← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 64

Sashe 46

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan dena insha Allah, Amma for Hameedah dole nayi magana dan ta ƙure ni ne, na daɗe da sanin tana min hassada da baƙin ciki akan komai, ko kasan murna tayi lokacin da na kasa assignment ɗin CON005?, kuma na gani na gane amma na nuna ban san tana yi ba, yanzu haka da muka fito wasu banzan maganganu take faɗa tsakanin ni da kai wai shine dalilin da na baka aiki a office ɗina dan kullum mu kasance tare, shima na danne rai na to kuma meye ruwan ta da kai, shiyasa na ci mata dan gobe kar ta kuma min dan wallahi in ta kuma se ta gwammace rungumar transformer kan matakin da zan ɗauka kanta".

ÆŠan murmushi ya saki ganin yadda take masifa kamar har yanzu Hameedar na gaban ta

"On her behalf, she's really sorry Miss, zata kiyaye gaba".

"Better for her". Ta faɗa tana kau da kanta gefe, a hankali a hankali yake ɗan mata hira though ba iyawa yayi ba amma ya ƙoƙarta dan ganin ya sauke mata fushin da take har se da yaga tayi ƴar dariya kafin ya ƙyale ta.

Yana yin parking tayi masa sallama tare da wuce wa cikin gida shima ya fice zuwa É—akin sa.

Kashe gari da tashin hankalin fake currency ɗin nan suka tashi, sosai suke ta kan bincike amma ko trace ɗin mutumin da ya sayi kayan ba'a samu ba, hankali fa ya tashi manager ya shiga cakwakiya dan bank ɗin da yaje depositing riƙe shi suka yi suka handling ɗin shi wa hukuma kan zr damfare su da kuɗin ƙarya, ba ƙaramin kuɗi Kisnah ta zuba ba kafin aka sake shi.

Duk wanda yaga kawu kuwa ze yi zaton shine ainahin me dukiyar dan yadda yayi wujiga wujiga dashi ya fita kamannin sa wajen neman yadda za'a yi ayi tracing mutumin, kai kamar ma yafi ita Kisnahn damuwa dan se ita ta koma tana kwantar masa da hankali kafin asamu ya É—an daidaita dan har suma biyu yayi.

Cikin wannan tashin hankalin aka kawo takardun hannun jari da wani Company ya zuba a K&S flour and food stuffs wanda dole ana buƙatar signing ɗin ta kafin ayi documenting a Kuma ba wa su waɗancan copy ɗin su.

Da wanna damar kawu yayi amfani wajen haɗawa da fake takardun ownership ɗin nan ya kai mata tayi signing sedai ba shi ya kai mata direct ba manager ɗin ta ya bawa ya kai, bata tsaya duba komai ba ta yi signing a duk inda akace tayi tare da bawa Saraki ajiya kan ya bawa manager in ya dawo karɓa ita kuma ta wuce station dan fa bank ɗin sun ƙi haƙura suna batun shigar da ƙara dole ana buƙatar ta dan ganin ko za'a iya cimma maslaha in suka zauna.

Gyara takardun yake yana girgiza kan sa ganin yadda gaba ɗaya ta ajiye takardun a hargitse kafin ya shiga jera su ɗaya bayan ɗaya yana ajiye kowacce inda ta dace ta hanyar karanta heading ɗin jiki har yakai kan ta ownership ɗin, cikin matuƙar mamaki ya ciro su har guda huɗu ya ajiye a gefe ya ƙarasa gyara waɗan can kafin ya shiga karanta su ɗaya bayan ɗaya, in akace mamaki to an rage matsayin yanayin da yake ciki, wani irin tsoron Allah ne ya ratsa shi a zaunen da yake ganin tsantsar rashin tsoron Allah, mugunta da kuma ƙarfa ƙarfar da wasu da suka daɗe da kwashe kayan su gaban manzon Allah suke yuƙurin aikatawa.

Takardar shedar mallakar kamfanoni ɗaiɗai har huɗu ne, K&S construction, K&S flour and food stuffs, K&S Furnitures, se K&S drinks, Kuma wai mugun se da ya duba manyan da suka fi girma, bunƙasa da kawo riba, dafe kansa yayi cikin tunanin waye me wannan aiki dan duk yadda aka yi wanda yasan ciki da bai na Companies ɗin ne da wannan aiki, kuma baya tantama shine boss ɗin Emeka, shine ƙashin bayan asarar da akayi yau haka kuma shine yake assasa duk wata asara dake ta afkuwa cikin kamfanonin a kwanakin nan.

Seda gaban sa ya faɗi da sunan kawu ya faɗo ran a, da sauri ya girgiza kan sa telling his mind it's impossible, yes impossible ace wai kawu ne behind all this evil act, no be ma yarda ba, taya ma ze zama kawu bayan shine ke kula da duka dukiyar tun kan ta girma kuma dukiyar tai ta haɓaka batare da wata matsala ba se yanzu, beside haka ma kalli fa tashin hankalin da kawun ya shiga a ɗazu, Bama shi bane, baze zama shi ba, ya sake jadda dawa a ran sa, to waye???

Yana cikin wannan tunanin har manager ya shigo be sani ba dan ya daɗe yana knocking Amma ba amsa so yayi tunanin ma ba kowa bari ya shigo ya ɗau takardun kawai ya wuce dan su kawu na jiran sa kasancewar da sanin sa aka bashi takardun ya aka bayan sun masa alƙawarin maƙudan kuɗaɗe.

Wani irin mazari jikin manager ya ɗauka ganin takardun a hannun Saraki yana jujjuya su tare da sake karanta su kamar wanda aka bashi aikin haddar su dan se da ya zamana ya haddace every single word dake kan papers ɗin nan, a hankali manager ya fice daga office ɗin batare da ya bari Saraki ya lura da shi ba, jiki na rawa ya zaro wayar sa ya shiga sanar da kawu halin da ake ciki bayan ya sami waje ya laɓe wanda daidai lokacin Saraki da yaga fitar sa ya biyo bayan sa da takardun a hannu ya na neman sa dan ya bashi tun kan yayi nisa.

Daidai wajen elevator yake jiyo magana ƙasa ƙasa dan haka ya ƙarasa a hankali ya ɗan laɓe dan jin waye ke waya haka cikin rawar murya alamun rashin gaskiya ga kuma ɓuyan da yayi wajen da yake tunanin ba wanda zeje dan elevator ɗin tsoho ne an dena amfani dashi so bame zuwa ta wajen se ta kama.

"Kayi haƙuri Alh ba laifi na bane, na kai takardun kamar yadda kace wallahi ban san yaya akayi aka samu wannan matsalar ba, kuma alamu sun nuna ita bata karanta ba tunda ta saka hannun wannan sabon ma'aikacin nata ne na samu yana dubawa".

Shiru yayi alamun saurare daga ɓangaren da yake kafin ya cire wayar faga kunnen sa yasa handsfree da alamun baya ji sosai kenan sedai ya rage Muryar yakai ta can ƙasa

"Lallai manager baka san da wa kake wasa ba , bari kaji in faÉ—a maka wallahi ko da wasa naji sunana ya fito a wannan batun se ka gwammace mutuwar ka kan rayuwar da zan sa kayi, kar kuma ka manta da nasan gidan ka, Æ´aÆ´a huÉ—u ga kuma tsaleliyar mata, Har yau Sama'ila na ke kuma kasan abinda zan iya aikatawa".

Gumi manager ya shiga sharewa jin kawu ya kashe wayar sa, da sauri Saraki ya lallaɓa ya bar wajen sedai tuni manager ya ganshi dan yaji sautin takalmi kamar ana tafiya a hankali, wani tashin hankalin manager ya Kuma shiga haka kuma be yi ƙasa a gwiwa ba ya sake kiran kawu ya sanar dashi.

******

"Ya zama dole su mutu a yau dukkan su, daga ita har É—an iskan yaron dake neman zame mana barazana, a yau zasu mutu base gobe ba dan a kan dukiyar nan zan iya yin komai akan kowa, dama na kawo waccan hanyar ne dan mu bar ta da ranta tunda kuma bata san hakan zata tafi tabi mattacen uban ta yau".

GyaÉ—a kai kawu yayi cikin yarda da batun Alh Haladu kafin ya zaro wayar sa ya shiga danna kira, within minutes aka É—auka ya kuma bada umarnin kisa ga duk wanda ke cikin motar su Kisnah bayan ya bada lambar motar ya kuma haÉ—a da location É—in da suke da kuma duk Possible titin da zasu iya bi su kai gida.

*******

A rikice ta dawo K&S furnitures saboda kiran ujilar da Saraki yayi mata, a parking space ta same shi tsaye yana jiranta fuskar sa ɗauke da wani yanayi, komawa mazaunin ta tayi ya shiga driver's side tare da tashin motar ya fice, seda ya hau kan titi kafin ya ɗora mata takardun a kan cinyar ta, da kallo ta bisu kafin a hankali ta ɗauka ta shiga karantawa, cikin tashin hankali ta ɗago cikin don yi masa magana sedai ko kafin ta kai ga hakan wata babbar mota ta zo ta daki tasu, hantsila wa motar su ta shiga yi kafin cikin ikon Allah ta tsaya daidai hakan yasa wata babbar motar yowa kan su sedai tuni Saraki da ya fahimci an shirya musu ne ya figi motar cikin wani irin azababben gudu hakan ya sa itama babbar motar rufa musu baya..............................✍️.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, comment and share fidabilillah.

Ouummey 31 (8/22/2022 9:20 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                          Page 3️⃣1️⃣

________________________📖 Tsawon lokaci suna zuba azababben gudu kan shimfiɗaɗɗen titin garin har suka fara ficewa daga cikin ainahin garin suna dosar daji ka, juyawa yayi ya kalli bayan sa ta cikin mirror ɗin motar, wani irin ƙure speed yayi ganin har lokacin babbar motar na bin su a baya itama cikin nata gudun.

Cikin tashin hankali ya kallo gefen da Kisnah take zaune kamar mara rai tsabar shock da ruÉ—anin da take ciki

"Ki É—aura seat belt É—in ki da sauri, am increasing the speed now dan za su iya cimma na".
Chapter 46 · 0% Book details