← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 64

Sashe 30

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tayi dan bata san amsar da zata bashi ba sedai ita sam bata ga aibun shigar tata ba, ita bata wani É—au saka irin wannan kayan a komai ba dan ta É—au hakan a matsayin tsarin rayuwar ta haka kuma kamar yadda Bature ya faÉ—a kowa yana da right yayi living life É—in shi as he wish dan haka ita ba me sa ido bace akan rayuwar wasu so bata san itama a fiye sa mata idon.

"Amma Ya Saraki yau birthday ɗin Surayya ne, tayi missing exact date ɗin saboda rashin lafiyan da tayi yanzu kuma ta samu sauƙi shiyasa ka shirya wannan partyn da murna biyu, jin daɗin warkewar ta da kuma birthday ɗin kaga kuwa dole ne muyi shiga me kyau dan taya ta murna ko?".

"Shine se kun bayyana tsiraici za'a san kuna farin ciki, inda zaki kyautawa kanki da kin koma kin canja wannan rigar to something more decent and better".

Ɗauke kanta kawai tayi ganin bafa ze fahimta ba ita kuma bata shirya bin wani tsarin sa ba na daban wanda ya zaɓawa kansa dan haka kawai itama ya barta da nata.

Ganin yadda ta É—auke kai yasan nufin ta bazata canja É—in ba so se be sake cewa komai ba kawai ya tashi motar ya fita daga gidan sedai a lokacin fuskar sa kamar wani mala'ikan É—aukan rai tsabar yadda ya haÉ—e ta, har suka je be sake kallon gefen da take ba haka itama dan taga in tayi sanyi neman sa ta dole yake yi.

Sosai partyn yayi musu daɗi ya kuma ƙayatar dasu, su Madam Kisnah ansha rawa kamar za'a cire ƙugun a yar, liƙi ne tayi kamar ba gobe haka itama an mata kamar a buɗe wani banki da kuɗin, basu tashi ba se after one Dan saura kaɗan two tayi.

Ko da ta fita da ƙyar ta gano inda ya ajiye motar ta ƙarasa, yanzu ma kamar ɗazu ba wanda yace wa ɗan uwan sa uffan har suka kai gida duk da dai ita Kisnah cike take tam da labarin da take son bashi na yadda event ɗin ya tafi sedai ganin ba fuska yasa dole ta haɗiye kayanta.

Tun daga lokacin kuma ya shiga fushi da ita, ze kaita duk inda take so batare da query ba haka kuma kome zata yi ya daina cewa komai, sosai take cikin rashin daɗin fushin nasa sedai ta rasa ta yadda zata fara bashi haƙuri dan expression ɗin sa is not helping at all, so biyu tana gwada shiga motar Ba tare da sallama ba amma ko kallon ta be yi ba balle ya harare ta yadda yake yi a baya har se ta fita tayi.

Yanzu ma jaye da babban trolley ta fito alamun dai zata yi balaguro, tasowa yayi ya buɗe booth ɗin tare da ɗaukar trolley ɗin ya saka a ciki kana ya rufe, be kalle ta ba ya ƙarasa ya buɗe side ɗin driver ya shiga tare da maida murfin ta rufe, kamar mata laka haka ta ƙarasa nata side ɗin ganin yadda yayi tafiyar da ya bar ta ko arziƙin kallo ɗaya bata samu ba daga gare shi.....................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fisabilillah.

Ouummey 20 (8/11/2022 10:39 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                           Page 2️⃣0️⃣

______________________📖 Manyan hamshaƙan mata ne ƴan gayu cikin shigar da kana kallon su kasan sun kai sun isa sun kuma tumbatsa dan gwala-gwalai ne kawai ke ta walwali a jikin su, zaune suke a falon gimbiya Rumana gaban su cike da kayan ciye ciyen da kama gani kasan mutane ne na musamman gare ta haka masu matuƙar daraja.

A hankali wata farar mata a cikin su ta É—ago ta kalli gimbiya Rumana dake zaune cikin su ana hira tana kai kyakkyawan slice of apple bakin ta

"Amma Rumana bakya tunanin mijin nan baki yace ce bawa yaron can Jamal sarautar nan, ni kam se naga kamar hankalin sa ya fi karkata ga yaran É—akin kishiyar ki ko da yake ba laifin sa bane a fili yake sun fi uthman nutsuwa nesa ba kusa ba".

"Haba Aunty Siyama, wannan wace irin magana ce haka, wace nutsuwa ce aka fi uthman ɗin da zan iya rantse miki baya wani shashanci, masu nutsuwar kuma ai a hakan dai a ka kori ɗaya daga cikin su kan aikata babban alfasha ko". Sarauniya Rumana ta faɗa da little ɓacin rai a harshen ta

"Alfashaar da kuka laƙaba masa ke da husna? Ko an faɗa miki ban san komai akan hakan bane, kawai na zuba muku ido ne dan nasan ba laifi kika yi ba wajen fighting Nasara wa ɗan ki, mu ajiye wannan maganar mu dawo kan wadda muke yi yanzu".

"Bana tunanin ya isa yayi hakan dai uthman shine gaba da yaron, dama wancan da aka kora ne gaba dasu gaba É—aya shiyasa ban kwantar da hankali na ba se da na tabbatar da fitar da cikin masarauta ta sigar da shi da ita har abada dan ko cikin ta be isa shigowa ba haka Sarauta sedai yaga anayi".

"Hakan yayi kyau, sedai kin san dole uthman yayi aure ko da ba'a taɓa sarki mara mata ba".

"Takawa ma yayi magana akan hakan kuma insha Allah ina kan tunanin mafita dan yace baze bada sarauta yanzu ba har se sunyi aure yaga irin kamun ludayin kowannen su ta fuskar riƙe iyali tukuna".

"Kina da hankali kuwa Rumana, naji kina maganar su, bayan kamata yayi yace uthman kawai anya ba wata a ƙasa kuwa?".

"No ba komai Aunty Siyama, kinsan shikansa Jamal din ya girma yanzu dan he's 28 shiyasa yayi pluhralizing Amma ba wani abu ba".

"Na gane"

Juya wa sarauniya Rumana tayi ga É—aya Æ´ar uwar ta su da tun da suka fara maganar bata ce ko uffan ba se danne danne da take yi a faskekiyar wayar hannun ta

"Wato har yanzu dai kina nan da halin miskilancin naki Khadijah, kina ji muna ta hira amma ko kallon mu ma ba kiyi ba, lallau Abu Sufyan yana ƙoƙarin zama dake".

Murmushi Khadijar tayi

"Hirar taku ce ba irin wadda zance komai a kai bace Aunty, abinda kuke magana akai kun san ba daidai bane haka abinda kuka aikata ke da husna, sedai ba zan iya tona muku asiri ba kasancewar ku Æ´an uwa ne, amma fa bazan fasa faÉ—a muku ba a kullum ku ji tsoron Allah".

"To ustaxiya, mun ji kuma mun gode".

ÆŠan murmushi kawai tayi ta cigaba da latse latse a wayar ta yayin da suma suka cigaba da tasu hirar.

**************

Gudu sosai motar take yi kasancewar titin ba wasu motoci da yawa se tsirarun na matafiya, shiru cikin motar ba alamun akwai me rai dan baka jin ƙarar komai se sautin nunfashin su dake fita a hankali a hankali se ko sautin karatun Alqur'ani mai girma da aka kai volume ɗin kusan can ƙarshen ƙasa.

Chatting take yi tana zaune a kujerar ta sa'i da lokaci bakin ta na sakin murmushi alamun tana enjoying chatting da koma waye take yi ɗin, ringing ɗin wayar ya saka fuskar ta ƙawatuwa da faffaɗan murmushi ganin sunan Deeq kan screen ɗin, picking tayi tare da kangawa wajen kunnen ta

"Deeeeeeeq". Ta faɗa a hankali dariya na ɗan kubce mata, daga can ɓangaren akace

"Kar ki wani kira suna na bayan kin shoshala min rashin m, Allah queen baki da kirki".

"Am sorry my Deeq, Allah na manta ne a lokacin hankali na yayi makaranta kasan dama na faɗa maka daga can muke, nasan ka fi kowa sanin halina ta wannan ɓangaren".

Ta faÉ—a da ragowar sautin dariya cikin muryar ta

"Sosai ma kuwa na san ki ciki da waje, from cover to cover so sedai in ba wa wasu labari".

"Yauwa my Deeq na San ka yi min uzuri ko?".

"Sosai ma kuwa Queen, kin taho ne?".

ÆŠan duban titi tayi kafin ta gyaÉ—a kan ta

"Muna hanya tuntuni, I think be fi ragowar three hundred kilometers ba mu ƙaraso, su Surayya sun ƙaraso ne?".

"Eh na bar su sun shige É—aki zasuyi freshen up".

"Then Sena ƙaraso ko?".

"Ok bye, I love you".

"I love you too babe". Ta faɗa tana katse kiran, a hankali ta gyara zaman ta tare da miƙa hannun ta baya ta ɗauko ƙaton headphone ɗin ta dake cikin medium handbag din ta tayi connecting da wayar ta tare da maƙala shi cikin kunnen ta ta ƙure ƙarar sa cikin waƙar koi mil Gaya ta cikin Film ɗin koi mil Gaya ɗin na jarumi Hrithik Roshan da jarumai pretty zinta sannna ta kwanta sosai cikin kujerar ta lumshe idanun ta tana bin waƙar a hankali.

Ɗan kallon ta yayi a kaikaice cikin takaicin yadda ta ƙwama uwar earpiece tana sauren waƙoƙin banza na wai arna can da ba lallai ta san me suke faɗa.

A haka ya cigaba da gudu kan shimfiɗaɗɗen titin da yasha sabuwar coal tar har suka kusa fara shiga birnin sawariya da duk wannan gudun yana amfani da Google map ne dan shi ne taɓa sanin akwai garin ma a ƙasar ba, ko da yake shi banda garin su Giwa da maƙwabtan su ba inda ya sani dan kusan ba anan yayi rabin rayuwar sa ba.

Tun daga nesa ya hango ƙarin ginin resort ɗin da kusan duk da gilasar aka yi shi, gini ne me girman gaske haka me matuƙar tsawo dan a ƙalla ze yi hawa hamsin, kyawawan furanni masu fitar da sassanyan ƙamshi zagaye dashi haka kuma dogayen bishiyun kwalliya suma sun kewaye shi hakan yasa hatta iskar wajen kusan ta musamman ce.
Chapter 30 · 0% Book details