← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 64

Sashe 42

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya miƙa hannun sa ya ɗau hankerchief ɗin sa dake kan table ya goge gumin kan goshin sa kafin ya tura kujerar sa baya cikin sauke numfashi.

"A cikin ma'aikatan gurin nan aka haÉ—a baki akayi wannan abun, waye Emeka maji?".

Tsayar da abun da take yi cikin computer É—in tare da maida hankalin ta kan sa

"Yana É—aya daga cikin in charge masu kula da quantityn ingredients É—in da ake zubawa yayin haÉ—a drinks É—in".

Ta faɗa tana ƙure shi da idanu cikin son ƙarin bayani

"Come closer".

Da saurin ta kuwa ta bar seat ɗin ta zuwa table ɗin sa tare da jawo kujera ta zauna next to him, juyo mata screen ɗin system ɗin sa yayi yana mata playing vedio ɗin da yai pausing, shiru tayi ta zuba wa screen ɗin ido tana kallo cikin tsananin mamaki da rashin yarda da abinda take ganin har short video ɗin ya ƙare...........................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 28 (8/20/2022 8:41 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

Ouummey 26 (8/20/2022 8:39 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                           Page 2️⃣6️⃣

_________________________📖 Tare suka zauna a office ɗin suna ayyuka sedai ana kiran sallah ya dakata daga aikin da yake yi na bin record ɗin spendings na watan da ya wuce da ta nemi a kawo nata shine fa yake bin lissafin dan ganin ko daidai yake.

Da kallo ta bishi kafin ta kautar da kanta ta cigaba da shigar da bayanan da take cikin laptop ganin ya shiga toilet, be daɗe ba ya fito fuskar sa jiƙe da ruwa haka hannun rigar sa a nannaɗe yana ƙoƙarin saukar dashi da alama dai alwala yayi.

Ɗagowa tayi ta bishi da kallo jin fitowar sa sedai unfortunately idanuj ta ya sauka kan tsintsiyar hannun sa da yake ƙoƙarin sauke hannun rigar, wow kawai ta iya furtawa cikin ranta ganin yadda wasu kyawawan baƙin gashi suka kwakkwanta suka nannaɗe a jikin fatar hannun nasa, sosai ta kasa janye idanun ta kan hannun dan tana matuƙar son taga mutum na da gashin hannu da ƙafa, da sauri ta bi ƙafafun sa da kallo taga nan ma yana dashi ko kuwa sedai taga wandon sa a sake yake hakan yasa ta kuma maida kanta kan hannun nasa da ya gama sakin ɗaya ya koma ɗayan

Jikin shi ne ya bashi ana kallon sa dan haka ya ɗago dan yasan ita ce tun da su biyu ne a office ɗin, kanta kuwa ya sauke duban sa yaga yanda ta kafe hannun sa da kallo har bata ƙi ƙiftawa, sake bin trace ɗin in da take kallon yayi ya tabbatar hannun sa take kallon se ya bar ƙoƙarin sauke sleeve ɗin da yake ya ɓoye hannun a bayan sa hakan yasa ta farga ta maza ta gyara zama tana maida kanta kan system ɗin cike da kunyar da bata taɓa tunanin tana da ita ba.

Ficewa yayi ya tsaya bakin office É—in ya gama gyara hannun rigar kafin ya wuce masallaci, ko da aka idar se da ya tsaya yayi addu'o'in sa kamar yadda ya saba kafin ya dawo har lokacin kuma tana kan aiki cikin system ga tarin tulin takardu gaban ta

"Miss lokacin sallah yayi, You leave the work kije kiyi se ki dawo ki cigaba".

Cak ta tsaya da aikin da take tana bin shi da kallo cikin tuno ita yaushe rabon ta da yin Sallah da rana irin haka, ita fa sallar ta se dare yayi take haÉ—e su duka tayi a lokaci É—aya tayi ta huta dan ita bata san wannan gutsire gutsiren da ake yi, a yi É—aya yanzu ayi wata anjima shiyasa take haÉ—e nata.

"Zan yi duka in na koma gida, hankali na baze kwanta ba se na gama shigar da informations É—in nan".

ÆŠan zato ido yayi yana kallon ta

"Excuse me, bangane se kinje gida ba, sallar ce se kinje gida ko aikin?".

"Haba sallar dai, aikin nan ai bazan bar office ba yau se na ƙara sa shi bari ma in ƙara maida hankali ka gani".

Mamaki ne ya kusan kar shi daga zaunen da yake, sallar take batun se taje gida Sannan zata haÉ—a, La hula wala quwwat, wannan wace irin rayuwa ce, anya yarinyar nan na da ilimin addini ko yaya a tare da ita kuwa? Baya tunanin hakan ko da dai hakan be kamata ya zama abin mamaki ba in yayi duba da É—abi'un ta da kuma ayyukan ta zuwa kan shigar ta, in yayi rantsuwa baze yi kaffara ba yarinyar nan bata ma san me ye addinin ba kwata kwata, ita dai kawai tana amsa sunan musulma ne amma kuwa iyayen ta sun cuce ta cuta mara adadi.

HaÉ—e ran sa yayi sosai dan ma kar ta samu wani fuskar yi masa musu ko wata magana

"Ki tashi kije ki yi sallah nace kar ki bari ranki ya ɓaci".

Sakin aikin tayi ta tsaya kallon shi cikin son yin magana sedai yadda ya haɗe gabas da yamma kamar wanda ke jiran ƙiris ya rufe ta da duka yasa ta miƙe tana ture system ɗin da ƙarfi har tana kusan faɗuwa, toilet ta nufa tana maganganu ƙasa ƙasa wanda bai jin me take faɗa ta shige.

Alwala tayi sedai gyaran dake cikin alwalar ba kaɗan bane, fitowa tayi tana goge fuska da towel ƙarami tare da nufar wani ɗaki me kyau me matsakaicin girma da akayi shi dan hutawa in an gaji da aiki ta shige, da ƙyar ta sami ƙaramin veil ta naɗa shi a kanta tayi Sallar.

Baki buÉ—e Saraki ya bita da kallo ganin ko minti biyu cikakku ba tayi da shiga É—akin ba amma har ta fito kuma wai tana nufin tayi Sallah

"Kam bala'i". Ya furta batare da ma yasan yayi ba, lallai this girl is unbelievable, tabɗi, lallai Yana da aiki a gaban shi amma for now Bari ya ƙyale ta kar tursasawar tayi yawa har ta fara jin haushin sa tun da suna tare da sannu ze gyara ta ne da izinin Ubangiji.

ÆŠauke kan sa yayi daga kanta ya cigaba da aikin sa itama haka har se can wani lokaci kafin ta ture system É—in tana tura baki

"Yunwa nake ji sosai yaa".

Ko kallon ta be yi ba ya cigaba da aikin sa, to ban da ma rainin hankali d ta faÉ—a masa me take nufin yayi mata, ko tana nufin ya fita ya siyo mata abinci ne, ashe ko zata wuni da yunwar.

Ganin yadda yayi banza da ita yasa itama ta share shi ta janyo wayar ta, order ta bayar sannan ta jingina da kujerar da take kai tana rufe idanun ta, ba ƙaramin gajiya tayi ba wallahi, ga gajiyar tafiyar jiya bata gama sakin ta ba ga ta aiki da ta kuma rafke ta se take jin kamar ba ita ba dan rabon ta da aikin wahala irin haka tun tana level two kafin daga baya taji gaba ɗaya zaman Companies ɗin ya ishe ta ba ta so ta maida ragamar kula da komai hannun kawu.

Knocking ɗin da ake a ƙofar yasa ta miƙe ta ƙara sa tareda buɗe ƙofar dan shi kam ko motsawa be yi ba balle ta sa ran yaje ya buɗe, deliveryn restaurant ɗin da tayi order ne yayi handing mata packs ɗin ya juya dan tayi musu payment online.

Gaban sa ta ajiye Masa pack ɗaya ta wuce da ɗaya wajen ta ta ajiye, fridge ta buɗe ta ciro goran ruwa biyu da lemo ta ajiye masa nasa ta ajiye nata gaban ta, ba tare da damuwar komai ba na wai yana zaune ta buɗe pack ɗin ta ta soma cin fried sphagetti with veggies da pepper soup ɗin ta hankali kwance tana yi tana sipping drink ɗin ta har ta ƙoshi kafin ta tattare komai ta ajiye a gefe ta ɗau ruwan ta sha to her satisfaction.

Duk abinda take yi yana sane sedai be maida hankali kan ta ba dan yasan dana ta saba cin abinci in public so cin abinci gaban sa baze gagare ta ba.

Messenger É—in ta ta kira ta bashi ragowar da ta rage tace a bawa me so ta cigaba da aikin ta, wasa wasa basu bar office É—in ba se after six, gudu sosai Saraki yayi ranar dan baya son missing magrib prayer da ake ta kira a masallatai, ko da yayi parking be fita ba se da ya sake jaddada wa Kisnah tayi sallah da ta shiga gida fiye da so uku sannan ya wuce a hanzar ce zuwa masallaci.

Ko da ta shiga wanka ta fara yi tare da canja kayan jikin ta da suka takure ta,  gajeran wando ta saka da ya wuce cinyoyin ta se ƙaramar riga me kamar shimi tana yi tana tunanin yanda zata dena saka irin wannan kayan ta koma saka wasu, tuno da yace tayi Sallah yasa ta miƙe tana ɓaɓɓata fuska kamar yana gaban ta ya zurma hijabin tayi ƴar fakin ta kamar yadda ta saba.

Kan bed ta faɗa dan kam yau bacci zata yi da wuri dan ta huce gajiya ta kuma tashi da wuri gobe, da kayan jikin ta ta kwanta bayan tayi offing light tare da locking ƙofar ta, within minutes tayi bacci abin ta.
Chapter 42 · 0% Book details