← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 64

Sashe 58

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko gama tsayuwa daidai bata yi ba ya ƙara so gaban ta yana huci kamar wanda ya haɗiyi garwashi idanun sa sun sauya launi saboda ɓacin rai, ƙanƙame jikin ta tayi jikin bangon ɗakin kamar zata koma Cikin sa saboda fargaba da tsoron Sarakin, kallon ta yake yana tuno yadda ta zagaye gari kanta buɗe ga shashancin da take yi da mazan garin, ɓacin ran da ya sake tuƙo shi yasa ya dunƙule hannun sa ya kaiwa garun da take tsaye jikin sa nauyi, runtse idanun ta Kisnah tayi jikin ta na ɗaukar rawa dan ta zata ita ze nausa sedai da suari ta buɗe idon jin ƙarar zubar ƙasa a bayan ta, zaro ido tayi waje ganin yadda gurin yayi rami yar ya fasa waje, da sauri ta juyo ta dubi hannun sa da duk ya kukkuje yana fitar da jini.

ÆŠagowa tayi da niyyar yi masa magana sedai ya riga ta buÉ—e baki

"How dere you, eyeh nace how dere you in Baki umarni ki ƙi bi, ban ce kar ki fita ba shine tsabar raini ki ka saka ƙafa kika fice and to make it worse ba ma ɗan kwali dan ki nuna min ban isa ba bazan faɗa miki kiji ba, kina tafe kina shashanci da mazan gari ko?".

Kai ta shiga girgiza masa da suari alaman ba haka bane kafin da ƙyar tayi summoning courage ɗin yin magana

"Allah ba haka bane yaa, banga zanin da nake sawa a kaina ba shiyasa kuma..........".

"Will you shot your stupid mouth ko sena kwaÉ—a miki mari a gurin?".

Tsawar da ya daka mata ya katse abinda take son faɗa ta maza ta saka hannun ta ta ƙara taushe bakin ta, mugun kallo ya cigaba da yi mata kafin kuma ya saki ƙwafa ya matsa inda buhun kayan marmarin da ta shigo dashi ya faɗi ya ɗauka ya fice.

Ajiyar zuciya ta saki tare da zame wa ta zauna a gurin tana dafe ƙirjin ta da hannu, dama haka yake? Abinda ta shiga tambayar kanta kenan kafin kuma ta jijjiga kai, amma fa ya bata tsoro, tayi zaton dukan ta ze yi irin yadda taga jikin sa na rawa saboda ɓacin rai.

Bata san ze ɗau zafi har haka ba da bata fita ba ɗan kwali ba, ganin ba yau ta saba fita hakan ba kuma a gaban sa tun suna manya yasa bata ɗauki fitar ta ba scarf a komai ba bayan haka ma suma matan garin basa sa komai a kan su suke ficewa, to me ze sa yaji haushin ta ita, ta ƙarshe tananin ta tana tura baki.

A can waje kuwa Nenne Saraki ya bawa kayan marmarin yace nasu ne kar a taba dasu suna dashi a ɗaki ta kuwa karɓa tana godiya, can wajen zagaye bukkar su ya fita ya zauna dan in ya koma ɗakin su a yadda yake ji ze iya sa mata hannu and baya fatan hakan ya fara faruwa tsakanin su tun yanzu, a rayuwar sa ya ƙi jinin namiji me dukan mace dan a ganin sa rashin tunani ne da hauka so ba ze so ya zama one ba .

Haka ya zauna wajen yana kallon yadda kowa yake al'amuran sa batare da sa ido ko wani ya damu da wani ba har duhu ya kawo jiki amma ko tunawa da yunwar cikin sa be yi ba dan tuni ɓacin rai yasa ya manta da ita.

Seda yayi sallar magrib nan waje cikin wani ɗan fili da suka yi wa gini kamu bakwai da bulon su na ƙasa da sunan masallaci kafin ya shiga gidan, kan tabarmar kabar da ya tadda arɗo ya zauna suka shiga tattauna batun seeds ɗin da ze noma a filin da aka bashi, sunyi nisa a batun gonar kafin ya shigo da batun tafiyar su nan da kwana biyar, shiru arɗo yayi yana bin shi da kallo yayinda shi kuma ya sunkuyar da kan sa ƙasa har arɗon yayi magana

"Anyi muku wani abu na rashin kyautawa ne Ahmad da kake batun tafiya?".

Da sauri ya É—ago yana sakin murmushi wa arÉ—o ganin yadda duk tsohon ya damu

"Ko kaɗan arɗo, sedai kamar yadda na sanar da kai kuma ka gani haɗari ne ya kawo mu zama da ku, kuma alhamdulillah ku ɗin mutane ne na gari dan kun karɓe mu batare da sanin ko su waye mu ba haka batare da neman komai daga gare mu ba, kayi haƙuri arɗo sedai zamu tafi ne dan iyayen mu suna can cikin tashin hankalin rashin sanin ina muke da kuma wane yanayi muke amma ba wai dan kun gaza damu ba, a zamanin nan bana tunanin za'a samu mutane masu matuƙar karamci irin ku arɗo".

Murmushin jin daÉ—in yabon da aka yi musu arÉ—o ya saki yana gyaÉ—a kan sa at the same time cikin yarda da batun Ahmad É—in,

"Hakane Ahmad, daÉ—in zama yasa na manta da ya kamata iyayen ku su san halin da kuke haka su san kuna raye, ban ji daÉ—in jin zaku tafi Ku bar mu ba amma hakan ya zama dole, kar ka damu Allah ya kaimu ranar".

Da Amin saraki ya amsa masa suka cigaba da hirar su har Nenne ta kawo musu abinci da ya kasance kwaÉ—on rama ne, tare suka saka hannu suka ci suka sha ruwa sannan suka É—ora firar, basu tashi a wajen ba seda arÉ—o yayi wa Saraki sallama kan yaje ya kwanta sannan ya tashi ya shiga bukkar su ba dan yaso ba.

Duk hirar da suka yi Kisnah na jin su dan takarar dake tsakanin bukkar su da ta su arɗo ba me nisa ba ce dan ana iya jin komai dake wakana a waje , ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin batun zasu bar garin in five days time, Allah ya sani tana rayuwa ne kawai cikin nuna all is well alhalin ba haka bane daurewa kawai take amma she is not used to all in the environment, kiwo da zuwa rafi ne kawai abinda tasan tana yi da zuciya ɗaya yake kuma sata nishaɗi da farin ciki se kuma da green view of the palace shima is something lovable to her.

Jin ze shigo ɗakin yasa ta takure jikin ta waje ɗaya tare da kwanciya kan buhun da take zaune, baccin ƙarya ta nuna tayi har lokacin da na gasken ya ɗauke ta gaba ɗaya a yadda take, ko kallon inda take be yi ba ya wuce wajen kwanciyar sa ya gyara shimfiɗar sa duk da a gyare take ya zauna tare da karanto addu'ar baccin sa ya shafa yakai kwance abinsa.

Ya daɗe kafin bacci ya iya ɗaukar sa saboda kayan jikin sa, kullum haka yake fama dan shi be iya bacci da kaya a jikin sa ba most especially riga sedai a nan dolen sa ya kwanta da ita tunda an haɗa shi kwana guri ɗaya da wannan yarinyar, bayan haka kuma rigunan su masu nauyi ne saboda na saƙi ne.

Asubar fari yayi Sallah tare da sammakon tafiya gona, cikin kwanakin da suka biyo baya gaba É—aya ya maida hankalin sa kan gonar dan so yake yayi ya gama dasa irin su tarkata su bar garin dan ya ishe shi, har kwana uku basa wani good times da ita dan fushi yake sosai, iya gaisuwa ke shiga tsakanin su kawai, in ta gaishe shi ya amsa mata da lafiya shikenan.

Ganin yadda ya ɗau fushi yasa ta kama kanta ta tsaya iya matsayin ta bata wani shisshige masa kamar da, in ya dawo yana ɗakin zata fita waje gurin su Nenne tayi zaman ta se dai in an kawo musu abinci sannan ta kai ɗakin su ci dan a kwano guda Nenne ke haɗa musu abinci, haka zasu zauna cin abincin shiru bame cewa komai, in sun gama ta ɗauka ta fita da ƙwarya to akushin ta cigaba da zamanta cikin su se lokacin da Nenne ta kore ta tukun take musu sallama ta shiga taya shirin bacci ta kwanta.

Ciki kwanaki huÉ—u kamar yadda yayi fata ya gama shuka seeds É—in gaba É—aya wanda ba abinda arÉ—o yayi a ciki se gyara masa in da ya kuskure har aka gama.

Ranar kam basu dawo da wuri ba duk da da wurin ya gama amma se arɗo ya ɗauke shi suka dinga zagaya gonakin da da kuma na maƙwaftan sa yana ganin yadda shukokin suka yi kyau sosai, nan suka ɓata lokaci har bayan isha kafin suka dawo, ko da suka shigo gidan ruwa kawai ya watsa tare da canja ya fita wajen arɗo dake zaune kan tabarmar sa dake gefen su Nenne, Bingel da Kisnah.

Tare suka cigaba da hirar gaba É—aya cikin farin ciki da kuma kewar su Kisnah da zasu bar garin gobe, kayan marmarin da su arÉ—on suka shigo dashi Nenne ta gyara ta ajiye wa Saraki da arÉ—o tare a gaban su su ma su uku nasu a haÉ—e.

Basu tashi daga zaman ba se kusan karfe goman dare sannan akayi sallama kowa ya nufi ɗakin sa, gyara masa shimfiɗar sa tayi lokacin yaje banɗaki sannan ta koma ta gyara tata da tsurar buhu ne se zanin saƙin da yayi laushi saboda shan ruwa da take haɗawa ta kwanta a kai.

Ko kafin ya shigo tuni tayi baccin ta dan ita kam bata da nauyin yin Bacci, wuyar ta ta kwanta tuni zata yi baccin ta abin ta, haka damuwa bata hana ta bacci shiyasa yanayin rayuwar ta ya zo mata da sauƙi dan irin cases ɗin da suka wanzu a rayuwar ta ba kowa ce zata iya ɗauka ba, sedai ba fa wai bata damuwa bane a'a abin dai na zuwa mata da sauƙin ne dan rashin bacci ma babbar damuwa ce dake assasa cututtuka da dama.
Chapter 58 · 0% Book details