƙare isar da saƙon ta ta wuce sama da ɗan gudu gudu har ta haye, ƙofar ma seda ta san tana fushi dan yadda tayi banging ɗin tada akwai wani a kusa ba ƙaramin ciwo zata ji masa ba.
Kayan jikin ta ta fara ciccire wa tana watsar wa har se da ta cire komai na jikin ta kafin ta ƙarasa toilet, ruwan sanyi ta sakar wa jikin ta ta tsaya a ciki har se da ta ji ranta yayi mata sanyi kafin ta yi wanka ta fita, tsane jikin ta tayi da towel sannan ta zura guntuwar red gown iya gwiwa ta warware chignon ɗin da tayi wa kanta ta maida shi French plait ta saki jelar a bayan ta.
Ledar ta da ta shigo da ita ta fito parlo ta ɗauka tare da nufar mini kitchen ɗin ta, plate ta ɗauka ta wanke duk da fess yake ta goge da duster sannan ta juye abin cikin ledar a kai, lumshe ido tayi cikin zaƙuwar fara cin gasasshiyar kazar wadda ta sha kayan haɗi kamar me, take cikin ta ya fara kukan yunwar da ta yo guziri daga office dan yau bata yi launch ba aiki ya ɗauke mata hankali.
********
Juyawa yayi da ledar hannun sa ya wuce É—akin sa bayan yayi locking motar, yaji daÉ—in yadda tayi wa Awwaf sosai dan hakan na nuna ta fara sanin ciwon kan ta kenan, a ganin sa da da kanta take rungume maza yanzu kuma tana fighting masu rungumar ta haka ma Nasara ce.
Poor Saraki be san ita Awwaf É—in ne ta raina wa hankali ba ba wai dena rungumar maza tayi ba duk da an daÉ—e hakan bata faru ba tun da kullum tana hanyar office to a ina zata gan wanda ta sani balle har ta runguma?
Wanka yayi ya canja kaya kafin ya zauna kan ledar sa shima ya shiga aika ta ciki, sosai gashin ya yi masa daɗi abaki dan haka yake ta lumshe idanu, abin dariya har ya cinye ma be san ya cinye ba seda yaji ledar ƙwalam kafin yayi murmushi ya tafi toilet ya wanke hannun sa.
Kitabul kaba'ir É—in da ya fanso recently ya É—auko ya shiga dubawa, lokacin da aya baro gida yayi nisa sosai sedai kwana biyu da yayi be duba ba ya É—an samu tangarÉ—a so ya koma baya ya shiga karanta wa cikin ransa.
Seda akayi kiran sallar magrib ya ajiye ya yi alwala ya fita zuwa Masallaci akayi sallah tare da shi har Isha sannan ya fito, da jallabiyyar jikin sa ya É—au key É—in motar da suka dawo da ita ya fita dan kai ta cinema Kamar yadda tace.
Cikin shigar jeans da half tigh shirt ta fito sedai ta saka brown overcoat a kai ta ɗora sou'wester a kanta ƙafar ta sanye da brown wedge shoe da ya mata masifar kyau.
BuÉ—e motar tayi ta shiga dan shi dama tuni ya shige ciki ita kawai yake jira, tana shiga ya tashi motar suka fita daga gidan bakin ta É—auke da addu'a.
Suna ƙarasawa ya yi parking a lot ɗin wajen tare da kashe motar yana jiran ta fita.
Karkatowa tayi tana kallon shi cikin É—an marairaice fuska
"Yaya pls mu shiga tare da kai kaima ka kalla, kaga fa kai kaÉ—ai zaka zauna a nan É—in har kusan 3 hours".