← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 64

Sashe 17

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_______________________📖 Gudu take sosai duk da ba haka ta saba tuƙi ba dan tana san isa da wuri, a yanzu bata da burin da ya wuce ta ganta gaban Mommy dan su zata, zafin da zuciyar ta take mata a lokacin ba kaɗan bane.

Gaban wani madaidaicin gida ta tsaye tare da yin horn, da sauri me gadin ya buÉ—e mata mota dan a kwanan nan ya gane ta saboda Wannan shine zuwan ta gidan na uku.

Parking tayi ta fito hannun ta riƙe da ledar da tayi wa Mommyn shopping kamar yadda ta turo mata text ɗin abubuwan da take buƙata, bakin madaidaicin falon ta tsaya tare da murɗa handle ɗin ta shiga.

Muguwar harara wata kakkaurar babbar mace ta maka mata tana jan tsaki

"Yanzu kuma me kika zo yi, Ni kam na shiga uku da wannan takurar, ita uwar ki ta kasa zama gidan ubanki saboda baƙin hali ta zo nan ta tare min kema kuma kin takura min da zirga zirga kamar me neman gafara, to wallahi baze yiwu ba, ko ki ɗauke kafar ki daga gidana ko na tarkata uwar ki na kora ku gaba ɗaya".

Zuba mata jajayen idon ta Megado tayi cikin tsananin ɓacin rai da takaici yadda ƙanwar babar ta ke musu cin kashin da ta ga dama dan kawai Mommy na zaune gidan ta, baki ta buɗe zata maida mata martani sedai tuni Mommy da ta fito daga ɗakin yara inda take kwana ta rufe mata baki da hannun ta kafin ta ja hannun Megadon zuwa ɗakin da ta fito.

Harara Aunty ta bi bayansu da ita tana sakin ƙananun maganganu sedai ko kallon ta Mommy batayi ba ta shige da Megado dan in tace zata tanka yanzun nan ƙanwar tata me Huna hasiya zata nemi yi mata tijara.

Fusge bakin ta Megado tayi bayan sun zauna kan wata three sitter ƙwalli ɗaya dake ɗakin se katifun yaran Aunty Hasiyar, Ido ta zubawa Mommy ganin yadda cikin kwana uku kawai ta fara yin baƙi ga wata ƴar rama da tayi again dan mugunta  kawu yayi mata ya faki idon ta ya kwashe ATM cards ɗin ta gashi ƴan kuɗin da ke hannun ta lokacin dubu da biyar ne kawai, nan gidan Aunty Hasiya kuwa ba wani jin daɗi ake ciki ba compared to gidan da ta baro, ba AC se fanka, ba ruwan roba se pure water, ba different dishes se ɗaya da matar gidan taga damar dafawa gashi tun da tazo a wannan three sitter ɗin take kwana dan Aunty tace bata da spare mattress Kuma ragowar na ƴaƴan ta ne sedai tai manage da kujerar.

Katse mata tunani Mommy tayi da dafa ta
"Yanzu Megado ba zaki sa ubanki yace na dawo ba, kina fa kallon rayuwar da nake ciki gidan wannan shegiyar yarinyar".

"Wallahi Mommy ya ƙi ko saurara ta amma abinda nake gani kawai me ze hana ki tattara mu koma, ai ba dole se ya san kin dawo ba ko?".

Zaro ido Mommy tayi
"Ashe kin manta tijarar ubanki, kaɗan daga aikin sa ma ya iya sakina kan hakan, Ni a ganina kawai zan kira ƴar iskar yarinyar can in bata haƙuri a wuce wajen, ragowar shirin mu kuwa se mu yi shi ta ƙarƙashin ƙasa ko".

"Wallahi sake raina mu zata yi Mommy, adai nemo wata shawarar ba wannan ba".

"Dole dai ita za'a yi Megado dan fa kin san in har ba ita tace ya dawo dani ba wannan uban naki da baƙin halin sa ze iya bari inyi wata ɗaya ko biyu a gida, ke har fiye ma wallahi".

"Ai sam Daddy be yi ba wallahi, Ni ban san me ya kaiki ma auren shi ba tun farko, shi abu ba kuÉ—i ba, ba ilimi ba, ba wani kuma kyau ba se shegen tsayi kamar me, yanzu dai jini yadda ya cuceni ya gada min tsayi kamar ba mace ba".

"Hmm Bari kawai, Ni kaina ban san me yaja ni ba a lokacin, kin san dai ƙaddara amma yadda nake da kyau na da diri a ƙuruciya ai be kamata na ƙare a wajen shi ba, yanzu dai ba wannan maganar ba, bari kiga in kira waccan sheɗaniyar dan in so samu ne in koma gidan nan yau dan wallahi na wahala matuƙa".

Mommy ta ƙare maganar tana dialing number Kisnah kana ta cigaba da faɗin

"Wai hatta caji fa a gidan nan bani da damar yi se ace in bada caja shiyasa yanzu haka 20% ne kawai dani".

"Ai wallahi Aunty Hasiya se ta san ba tada mutunci, banda arziƙin kina gidan ta ita har ta isa ta yi min ko da kallon banza ne balle zagi".

Da sauri Mommy ta nuna wa Megado tayi shiru ta hanyar sa hannun ta a bakin Megadon jin wayar na ringing.

**************

Cikin mall É—in suka shiga inda Kisnah ta shiga lodar kaya kamar ba da kuÉ—i za'a biya ba, cart huÉ—u ta cika ma'aikata na bin ta dashi a baya dan shi kam Saraki tun da suka shigo ya nemi waje É—aya ya tsaya.

Ɓangaren kayan maza ta koma ta shiga jida kamar ba zata dena ba har se da ringing ɗin wayar ta ya tsaida ta kafin ta ƙarasa kusa da Saraki ta miƙa masa ATM card ɗin ta tayi masa alamar ya bi ma'aikatan suje a biya ita kuma ta tsaya amsa kiran, har yayi gaba ya tuna bata faɗa masa pin ɗin ba dan haka ya koma

"Oh sannu fa, ashe kece, to ya hutu fatan kina jin daÉ—i tare da enjoying zaman".

Sentence É—in da ya shiga kunnen shi kenan da ya iske tana faÉ—a cikin salo na rainin wayo, shiru tayi cikin sauraren Mommy kafin ta saki dariya

"Ke É—in uwa ta? Wai Mommy nah! Mommy my foot kinji, Baki da wani matsayi wajena sama da na matar kawu na haka sunan ki a bakina da zuciya ta Halima ne ko ba haka gyatumi ya raÉ—a miki ba".

Daga can ɓangaren Mommy ta cika da takaici da ɓacin ran wulaƙancin Kisnah sedai bata da yadda zata yi, nema take dole ta danne komai a ranta, dan haka ta ɗan saki murmushin da be kai ciki ba

"Hakane sunana Halima, sedai duk mu ajiye wannan a gefe, dama na kira ne in baki haƙuri dan Allah kisa kawun ki ya dawo dani, na miki alƙawari Megado bazata kuma shiga sabgar ki ba".

Jinjina kai Kisnah tayi
"Amma nayi mamakin jin kinyi laushi cikin kwana uku, ashe dama ke É—in kura ce da fatar damisa, damisar kwali me bawa yaro tsoro, anyways tun da kinyi apologizing ki shirya kayan ki ki dawo anjima sedai fa ko da wasa wani raini ya kuma shiga tsakanin Æ´arki dani ko ke kanki to tabbas zan sa a yanka Miki red ticket, Kim San dai mijin naki a tafin hannu na yake, byee bye uwar me bed".

Katse wayar tayi ta maida kallon ta fuskar sa dan ta lura da tsayuwar sa tuntuni, sosai ta zuba idanun ta kan kyakkyawar fuskar sa wanda tun zuwan ta se yanzu ta iya karfin halin hakan, ƙarewa fuskar kallo tayi sosai ba tare da ta yadda idanun sa ya shiga nata ba kafin ta kawar tana me yaba kyan shi cikin ranta,

"The pin".

ÆŠan juyowa tayi dan sam ta manta na bata faÉ—a masa pin É—in ba

"1469".

Juyawa yayi ya koma wajen accountant ɗin ita kuma ta cigaba da tsayuwar jiran su tana kiran Leekha dan jin ya jikin Surry kafin ta ƙarasa.

************

"Barka da dare Mamin ya Saraki".
Cikin murmushin ta me kyau na dattijan ƙwarai ta amsa wa ɗan nata gaisuwar da yayi mata

"Barka kadai ƙanin Saraki". Dariya ce ta ƙwacewa Jamal na jin daɗin yadda yau mahaifiyar tasu ta sake har take iya barkwanci

"Fatan Abbin Maimartaba na cikin ƙoshin lafiya".

"Lafiya lau Mamin mu". Ya amsa mata cikin farin cikin jin ta kirashi da Abbin Maimartaba dan yaci sunan baban takawa ne.

"Nazo yi miki albishir É—in amincewar takawa na tafiya ta dan haka insha Allah nan da kwanaki biyu nake sa ran tafiya".

"Naji daÉ—in hakan yaro na sedai ina jin damuwa kan tafiyar nan taka, nayi istikhara na tsawon kwana huÉ—u kuma alhamdulillah naji kwanciyar hankali sosai dan da alama Saraki na yana Lafiya dan haka ka bar batun nan dan ina son ganin giccin ka a tare da ni Jamal".

"Amma Mami na riga na faÉ—awa takawa zan yi tafiyar nan har ya amince min, ba kya tunanin ya kawo wani tunani na daban kan fasawar tawa?

"Sam ba zaka fasa tafiya ba Jamal, kaje ƙasar da kace masa zaka kayi course ɗin wata biyun under your field daga nan ka dawo kayi aure dan Allah, ina son ganin grandchildren ɗina kafin lokaci na yayi".

Da sauri ya ruƙo hannun ta jin tana kawo batun mutuwa da sam baya san ji bawai dan be san dole zata mutun ba se dan yana fatan tayi tsawon rayuwar da zata ga dawowar gudan jinin ta mafi sayuwa a ranta cikin gidan uban sa da aka koreshi, cikin gatan sa kuma tunƙahon sa har ya taka matsayin da maƙiya suka ƙulla masa sharri domin shi.

"Insha Allah zan yi kamar yadda kika ce Mamina, ki taya ni da addu'a Allah ya bani Sa'a kinji alfahari na".

Hannu ta ɗora kan shi tayi masa addu'a kamar yadda ta saba yayinda cikin ranta ke ɗauke da kewar ɗan ta da yafi kowa kusanci da ita itama tafi kowa kusanci dashi, addu'a tayi masa a ranta kamar yadda ta saba duk ta tuno shi duk dama be taɓa barin ranta ba sedai ta danne kawai.

Sallama Jamal yayi mata ya tafi processing duk abinda ke haÉ—a na tafiyar ita kuma ta cigaba da duba litattafan addu'o'in da ya shigo ya same ta tana yi.

Ko da dare ta shirya tsaf dan zuwa turakar takawa kasancewar ita ke da kwana ranar, cikin haɗaɗɗen falon sa da ya kasance bame shiga se shi da matansa da ƴaƴansa ta same shi hannun sa riƙe da jarida yana dubawa, da sallama ta shiga ta zauna kusa dashi kafin ta miƙa gaisuwa.
Chapter 17 · 0% Book details