← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 64

Sashe 8

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ta maida hankalin ta kan malamin da ke ta bayani tana jotting wasu tana understanding wasu, wata irin ƙwaƙwalwa Allah ya bata me saurin fahimta da ɗaukar abu, wuyar ta ta saka kanta tofa duk wahalar karatu a wajen Kisnah se ya koma bakomai ba shi yasa dole su Surayya ke haƙurin zama da ita dan suna amfana sosai ta ɓangaren karatu haka kuma ba dan ita ba da yawanci karatun ma ba yi zasuyi ba dan baya gaban su.

Ko da malamin ya fita tattare littattafan tayi waje É—aya Meenah dake gefen ta ta É—auka haÉ—e da nata, fita sukayi a hall É—in dan basu da wata lecture É—in se after 2 hours, library ta wuce suka bi bayan ta, haushi sosai ya kama Surry da Hameedah dan su in akwai abinda suka tsana be wuce wannan shiga Library É—in ba se dai kuma ba yadda zasu yi dan indai zata shiga dolen su su bita.

Haushin Kisnah Hameedah ke ji ganin yadda ta zama boss É—in su, komai se abinda tace zasu yi, in partying É—in ne, in clubbing É—in ne, karatun ne ko zaman gida du se abinda tace.

Haka ba yadda suka iya suka shiga, circulation suka samu suka zauna kowacce ta ciro book É—in da zata karanta suka mai da hankali kai.

_____________

                   *MASARAUTA*

A can masarautar DAULATUL NOOR kuwa al'amura na tafiya yadda ya kamata a ɓangaren sha'anin sarauta, sedai a ɓangaren Haleematus~Sadiya kawai dai tana rayuwa ne blankly, Sam babu ɗigon farin ciki a rayuwar ta se ɗumbin baƙin ciki da damuwa da take ɓoyewa a ranta saboda wasu rayuka da ba zata so dakushe rayuwar su ba.

Kamar yau da take zaune cikin hamshaƙin falon ta da yaji kayan alatun sarauta, duk inda ake neman haɗuwa da tsari na ƙyale ƙyalen gidan sarauta to fa tabbas akwai shi a wannan falo.

Kishingiɗe take akan kilisar ta idanun ta lumshe tayi nisan kiwo cikin duniyar tunani da ta zame mata abokiyar rayuwa tun bayan barin hasken ranta kuma gudan jinin ta YARIMA SARAKI ƙasar, a kullum ba ta da wani aiki se wannan tunanin dan ma tana ƙoƙarin ganin ta danne wani abin a ranta ko dan ragowar ƴaƴan ta su samu farin ciki sedai wani abun yana gagara dannuwa har ya fito ya bayyana kansa a zahiri.

Duk kirarin da ake yi na isowar Yarima Jamal bata ji ba ba kuma ta san anayi ba har se da jakadiyar ta ta É—an bubbuga gefen kilisar ta kafin ta yi firgigit ta dawo duniyar mu.

"Allah ya ƙara wa gimbiyar Giwa lafiya, yarima Jamal ke neman iso".

GyaÉ—a kanta kawai tayi batare da ta iya magana ba dan a lokacin da zata sami dama to tabbas kuka zata yi.
Cikin takun ƙasaita haɗi da izzar da ta zagaye jinin jikin sa yake takowa cikin falon yayinda bayi da kuyangi ke ta zubewa suna gaida shi, da fara'a yake amsa musu dan Yarima Jamal mutum ne me fara'a da barkwanci haka ko ga talakawan ƙasan sa be kasance me girman kai da ɗagawa be se ko ɗan abinda ba'a rasa ba na jinin sarauta dake yawo jikin sa.

Gaban mahaifiyar sa ya zauna yana tanƙwashe ƙafafun sa kana ya sunkuyar da kansa

"Barka da rana Mamin saraki, gimbiyar Giwa kuma sarauniyar mai martaba, fatan na same ki lafiya".

Murmushi ne ya wanzu kan fuskar sarauniya Haleematu, duk da soyayyar saraki a ranta daban ce amma tana matuƙar so da ƙaunar ragowar ƴaƴan ta suma.
Hannu takai kanshi dake sunkuye ta shafa sumar kansa da ta kasance baƙa ƙirin kuma me tsayi da kuma taushi kamar me kasancewar su jinin larabawa da kuma Fulani.

Hannu yakai ya riƙo na mahaifiyar sa kana ya ɗago yana sakin kyakkyawan murmushi, fatabarakallahu Ahsanul khaleeqeen, tabbas yarima Jamal kyakkyawa ne da ze amsa sunan kyakkyawa a ko ina, haka fara'ar fuskar sa na daɗa ƙara masa kyau da haiba.

"Ina fatan gimbiyar Giwa ta kasance cikin walwala da farin ciki, ya zamo bata da wata damuwa".

"Ina cikin farin cikin sanin ina daku a tare dani yarima sedai zuciya ta baza ta iya daina tunani da damuwa da halin da saraki na ya ke ciki ba".

"Shin ban alƙawaran tawa sarauniya sama mata farin ciki a duk inda yake ba?".

"Bana fatan yarima na yayi abinda mahaifin sa ze yi fushi da shi, kai kaÉ—ai gare ni yanzu dan haka ba zan so rasaka a kusa dani ba in ba Haka ba zuciya ta zata buga ne dan bazan iya jurewa ba".

"Karki damu Mamin Saraki, maimartaba baze taɓa sanin na fita neman Yaya ba sedai in ke zaki faɗa masa, a yanzu haka na shigar da uzurin son barin ƙasar nan zuwa ƙasar Sarbila dan yin wani course a ɓangaren karatu na na tsawon shekara biyu, ki taya ni da addu'a Allah ya sa maimartaba ya yarda domin amincewar sa ita ce komai".

"Addu'a ta na tare daku a koda yaushe, kai da Saraki na har ma da ƙanwar ku da ke gidan aure, Allah ya tsare min ku a duk inda zaku sami kanku ya baku Sa'a da Nasara a rayuwar ku, Allah ya haskaka min rayuwar ku ya kare ku daga sharrin duk wani abin ƙi tare da ku da al'ummar Musulmi baki ɗaya".

Da Ameen yake ta amsa addu'ar mahaifiyar sa zuciyar sa cike da tsantsan tausayin ta, batun yau ba ya daɗe da sanin irin so da ƙaunar da mahaifiyar tasu ke yi musu sedai Saraki daban ne a ranta, ko da yasan hakan be damu ba domin ta na nuna musu so ne equally haka kuma dole taso Sarakin tunda shine ɗa na fari da ta fara haifa haka kuma ɗan da ke tsananin so da ƙaunar ta tare da yi mata biyayya matuƙa.

Sallama yayi mata ya fita daga kilisar ta ya wuce zuwa ɓangaren sa, alkyabbar jikin sa ya zare kana ya rage kayan jikin sa ya kwanta kan gadon sa ya shiga wassafa yadda ze fara neman ɗan uwan sa, ba wai ze dawo dashi gidan sarautar bane, a'a su san inda yake kawai suke so da kuma lafiyar shi ko hankalin su da na mahaifiyar su ya kwanta.

Ƙarar wayar sa ce ta katse masa lissafe lissafen sa, janyo wayar yayi yai picking, lumshe ido yayi lokacin da sassanyar Muryar ta ya daki kunnen sa.

"Barka kadai lovely, hope kina lafiya".

"Lafiya na ƙalau Alhamdulillah dear, ya su Mamin yaya Saraki".

"Tana lafiya lau Alhamdulillah, ya nan wajen su Mama".

"Itama suna lafiya, yau ban ji kiranka ba shine na kira inji ko lafiya".

"Lafiya lau lovely nayi busy ne kawai, dama ina so in shigo muyi magana".

"Okay to in jiraka kenan yau".

"Se gobe dai, yau zamu zauna da maimartaba".

"A fito lafiya, Allah ya ƙarawa Sarkin Giwa lafiya".

"Ameen, Ameen".

Kashe wayar yayi yana komawa kwance yana saƙe saƙe, hasashen yadda zasu ƙare da maimartaba yake bisa saƙon kiran da aka isar masa daga Sarkin, yana haka har bacci ya ɗauke shi.

_______________

Tsaye yake bakin shago yana miƙa wa Faruq ɗaya daga cikin abokan aikin sa a shagon takalman mata yana miƙa wa wasu ƴan mata suna gwada wa dan zaɓar wanda yayi musu, a sati da kwana biyar da zuwan Saraki shagon sun ƙara samun customers sosai Musamman ƴanmata wanda yawanci in suka zo haka za suyi ta ƙoƙarin jan Sarakin da hira sedai kallo basu ishe shi ba balle ya tanka musu, haka za suyi ta zuba sedai ragowar yaran shagon su amsa musu amma ba hakan ke hana su dawowa gobe ba.

Yanzu ma haka yarinyar se wani iyayi take yi amma Saraki ko kallo bata ishe shi ba dan wallahi shi ko kalar ta baze iya cewa gata ba, ita da Faruq take ta zubar ta wanda yawanci tambaya ce take masa game da Sarakin yana bata amsa iya wadda ya sani wata kuma yayi dariya har ta gama ta wuce.

"Kar ka kuma sanar da kowa komai a kaina Faruq, bana so".

Dariya Faruq yayi yana sara masa tare da faÉ—in Yes sir, murmushi kawai Saraki yayi da ba kowa ze San yayi ba, tuni su Faruq suka gane halin sa na rashin son magana da hayaniya shiyasa ba sa wani damuwa dan sun yi masa magana yayi murmushi ko body language.

Yau da wuri suka tashi kasancewar juma'a, wanka yayi yana komawa dan Allah yasani yana ƙoƙari da haƙuri da rashin wanka da yawa da yake yi yanzu a rana, singlet ya bari da dogon wandon jeans ɗin jikin sa ya ɗau Alqur'ani ya ɗora da bitar da yake yi dan baya son haddar sa ta Sami matsala.

Haka yake rayuwar sa kullum tsawon sati biyu kenan da zuwan sa garin manya, da safe yayi wanka ya dafa tea ya karya, ƙarfe tara ya wuce kasuwa, da rana baya cin komai dan baze iya cin abincin kasuwa ba, ƙarfe shida zuwa da rabi ya dawo gida, wanka yake fara yi se yai kwanciyar sa ya huta ko ya yi karatun sa kamar dai yau daga nan baya fita se masallaci magrib ya jira ayi isha sannan ya dawo daga nan kuma se gobe ze fito da asuba yayi Sallah.

______________

Ƙarfe sha biyu sannan suka fito daga Library, dukkan su sunyi wujiga wujiga banda Kisnah dan ita in tasa kanta zata yi abu to fa duk wuyar sa ita bata gani.

Motar Kisnah suka shiga suka fita duk da kowacce da tata ta zo, abinci suka fita ci dan basa cin komai na makarantar, EAT WELL restaurant suka je, vip suka shige akayi serving É—in su abinda kowacce ke so suka ci suka sha kafin suka fito.

Kamar ance ta ɗaga kan ta ta sauke idanun ta kansa, zaro ido tayi tana faɗin wow tare da kwass da gudu ta nu feshi, bata yi wata wata ba ta faɗa kansa.....................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

*Vote, comment and share fisabilillah*

Ouummey 07 (8/1/2022 3:23 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
Chapter 8 · 0% Book details