Sashe 13
Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har ƙofar makeken mansion ɗin ta me napep ya Kaita yana ta mamakin yadda akayi me rayuwa cikin wannan gidan ta iya fita ba mota har ta shiga ta haya, wajen security ɗin bakin gate ta karɓi dubu uku ta miƙa wa me adaidaita, da hanzarin sa ya zari dubu ɗaya yana faɗa mata tayi kuskuren ƙara masa kuɗi, da murmushi kan fuskar ta ta sanar dashi ba wai mantuwa tayi ba tana sane ta ƙara masa tare da masa fatan alkhairi, addu'a sosai yayi mata lokacin har ta shige kafin yaja motar sa yayi gaba.
Gaisuwar da ma'aikata ke mata ta amsa a gurguje tana shigewa tanƙamemen falon nasu, bata tsaya duban komai ba ta haye saman ta da gudu dan wanka kawai take san yi shine dalilin barin ta asibitin batare da neman kowa ba, a wannan karon kam ta san dole ta haɗa da ruwan zafi dan gasa kanta, sosai taji daɗin ruwan zafin dan ruwa uku tayi sannan ta fito ta kunna shower ɗin ruwan sanyi dan ɗauraye jikin ta kamar yadda ta saba, shirya wa ta shiga yi bayan ta fito daga toilet ɗin tana ture duk wani tunanin abinda ya faru a ƙwaƙwalwar ta dan tana son samun hutu kafin komai, seda ta shirya cikin three quarter da ya ɗan wuce gwiwar ta hakan be sauka kan ƙafar ta ba da riga t-shirt da ta kama ta sosai, kan bed ta faɗa duk da kuwa tana jin yunwa akan ta fi buƙatar bacci kafin komai.
Bacci tayi sosai da se kusan sha biyu ta farka, a gigice ta tashi dan yunwar da ta azalzale ta, slippers ɗin ta masu taushi da akayiwa ado,n gashin damisa ta saka ta sauka ƙasa, da ido kawu dake zaune kan sofa ya bita har ta shige kitchen, da kanta ta dafa noodles shaf shaf sedai kallo ɗaya zaka wa plate ɗin kaji ta burge ka, veggies ne a cikin ta a awadace banda niƙaƙƙen naman da ta zuba, iya ƙamshin ta ka zai shaida maka ba ƙaramin daɗi zata yi a baki ba banda kuma yanda tayi plating abincin, kan dining ta zauna ta fara cin abin ta da zafin sa dan yadda take ji bazata iya jira har ta ɗan give ba bayaga haka tafi son cin abinci da ɗan zafi, ruwa ta kora bayan ta gama kana ta ja kujerar baya ta jingina jikin bayan kujerar ta lumshe idanun ta har taji ta koma daidai kafin ta tashi ta nufi hawa saman ta sedai tuni kawu ya dakatar da ita.
"Zo nan daughter, tun safe nake jiran ki farka dan muyi magana se kuma naga yanzu kin taso da yunwa shiyasa ban tare ki ba".
Ɗan juyowa tayi ta kalli kawu kafin kuma ta dawo cikin falon kamar yadda yace tayi, kan sofar dake opposite ɗin shi ta zauna cikin salon zaman ta na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, gyaran murya kawu da takaici ya cika wa ciki yayi kafin ya ɗan haɗe rai irin ba wasan nan
"Jiya a ina kika kwana".
Kallo ta ƙure kawu dashi kafin ta saki murmushi silently
"A club".
Harara yake mata a kaikaice kafin yace "Amma ya akayi mutane na basu ganki ba".
Surprisingly ta ƙanƙance idanun ta
"Mutanen ka, bangane ba, dama ka sa abi bayana ne?".
A É—an daburce kawu ya gyara zama kafin ya É—an dake
"Yes, sure nasa abi min bayanki a ganar min inda zaki dan yawon ki ya fara damuna".
"Oh I see, so an dai tabbatar maka da club naje ko?".
"Sosai, sedai ba'a faɗa min inda kika kwana ba bayan ƙarfe uku ake rufe club, ke kuma se to nine na safe kika dawo gida".
"Na kwana gidan wani customer na ne, da matsala?". Ta faÉ—a tana É—age masa hira É—aya, baki buÉ—e kawu ya bita da kallo speechlessly dan duk yadda yake tunanin Kisnah ta nuna masa ta zarce nan.
Sama ta haye ganin kawu bai da abin cewa kuma, abinda be sani ba shine ta san yasa an bi bayan ta dan she's very sensitive hakan yasa ta lura da motar dake bin bayan ta duk da cewa a ƙware suke komai, ko da wannan incident ɗin be faru ba dama ta shirya plan ɗin da zata musu sedai kawai suji ta a gida.
Zama tayi kan gadon ta tana me tunano duk abinda ya faru jiya da dare da har ta ganta a asibiti, sosai komai da komai ke dawowa kan ta har abinda ya faru da Surry ta bisu, bawai Suma tayi ba a lokacin ko bata jin meke faruwa ba, tana jin komai sedai bata jin karfin jikin ta da bazata iya aikata komai ba haka kuma tana ji da ganin komai ne kamar a mafarki, kamar ba gaske ba, kamar a wata duniyar ba wadda take ciki ba.
Hawaye ne suka zubo idanun ta tuno yadda Surry tayi ƙoƙarin ceto ta da abinda ya sami Surryn.
Da sauri ta miƙe ta ciri wani pink Hill shoe kalar rigar jikin ta tare da scarf ta ɗaure kan ta wanda majority in zata skul ta ke ɗaurawa, wayoyin ta ta zuba cikin pocket kafin ta fara dialing number Meenah tana gangarowa daga step, a ɗan hanzarce ta katse Meenah dake ƙoƙarin fara tambayar yaya take wanda hakan ya zame wa duk ƴan Click ɗin nasu ɗabi'a tambayar ya junan su suka kwana
"Meenah Surry na asibiti fa, mu haÉ—u can yanzun nan, Ado Muhammad manya hospital, ki sanar dasu Leekha".
Bata tsaya jin me Meenahn zata ce ba ta katse wayar ta fita da sauri, a compound ta É—au wata dark Ash motar ta ta fice da sauri hankalin ta a tashe sanin kome ya samu Surryn fa saboda ita ne.
"Wannan anyi sheÉ—aniyar yarinya".
"Ƴar iskar yarinya mara mutunci".
"Allah ya shirya amma wannan yarinya bata da tarbiyya".
Ire-iren waɗannan kalaman da an wanda ya fisu muni Kisnah ke ta samu wajen mutanen dake kan titin dama na gefe, wasu har dasu tsinuwa wasu kuma fatan shiriya, ita kam tuƙin ta take yi cikin son ganin ta isa hospital ɗin da wuri, a haka ta isa Allah yaso ma gate ɗin a buɗe yake dan haka ta shige, parking tayi ta fita da sauri ko amsa gaisuwar da ma'aikatan asibitin ke mata bata yi ba, kun san halin mutane ina suka ga me maiƙo ko da basu sanshi ba balle ita da sunan ta da hoton ta yayi tambari a gari.
Ɗakin da aka nuna mata matsayin na Surry ta shiga da sauri, wani irin ƙarnin magani da warin allura yasa ta kai hannu ta toshe hancin ta, da sauri ta juya ta fita zuwa wajen likitan da ya duba su, bayanin tana son a sallame su ta canja wa Surayya asibiti tayi masa, be ja da nisa ba ya yarda ya basu sallama bayan ya kira ƴan sandan da suka kawo su, cikin tsananin jin daɗin ganin ta ƴan sandan suka yarda da sauri dan sun san tun da suka ga Kisnah to fa yau sun warke, aikuwa alkhairi sosai tayi musu suna ta washe baki, cikin ƙankanin lokaci aka canjawa Surayya asibiti zuwa wata tsadaddiyar private hospital aka canja mata, take a ka kai su wani tanƙamemen ɗaki kamar a gidan su, likitoci suka rufu kan ta aka fara bata kulawar data dace, banbancin asibitin kuɗi dana gwamnati kenan, *KULAWA*!
Ƙarar wayar ta yasa ta cire tagumin da tayi tana duban
screen É—in, ganin sunan Meenah yasa tayi picking tare da sawa a speaker.......................âœï¸
Â©ï¸ Ouummey 📚âœï¸.
*☑ï¸Ote, comment and share fidabilillah*.
Ouummey 10 (8/3/2022 3:52 PM )
💠💠💠💠💠💠💠ðŸ’
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠ðŸ’
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.Aâœï¸*
_________________________________
             Page 1ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
_____________________📖 "Hasbunallah wani'imal wakeel". Ya faɗa yana dafe kansa, shiru shagon yayi cikin jimamin tsaka me wuyar da ta same su lokaci ɗaya daga sama, dukkan su tagumi ne suka yi da hannu bibbiyu barin ma Alh Musa me shagon.
A hankali Alh Musa ya É—an motsa kafin ya fara magana cikin muryar dake bayyana ainahin damuwar da yake ciki
"Wannan abu da ya faru damu rubutacciyar ƙaddara ce da bawa baze iya guje mata ba, na daɗe da sanin muna da magauta da mahassada cikin kasuwar nan kuma abokan sana'ar mu ne sedai ban ɗauka abin ze iya kaiwa har haka ba".
Numfashi yaja ya sauke a ɗame kafin ya cigaba cikin ƙarfin hali
"Ina me baku haƙuri domin nima ba haka naso ba sedai ba yadda muka iya da hukuncin Allah, ina me baƙin cikin sanar daku na sallame ku gaba ɗaya a yau, Allah ya baku wasu hanyoyin samu ya yiwa rayuwar ku albarka ya saka muku da alkhairi bisa zaman amanar da kuka yi dani da junan ku, duk wanda na ɓatawa a zaman mu ya yafe min dan ɗan adam ajizi ne, nikam baku taɓa min komai ba koma kun min na yafe muku duniya da lahira".
Shiru duk sukayi wasu na sharar hawaye, ko a shekaran jiya basu taɓa kawo tunanin haka na iya faruwa dasu ba, sedai in akace kana da magauta da mahassada to fa se kariyar Allah kawai.