← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 64

Sashe 38

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka cigaba da tafiyar kurame dan yau be sa ko ɗaya ba daga karatun har wa'azin har suka ƙarasa, kamar dai kowane daga cikin companies ɗin wannan ma seda akayi screening ɗin su irrespective of wai me company ɗin ce da kan ta, wannan doka ce ta tun mahaifin ta na raye dan gudun afkuwar matsala ko tashin hankali se dai a yanzu ga Kisnah ita bata ga wani amfanin hakan ba tunda a haka ba'a fasa handama da rashin gaskiya a cikin ma'aikatan ba.

Wajen da take ajiye mota ta nuna masa ya yi parking kafin suka fito suka jera zuwa cikin babban building É—in, gaisuwar da receptionist É—in ke musu ta amsa tana mamakin irin kallon da biyu daga ciki suka bi Saraki dashi.

Pretending gaisawa da ma'aikata tayi hakan yasa ya ɗan yi gaba kafin ya tsaya jiran ta tun da be san kan wannan Company ɗin ba, da wannan damar ta yi amfani wajen ƙare masa kallo dan san sanin dalilin kallon da receptionist ɗin suka bishi da shi.

Baƙin dogon jeans ne a jikin sa se long  sleeve shirt Fara tas ƙafar sa sanye da baƙin brogues da ya sanya, ba ƙaramin kyau yayi ba cikin shigar tun bare gashin kan sa dake ƙyalli wanda ya fito ta ƙasan beret ɗin da ya sanya wa kan sa, se yanzu ta gan dalilin da ya sanya suka wani watsa masa ido kamar zasu cinye shi da su, bata san me yasa ba se ta tsinci kan ta da jin haushin su wanda ya tursasa mata juyawa ta jefa musu wata ƴar iskar harara kafin tayi ƙwafa ta wuce inda ya tsaya suka nufi lifter.

Haushi sosai ya cika ta se cika take tana batsewa har suka shiga office ɗin, zama yayi kan kujerar dake gaban ƙaton table ɗin yana bin ta da kallo yadda take ta kumbura fuska kamar wadda aka zaga, kau da kan sa yayi yana ayyana may be ita da employees ɗin ta ne.

A hankali yake zagaye idanun sa cikin office ɗin sa yana jinjina girman gurin dan kuwa yaci ayi madaidaitan offices kusan huɗu ko uku, tsaruwar office ɗin ta burge shi dan ba'a wani cika tarkace ba amma yayi kyau sosai, ga kuma tsaftar da ya gani na wajen dan duk da bata cika shiga office ɗin ba amma a share suka tadda shi yana tashin ƙamshi.

Zama tayi ita ma kujerar dake gefen sa ta juya ta yadda zatai facing É—in shi kafin ta soma magana cikin sanyin murya da fatan ya yarda da batun da zata kawo masa.

"Kamar yadda kaga gidan mu nasan ko ban faɗa maka komai ba kasan kawu da Mommy ba iyaye na bane, kawu ƙanin Abbu na ne da nake rayuwa tare da su currently, ba ni da wa bani da ƙani ni kaɗai ce wajen parents ɗina, kwanakin baya kasan kaɗan daga cikin matsalolin da na ringa samu daga wasu cikin companies ɗina hakan yasa na yanke shawarar yin amfani da ƙanƙanin lokacin da nake dashi kafin mu fara project dan kula da harkokin kasuwanci na sedai bazan iya ni kaɗai ba dole se da taimakon wani, Please Yaya kayi min favor ɗin karɓar aiki tare da ni, na yarda da kai nasan ba zaka cuce ni ba, ina buƙatar ka sosai cikin tafiyar kasuwanci na Yaa, alamu sun nuna akwai masu son ganin bayan dukiya ta dan haka suke min zagon ƙasa, nayi iya ƙoƙari na wajen ganin nayi tracing ɗin su sedai na kasa samun dama".

Kallon ta kawai yake tun da ta fara magana har ta ƙarasa kafin yayi ajiyar zuciya

"And what about shi kawun, ina ce shike kula da komai na companies É—in?".

"Shine yaa, amma bana gane komai a abubuwan da yake jagora, a lissafin shekarar da ya gabata da akayi lissafin shekara me makon ace an sami riba se ma kuɗin Company da ya dulmiya, kuɗi ba ƙanana ba fa, haka ma wannan shekarar da muke ciki yanzu muna wata na huɗu ne amma kullum cikin cases ake na ɓatan kaya, kuɗi, rashin maida hankalin ma'aikata and many more problems, beside this kawu ya Fara manyan ta dole se ana taimaka masa banda haka ma kaga companies ɗin kusan biyar ne dole baze yiwu ace mutum ɗaya ke controlling abubuwan su ba in kuwa akace haka za'a yi dole a ringa samun matsaloli kamar yadda muke fuskanta yanzu".

A hankali ya É—an gyara zaman sa cikin kujerar kafin ya kalle ta sosai

"Kin taɓa ganin an ɗauki mutum aiki ba takardu? Ko kuwa a ina za'a nemo takardun da za'a saka cikin file ɗina? Kin dai san dole a buɗe min file kamar kowane ma'aikaci ko, that aside, se wa ya dinga driving ɗin ki?".

"Is not a big deal Yaa, se na nemi new drive shikenan, maganar takardu kuma ai Company É—in na wa ne ina da right É—in kawo duk wanda na yarda dashi ko da kowa ne yarda ba in as much as na yarda ni shikenan".

"Okay will get to think about it". Ya faÉ—a yana É—an relaxing cikin chair É—in, marairaice fuska tayi dan Allah ya na gani so take ta san matsayar da suka cimma wa ko hankalin ta ya kwanta, yanzu kam she has no peace of mind seeing her father's hustle been wasted

"Dan Allah fa nace tun farko yaa, Abbu na yasha wahala kafin ya kafa companies É—in nan yaa bana son wahalar sa ta tafi a banza, ka taimaka pls".

"Tun da kin matsa then fine na amince amma ina da sharaÉ—i".

Cikin murnar da ta cika ta ta matsin da sauri kamar zata faÉ—a masa tana washe baki

"Naji daÉ—i sosai yaa, ban damu da sharaÉ—in naka ba dan zan yi komai in har zaka yarda, faÉ—a min meye sharaÉ—in".

ÆŠan jan fasali yayi kafin ya tsare ta da idanu

"SharaÉ—in ba wani me tsauri bane, kawai ban yarda da batun É—aukar new drive bane, I'll be driving you and also be working, and the last shine you'll be dressing decently and abandon clubbing, that's all".

Shiru Kisnah tayi yayinda duk wata murnar ta ta koma ciki, she's just thinking of how can she stopped clubbing at once, abun ya riga ya shiga jinin ta haka in ma barin ne tasan sedai ta rage bit by bit Kuma haka ya kamata yace in ma baya san clubbing É—in se yace ta rage ba ta daina ba.

Ɗauke kan sa Saraki yayi tare da ciro phone ɗin sa ya shiga pressing kamar ma hankalin sa baya kanta yayinda yake kallon ta a kaikaice praying internally Rabb yasa ta yarda da sharaɗin sa dan haka kawai abun ya zo masa ganin yadda ta damu da dukiyar yasan wanna ne kaɗai hanyar da ze bi wajen daƙile clubbing ɗin ta though ta kwana biyu bata je ba sedai yasan saboda exams da kuma tafiyar da suka yi ne yasan tana gab da cigaba da zuwa tunda sun dawo yanzu.

Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tare da neman seat ɗin da ta tashi ta koma ta zauna tana me cigaba da tunani, a hankali kamar wadda akayi wa dole ta furta

"Na amince".

ÆŠagowa yayi ya kalle ta ya É—an yatsuna fuska irin kamar an takura masa É—in nan

"See ba dole bane ba fa, naga duk kin wani yi sanyi, abin nan zaɓin ki ne, you've the choice dan haka in Baki yardan ba i don't give a damn, dama zan yi saboda Abbun ki da kika sako, so in ranki be kwanata ba a bar maganar".

Da sauri ta girgiza masa kanta tana ƙoƙarin more damuwar kan fuskar ta dan kar ya fasa, she have no hope in Bashi ba so she won't let him go

"Na yarda fa yaa, ba wai ina kokonto bane in adai kawai tunanin yadda zan daina clubbing rana É—aya bayan am used to it though da wahala amma zan yi hakan insha Allah, I'll do it for Abbu na surely".

Sauke ajiyar zuciya yayi a ɓoye tare da yin hamadala yana godewa Allah da ya bashi damar fara saita ta kan hanya cikin sauƙi, he pray one day ta zama yarinya ta gari insha Allah.

Gaban computer ta dake office ɗin ta koma ta zauna tare da typing abun da be san me take rubuta wa ba se dai hannun ta da yake jin suna motsa keyboard ɗin cike da ƙware wa, tashi tayi ta ƙara sa gaban printer da ke cikin office ɗin ta ciri wata takardu guda uku ta dawo kujerar da ta tashi wadda take opposite ɗin sa ta zauna tare da tura masa papers biyu

"You sign this papers, wannan ta farkon takardar ɗaukar ka aiki ne, ta biyun kuma takardar oath na yadda da dukkan wasu rules and regulations na company ne, ragowar takardun ka kuma zamu je court muyi affidavit ɗin ɓatan documents, ina tunanin shikenan ko".

Shiru yayi yana kallon ta kafin a hankali ya motsa bakin sa

"I thought ƙarya haramun ne a musulunci ko".

Kallon shi tayi sosai wannan karon cikin ƙosawa da halayyan nashi na yau

"Haba mana yaa, ai ni dai nayi ƙaryan ba kai ba ko, to zunubin a kaina, haba mutum kamar me wanna ko liman albarka". Ta ƙarashe ƙarshen sentence ɗin can ƙasa ƙasa kamar me ƙunƙuni

Murmushi yayi dan sarai yaji abinda ta faÉ—a so ya kalle ta yana É—aga gira

"Miss kamar kina magana ko?".

Wanna karon sosai ta ɓata fuska dan Allah ta gaji da gaske

"Ni ba abinda nace fa".

"Oh i thought magana kika yi".

Girgiza masa kai kawai tayi dan ta fahimci neman magana yake ita kuma bazata biye masa ba balle har ya sami abin fakewa yace ba zai karɓi aikin nan ba dan ina hakan ta faru bata san kuma ha zata yi ba.

She really need to have a partner da zasu yi joining hands wajen ya ƙar ma ha'in tan companies ɗin ta su kuma ciyar dashi gaba se dai bayan Sarakin bata ganin akwai wani da zata iya yarda dashi a kan batun.
Chapter 38 · 0% Book details