← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 64

Sashe 32

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu suke sosai dan kowa ya ƙurewa nashi ido cikin son yaga shi yayi winning Wanda se sun Kai wani ɗan ƙaramin mountain dake gefen ruwan daga can nesa sannan zasu juyo, cikin ƙwarewa Kisnah take murɗa steering dan duk cikin su ta fi su iya wa dan lokacin tana Canada babbar gasar tseren jiragen ruwa take yi kuma so uku tana winning, yanzu ma duk ta kere musu tuni se debate ɗin ya koma tsakanin Deeq da Surayya dan da ya wuce ta take dagewa ta zo ta wuce shi haka shima yaƙi bari ta wuce shi, suna cikin haka har Kisnah takai ta juyi ta zo ta gota su tana musu dariya sedai tana wuce su kuma nata jirgin ya mutu, cak jirgin ya tsaya cikin ruwan ya ƙi gana yaƙi baya haka tana tsaye tana faman danne danne dan ya tashi sedai fafur ya ƙi a haka har Surayya tazo ta wuce ta haka ma Deeq suna ta mata dariya da gwalo.

Sosai ta cika tayi fam kamar zatai bombing a lokaci guda, haka tana ji tana gani Surayya tayi winning sannan Deeq ya kawo mata wani jirgin ta bar wannan a cikin ruwan, tana direwa daga cikin jirgin ƙarar ta ta shige cikin lallausan yashin dake bakin sea ɗin , zare kafar tai ta cigaba da tafiya tana cire cardigan ɗin Leekha da ta ara, tun kafin ta ƙarasa take wurgawa Surayya dake mata dariya harara, ajiyewa Leekha rigar tayi a gabanta kana ta koma kujerar ta ta zauna, dariyar da Surayya ta fashe da ita yasa ta ji kamar ta rufe ta da duka har se ta huce haushin da take tura mata.

Zumbur ta miƙe daga kujerar ta hau zubawa Surayya masifa sedai ko kula ta ba tayi ba sema rawa da ta hau tiƙawa tana waƙar winner, I'm the winner.

_winner, I'm the winner_
_winner, go laugh at looser_
_looser, go shout at the winner_

Haka take ta maimata wa ana ta musu dariya hakan ya sake ƙular da Kisnah ta juya fuuu zata wuce, Deeq da yafi kowa sanin yadda ta tsani taga an cinye ta a tseren ya maza ya ruƙo hannun ta, a fusace ta juya kamar wadda zata kai duka ya maza ya rungume ta ƙam a jikin sa wanda yasa ta shiga sauke ajiyar zuciya tana lafewa a jikin nasa daidai lokacin da Saraki ya ƙaraso wajen dan tuni ya tashi yai sallar magrib ya jira yayi ta isha kafin ya fito ya na ɗan zazzagaya wajen wanda ya hango ruwan ta cikin glass ɗin dake fuskantar ruwan dan haka ya fito dan zuwa bakin ruwan kamar yadda yake matuƙar so ya kuma saba a da sedai tun da ya fara tunkaro wajen yake jin kamar Muryar ta tana bala'i da ya ƙaraso sosai kuma ya tsince ta rungume cikin ƙirjin wani saurayi ta saka hannu ta zagaye shi Kamar yadda shima yayi mata.

Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idon sa ya cigaba da tafiyar sa har ya ƙarasa bakin sea ɗin ya zauna kan rairayin wajen yana saka ƙafafun sa cikin ruwan, lumshe idon sa yayi cikin jin daɗi lokacin da sanyin ruwan ya ratsa fatar ƙafar sa, wani memory me matuƙar daɗi na yawo cikin kansa, its a family memory, family moment da suka yi spending shi da Mamin sa da Jamal har ma da Miemie lokacin da suka kai masa ziyara America inda yayi karatun sa har ma ya fara aikin sa kafin mahaifin sa ya matsa masa da batun komawar sa gida ashe ƙaddara ke kiran sa, ƙaddarar da be san da wane suna ze kira ta ba abinda ya sani itace ƙaddara mafi tsauri a rayuwar sa sedai yana fatan Allah ya bashi ikon cinye jarabawar da ya masa.

Ya daɗe zaune a wajen dan har be san lokacin da ya ɓata ba a wajen se da yaji saukar hannu kan kafaɗar sa kafin ya buɗe idanun sa da ya rufe tun da ya zauna a wajen, janye idanun ta tayi daga duban da take wa fuskar ta saboda tasirin nasa idanun da take ji cikin nata da bazata iya daurewa ba.

Hannun ta da ta É—ora kan kafaÉ—ar sa yabi da kallo kafin ya maida kan fuskar ta hakan yasa tayi saurin janye hannun ta kuma fara magana dan kare kanta

"Ina ta maka magana ne baka ji ba shiyasa na am am shine na ɗan taɓa ka".

Janye idanun sa yayi ya maida kan ruwan da ke motsi kaÉ—an kaÉ—an ga kuma fresh air dake busawa a hankali a hankali, gurin so peaceful haka yanayin me saka nishaÉ—i da nutsuwa ne, kamar daga sama ta jiyo shi yana faÉ—in

"Har ya tafi ne?".

ÆŠan kallon sa tayi amma se taga hankalin sa baya kanta, tunani ta tafi na wa yake nufi kafin ta tuno da Deeq

"A'a yaje É—akin sa he's spending 2 weeks here too".

Bece mata komai ba haka itama bata kuma cewa komai ba suka cigaba da zama a wajen har kusan sha ɗaya na dare kafin ya miƙe sannan ita ma ta miƙe, wayar sa da ya ajiye a wajen ya sunkuya ya ɗauka ya juya ze wuce tayi saurin kiran sunan sa

"Yaa Saraki".

Cak ya tsaya a wajen da yayi yaki biyu sedai be juyo ba hakan yasa ta sha gaban sa da sauri tana ƙwalƙwal da ido tare da langaɓar da kai

"Am sorry Ya, Dan Allah kayi haƙuri".

Shiru yayi yana kallon fuskar ta kamar me son gano wani abu a cikin ta kafin ya magantu

"Sorry? For what? Me kika min na haƙuri kuma?".

"Ni dai am sorry please".
Jijiga kansa yayi

"A sani na ana bada haƙuri ne in anyi laifi, nikuma ban san kinyi wani laifi ba". Ya faɗa yana shirin ratse ta ya wuce, da sauri ta maza ta ruƙo hannun sa

"Amma Ya fushi fa kake sani shiyasa na baka haƙuri".

"Fushi akan me, kawai se in kama fushi ba Amin komai ba kamar mahaukaci, Ni bana fushi da ke".

"Allah ya fushi kake yi".

Wannan a É—an kausashe ya fisge hannun sa

"Na faÉ—a miki ni bana fushi dake so Please leave me alone, I wanna sleep".

Ya faÉ—a yana yin gaba da sauri, itama da saurin ta biyo shi tana share hawayen da ya zubo mata

"Am sorry for that night yaa, am sorry for the dress, am sorry for everything please".

Ta faɗa Muryar ta na breaking saboda kukan da ya taho mata, tsaya wa yayi jin abinda take faɗa, sosai yaji daɗi a ransa ganin ta san abinda tai kenan tunda gashi ta faɗa da bakin ta sedai not so easy like this, baze haƙura da sauri ba ko dan gaba dan haka se ya ɗan yi ƙaramin tsaki ya juyo a masifance

"See I have nothing to do with your night partying or whatever and also your dressings, this life's so simple, so easy and you have the right to live your life as you wish, as you want and as you plan, am not your father nor your brother, we have no any blood ties or something, am only driver, a mere driver whom you paid to serve you, and am doing that, you also payed me, so I have nothing to do with your life, please am sleepy, make you go live me rest". 

Ya ƙarashe cikin pidgin Yana wuce wa gaba ya bar ta a wajen sororo tana bin bayan sa da kallo har ya ƙure mata kafin ta sulale ƙasa, ba kuka take ba dan kafin abu yasa ta kuka ana daɗe wa, tasowar ta batare da kowa a tare da ita ba da sunan family yasa ta zama strong, very strong da ba ƙaramin abu ke sa hawaye forming a idon ta ba, hakan yasa yanzu ma bata yi kuka ba se dai tana jin zafi, zafin yadda ya faɗa mata magana, yadda ya tafiyar sa ya barta jama'a na kallon ta duk da tasan kowa a wajen sabgar sa yake ba wanda ya damu da wani amma ta ji haushi ta kuma ji zafi.

A hankali ta tashi tana kakkaɓe yashin jikin ta kafin tayi making up mind ɗin ta, he said she should leave him and she'll, he said she should live her life as she want Kuma zata yi amd she'll show no concern to him or everything related to him, zata nuna masa she had a heart a ƙirjin ta, a very strong heart.

Da wannan tunanin ta koma É—akin su inda ta same su zaune anata raha da dariya.

Zama tayi cikin su itama dan ba zata ɓata ranta saboda shi ba ehe, nan sukai ta kallo ana hira har se to one kafin Deeq ya musu sallama ya tafi nasa ɗakin suma kowa ya shige bedroom ɗin sa.

Kashegari da safe ko da suka shirya motar Deeq suka shige suka fita gaba É—aya, yawo sosai suka sha dan ya zazzagaya da su wurare sosai, they had a lot of fun together, sun yi hotuna sosai haka basu suka dawo ba se after twelve hakan yasa ranar basu haÉ—u ba gaba É—aya.

Washegari basu fita da wuri ba se two da su Hameedah suka matsa mata shiga cinemar dake cikin resort ɗin wai kallon wani American Film, sam ita bata ra'ayin anything Hollywood Amma haka dole suka takura mata shiyasa kawai ta haƙura ta bisu se gashi to her surprise film ɗin ya burge ta over.

Two hours film É—in yayi lasting kafin suka fito duk ta gaji ga yunwa da take ji se dariya suke mata wai Madam food amma ko kallon su bata yi ba ta faÉ—a restaurant É—in gurin ta nemi table ta zauna tare da kiran waiter ta ticking abinda take so kafin ta koma cikin kujerar ta lafe tana jiran a kawo.
Chapter 32 · 0% Book details