← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 64

Sashe 28

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma kafin ta fita addu'o'i ya mata sosai cikin mata fatan dawwamammiyar nasara kafin ya sata karanta wasu addu'o'i kafin ta fita daga motar, itama bata wani damuwa take yin duk abinda yace dan zaman su na kwanakin yasa ta saba da yadda yake da yawan addu'a dan har sallama yanzu takanyi sa'i da lokaci kafin ta shiga waje.

A wajen sa hakan ma nasara ce shiyasa be fita takurawa da se ta canja komai a lokaci guda ba dan yasan hakan ba me yiwuwa bane kuma baya san taga kamar takura ne shiyasa yake bi da ita a hankali yadda zata yi komai cikin ra'ayin kanta ba tursasawa ba haka kuma ya fahimci in yace ce tursasa itama ɗin ba kanwar lasa bace ba tanƙwaruwa zata yi ba.

Cikin ikon Allah tayi jarabawar ta ta gama lafiya tare da taimakon Saraki da kacokan yanzu ta ɗau duk wata girmamawa ta bashi, Ya sama Ya ƙasa take kiran shi haka yanzu ya san abubuwa kaɗan kaɗan game da ita da wasu daga cikin dukiyar ta wanda da kanta sanar dashi dan samun solution kan matsalolin ɓatan kuɗi da ta nemi shawara a wajen shi.

Bayan dogon nazari ya bata solution ɗin da da taimakon Ubangiji se gashi an yi nasarar gano me wannan account ɗin da kuɗaɗen nan suka shige, wani ƙaramin ma'aikaci ne dake da post ɗin gyara files, mamaki ya kama su kamar me da tunanin taya ya kasance shi, tawace hanyar har yake samun access haka, dole akwai wani behind his shadows sedai anyi yin duniya mutumin ya faɗi wa ya sashi ya kafe kan ba kowa, dole aka miƙa shi kotu aka yanke masa hukuncin shekara biyar a prison tun da ya kasa biyan tarar da aka yanka masa ta miliyan uku, sosai Kisnah yaji tausayin sa har tana batun zata ce ta yafe sedai tuni Saraki ya dakatar da ita dan irin su dole se ana hukunta su dan ba wai ze Dena bane ko tace ta yafe ɗin.

Kayan abinci yasa ta siya ta kai gidan mutumin da a kallon farko da tayi wa gidan ta daÉ—a tabbatar da tabbas wani ne ya sashi dan É—aki É—aya ne a gidan se kitchen da toilet É—in da aka zagaye da kwano, jijjiga kai kawai tayi kafin ta saka almajirai aka shiga da kayan abincin da suka ciki booth da su.

Godiya ba kama hannun yaro matar sa ta shiga yi ita da Æ´aÆ´an ta mata biyar se maza biyu dan dama cikin matsalar abincin suke.

Yanzu ma zaune yake kan É—aya daga cikin kujerun office É—in ta na K&S shopping mall da ke gaban table É—in ta wanda shine karo na farko da ya shiga office É—in shima bisa dagiya da magiyar da tayi ta masa har da guntun hawayen ta, laptop É—in da take aiki da ita a office ne ta turo gabam sa kafin ta zagaya ta gefen sa ta shiga yi masa bayani tana daddanna keyboard É—in.

Kwanan nan aka nemi wasu kaya aka rasa a mall ɗin kuma an rasa ta ina suka bi suka sulale daga cikin mall ɗin, kaya ne bana ƙananan kuɗi ba dan kusan rabin ribar da aka samu a wannan shekarar cikin mall ɗin suka sa suka yi order sedai kwana uku da zuwan kayan aka nemi kusan rabin su aka rasa, abinda ya jawo babbar matsala kenan aka shiga binciken ina kayan suka yi sedai har yau an kasa ganowa shiyasa tana gama exam ta maida hankalin ta kan mall ɗin ɗan yana cikin best kadarorin ta da take matuƙar so dan purposely dama ita aka buɗe wa tun iyayen ta na da rai.

Yanzu ma bayanin duk ma'aikatan dake cikin mall É—in take masa da post É—in kowanne da kuma albashin da yake É—auka a duk wata, É—aya bayan É—aya ya fara scrolling through list É—in har ya gama kafin ya ajiye mouse É—in ya fuskance ga sosai.

"A yadda na bi bayanan duk ma'aikatan ban ga komai ba sedai akwai strategy da zamu bi, for now ki sa a tara su gaba É—aya a É—akin meeting in kuna dashi in babu kuma su taru a tsakiyar mall É—in bayan an sallami kowane customer".

Gyaɗa kanta tayi da sauri kafin ta ƙarara wajen landline ɗin dake kan table ɗin ta ta daddanna wasu numbers ta kara a kunne, bata tsaya amsa sallamar da yake mata ba bare gaisuwar da ta biyo baya

"Ka sa a sallami kowane customer da yake cikin mall É—in nan da mintina goma ya zama ba kowa a ciki sannan ka sanar da kowane ma'aikaci ya hallara a meeting hall in next 30 mins".

Ajiye wayar tayi ta juyo gare shi
"Na sanar dasu Ya, what next?".

"In suka taru Zamuyi addressing issue É—in tare da yin barazana sosai kafin mu examining facial expressions É—in su, insha Allah zamu iya gano criminals É—in ta haka".

Faffaɗan murmushi ne ya wanzu saman fuskar ta kafin ta sara masa gani da ƙamewa tana faɗin
"Salute you sir".

Girgiza kansa kawai yayi dan yanzu ya fara sanin halin ta na surutu da barkwanci dan har ya dena damuwa, ƙarkari ya bata amsar abinda yaga ze iya Wanda baze iya ba kuma ya kalle ta kawai..........................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 19 (8/10/2022 10:16 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 1️⃣9️⃣

_____________________📖 Kamar yadda ta bada umarni haka akayi, 30 mins after manager ya kirata yana tabbatar mata da duk ma'aikatan na hall kamar yadda tace ayi, amsa masa tayi da gata nan zuwa ta ajiye wayar tana kallon Saraki

"Yaa suna wajen mu kaÉ—ai ake kira".

Nodding head ɗin sa yayi yana miƙewa tare da gyara rigar yadin kuftar jikin sa da akayi wa plain ɗin ki sedai ba ƙaramin amsar shi yayi ba kamar a sace a gudu, yana cikin set goma da ya ɗin ka cikin kuɗin albashin sa na farko da ya ɗauka two weeks back, yadi kala huɗu se shadda huɗu boyle biyu.

Clutch ɗin dake haɗe da rigar jikin ta ta ɗauka kan table ɗin da ta ajiye ta farkon shigowar su ta bi bayan sa ɗan tuni ya fita. Bakin ƙofar ta tadda shi dan haka itama ta tsaya sedai kafin ta kai ga tambayar me yasa ya tsaya ya riga ta nuna hanya tare da faɗin

"You lead me".

Bata yi musu ba tayi gaba ya biyo ta a baya dan ta san be san wajen ba to mutumin da ya fara shigowa mall É—in yau taya de san É—akin meeting É—in su.

Ƙaton ɗaki ne da kana shigar da zaka sheda na meeting ɗin ne saboda ƙaton table ɗin da ya zage yi ɗakin duk girman sa kuwa se kujeru dake jikin sa wanda a yanzu ma'aikatan wajen ke zaune a kai se kujera ɗaya da ba kowa dake gefen dama ga kujera guda ɗaya tal dake can gaba tana facing table ɗin wadda itace akayi purposely sabida ita.

Miƙewa gaba ɗaya ma'aikatan suka yi cikin nuna girmamawa, kujerar da manager ke kai wadda ke gefen daman ta ya miƙe da sauri ya koma cikin ma'aikatan dan akwai two vacant seats, tun kafin ma ya nemi wajen zama ta ƙarasa da sauri ta zauna kan kujerar da manager ya tashi kafin cikin muryar ban girma ta nuna masa kujerar da ita tayi supposing ta zauna.

"Please have your seat sir".

Shiru yayi cikin Binta da kallon bangane me kike nufi ba yana sake haɗe rai, haɗe hannayen ta tayi alamun Please tana sake roƙon sa da ido, harara ta yayi kafin ya maida duban sa kan ma'aikatan da wasu suka sunkuyar da kai yayinda wasu suke bin su da ido kamar television mamaki rubuce ƙuru ƙuru kan fuskar su.

Ɗan gyaran murya yayi kafin ya zauna yana fuskantar su kafin a hankali ya shiga bin su da ido cikin son ƙayyade adadin su wanda be wani sha wahala ba ya ƙirge su, su 35 ne ma'aikatan ciki dan uniform ɗin su ya banbanta da na securities da suke 10.

Cikin sassanyan Muryar sa ya soma da gaishe su gaba É—aya

Good afternoon all".

ÆŠan shiru yayi ya basu damar amsawa kafin ya cigaba

"Mun taru a nan bisa dalilin da ba na haufin kowa ya sani, wanda be sani ba ma ina farin cikin sanar dashi a yanzu cewa mun taru a nan ne kan dalilin ɓatan kaya da muka fuskanta sati da ƴan kwanaki da suka wuce, ba wai mun tara ku a nan dan binciken wanda ya ɗau kayan bane, a'a mun tara ku a nan ne dan sanar da ku mun yi nasarar gano wanda yayi hanyar ɓatan kayan wanda alhamdulillah muna kan tunanin tura case ɗin court........". Ya ɗan dakata cikin bin fuskar kowanne da kallo har idanun sa yayi nasarar sauka a inda ya dace dan yayinda ragowar kowa ke garin ciki da godewa Allah kan nasarar da aka samu me aikin yaƙe kawai yake yi haka kuma ga duk wanda yasan malamar aikin lawyer kallo ɗaya ce masa ya dasa alamar tambaya akan sa da kuma look ɗin da idon sa ke fitar wa.

"Sedai kafin mu miƙa me wannan aiki court zamu bashi dama, zamu bashi dama ta ƙarashe wato dawo da kayan salin alin ba tareda kowa ya sani ba haka batare da mun tona masa asiri ba".
Chapter 28 · 0% Book details