← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 64

Sashe 3

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗaya daga cikin ƙofofin dake falon ce ta buɗe yayin da wata farar mace mai matsakaicin tsayi ta bayyana, ba laifi za'a iya sata cikin jerin mata masu kyau dan ba laifi akwai wadatar idanu se ko hancin ta da bai fiya tsayi sosai ba.
Ƙarasa fitowa tayi ta nemi ɗaya daga cikin kujerun dake falon ta zauna kafin cikin yamutsa fuska ta fara magana

"Haba Megado, me yasa kin fiya wutar ciki ne? Ko kin san ihunki ne ya tashe Ni daga bacci? Dan Allah ki dinga sassauta wa haba".

Wani kallo budurwar da aka kira maigado takewa mahaifiyar tata
"Ai dai kin san bazan zauna ina wage baki alhalin ba ayi min komai ba ko? To kiyi ewa waccan mara mutuncin yarinyar magana dan wallahi ta kaini maƙura dan haka zan fara ɗaukar mataki".

"Ke wai me yasa kin fiya wauta ne, kin san sarai yarinyar nan ba mutunci ne ya cika ta ba yanzun nan zata saka mahaifin ku yazo ya ci mutuncin mu tunda kin san tsoron ta yake ji, nace mu bi a hankali kema kin san bazan taɓa ƙyale ta ba dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzu faɗa min me tayi miki?

"Abinci fa nasa Rayya ta dafa min saboda ina da lectures Kuma ni wanda suka dafa be min ba Shine ƴar iskar nan ta karɓe ta cinye, yanzu gashi in nace Zan jira makara zanyi".

"Ki barta dani, ba tana taƙama dukiyar ta bace muke cin arziƙi, na miki alƙawarin sena wulaƙanta rayuwar ta kuma kin tabbatar da zanyi ko?

Gyaɗa kai maigado tayi kana ta karɓi dubu biyun da mahaifiyar tata ke bata ta saka a jaka, buɗe baki tayi zatai magana sai dai ƙamshin da ya gauraye falon tareda takun takalmi ne ya katse ta.

"Ƙwas ƙwas ƙwas" haka sautin takalmin ke bayarwa wanda ya shaida na mace ne, a hankali suka ɗaga kansu zuwa staircase ɗin dake parlon duk kuwa da sun tabbatar ita ɗin ce ke saukowa.

Matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekaru 18-19 ba, fara ce sosai domin skin ɗin ta har wani yellow yellow yake yi saboda tsabar hutu da jin daɗi, sanye take da wata guntuwar red gown da bata gama ƙarasa sauka a gwiwar ta ba, sosai rigar ta kamata ta kuma haskata, ƙafar ta na sanye da red high hill takalmi se gashin kanta da ya sha gyara ya lafe a gadon bayan ta se ko red hat da ta ɗora masa, hannunta ɗaya riƙe da car key da take karkaɗawa se ɗayan riƙe da mini red purse da ta sha adon stones se walwali da ɗaukar ido take yi.

Ƙarasawa tsakiyar falon tayi cikin takunta na cat walk, hannu ta saka ta ture hat ɗin baya hakan yasa fuskar ta bayyana kana ta ɗago ta dubi Mommy dake zaune ta sakar mata wani makirin murmushi.

Se yanzu na tabbatar da kyanta domin iya fuskar ta abar kallo ce, wasu irin idanuwa gare ta masu matuƙar maiƙo da ɗaukar hankali wato oily eyes, Haka Kuma ƙwayar idanunta ba baƙa bace golden brown ce wadda kalar take sake dulmiyar da duk me kallon ta, idanunta matsakaita ne masu ɗauke da zara zaran thick black eyelashes Wanda suke kwanciya sosai in ta rufe idanun, haka girarta cikakkiya ce dan har tana neman haɗewa sai dai ba ta ƙarasa haɗewar ba, siririn hanci gare ta mai matsakaicin tsayi se ƙaramin bakin ta mai ɗauke da kyawawan luscious pink lips Wanda kallo ɗaya za'a yi musu asan zasuyi matuƙar daɗi da laushi a baki, a taƙaice dai ita ɗin na tsananin kama da jarumar nan sridevi ta ƙasar India.

KarkaÉ—a mukullin hannunta tayi daidai fuskar Mommy kafin ta ce mata "Hi".

Takaici da baƙin ciki ne suka cika zuciyar Mommy da ɗiyar ta mai gado sedai ita gogar ko a jikinta, juyawa tayi ta nufi entrance ɗin falon ta fita, sai da ta buɗe ƙofar sannan ta juyo ta kalli Mommy cikin yamutsa fuska tace "oops, kinga na manta, ki faɗa wa mijinki account balance ɗina yayi low, Ina buƙatar transfer ɗin 2 millions urgently in ya fito".  Tana gama faɗar haka ta fice daga falon zuwa farfajiyar gidan.

Girman farfajiyar gidan kawai ya isa sanar da ainahin girman gidan, domin kuwa kuwa manya manyan flats uku ne a cikin gidan wanda duk flat É—aya ya yi girman gidan masu rufi asiri uku ko huÉ—u.

Ba tareda ta tsaya amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke ma ta ba ta ɗaɗɗaga musu hannu dan sauri take yi, wata jar mota ta buɗe wadda ke cikin motoci sama da goma dake harabar gidan, motar se ƙyalli da ɗaukar ido take yi, shiga ciki tayi tai mata key kana ta fice daga gidan cikin matuƙar gudu kamar yadda ta saba.

Gudu take yi sosai yayin da ta ƙure volume ɗin motar cikin waƙar Dil to pagal hai dan ita ɗin die hard fan ɗin Indian films and music ce, yanzu haka cinema zata je kallon sabon Film ɗin jaruma Rani me suna Black, gashi ta kusa makara duk datasan bata da matsalar ticket nata a ajiye yake.

Wayar ta ce ta fara ringing hakan yasa ta rage volume ɗin waƙar tai picking tareda sa wayar a speaker ta ajiye ta.

"Hey Kisnah beauty, kina Ina ne, gamu har mun shiga cinema baki ƙaraso ba?

"On my way babe"

"Okay, se kin ƙaraso".

Kashe wayar tayi ta ƙure volume ɗin waƙar ta, tana tuƙi tana bin waƙar tareda girgiza kanta cikin zallar nishaɗi.

Gudun da take yi sam ba na hankali bane amma ba yadda mutane suka iya da ita dan har sun fara sabawa, shiyasa da yawa masu ababen hawa ke kaucewa suna bata hanya, wasu na zagi wasu na tsine mata yayin da ita bata masan sunayi ba.

Haka salan tuƙin ta yake shiyasa Bata driving da kanta se dai ta ɗau driver, to driver ɗin nata ne babansa ba lafiya dole ya ajiye aikin dan kula dashi, yanzu hakan tana kan neman wani ne shine fa kwana biyu take tuƙa kanta dan bazata iya zama gida ba dole se ta fita.

A gurguje tayi parking motar ta dan lokacin har an fara Film É—in, hakan yasa tayi wrong parking tayi blocking wasu manyan motoci uku.

Zama tayi a gurin zamanta na musamman inda ta sami ƙawayenta huɗu duk sun iso, ba tareda ta kula kowacce ba ta zauna tareda fito da park ɗin creamy crackers ɗin ta ta fara jefawa a baki tana maida hankalin ta kan Film ɗin.................📝

             Ouummey ✍️

☑️ote
Comment
Share.

Ouummey 03 ( 7/29/2022 7:56 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

                         Page 3️⃣

__________________📖 jefa crackers ɗin take bakin ta yayinda hankalin ta gaba ɗaya ke kan moves ɗin jaruman.

Kwaɓe fuska tayi lokacin da aka haska scene ɗin da jarumi Amitabh bachan yake saka jaruma Rani Mukherjee a cikin ruwan sama, kan kace me se ga hawaye na zuba a fuskar ta, meenah da ta san haka ze faru ce ta riƙo ta jikin ta tana lallashin ta, juyowa ragowar sukayi, Hameedah, Surayya, da Maleeka sukayi suna sake comforting ɗin ta har tayi shiru, tagumi ta saka tana cigaba da kallon, ita ɗin me tausayi ce most especially ga masu nakasa da kuma talakawa, most of the times in tazo cinema se tayi kuka saboda tausayi, either na yadda wasu ke fama da talauci, yadda ake ciki zalin wasu ko rabuwar masoya kuma ba hakan ne ze Hana ta dawowa gobe ba.

"Yeeeeeeehhhhhh".  Ta buga tsalle tana ihu lokacin da jarumar ta kammala degree ɗin ta tana speech ranar convocation , gaba ɗaya ta ruɗa wajen da ihun ta da tsalle wai murna take, majority na occupants ɗin ji suke kamar su shaƙe ta dan takaici yayinda minority basu ko kalle ta ba dan sun saba da ihunta tun bare in tana kallon wrestling, yanzu zaka ji tana ihun "yauwa, dake shi, ɗaga shi ka buga shi, karka bari ya yarda kai, wayyo, tashi, yauwa kauce, ehen kai masa duka........" and many more of this.

Ɗaukar ledar crackers ɗin ta tayi ta nufi hanyar fita tana waƙe waƙen ta da suka zauna a bakin ta kai kace ita ce ta raira su, bin bayanta su Hameedah suka yi yayinda meenah ta ƙara sa suka jera suna tafiya har suka fita daga cikin ainahin cinema ɗin zuwa parking lot ɗin da ta ajiye motar ta.

Maza huÉ—u suka tarar tsaye jikin motoci ukun da tayi blocking saboda saurin da take yi, nufar motar ta tayi zata buÉ—e É—ayan ya sha gaban ta yana jifanta da wani É—an iskan kallo, É—agowa tayi itama tana masa kallon mamaki dan bata ma lura da cewa tai blocking É—in su ba.

"Wace iriyar kidahum ce ke da Zaki blocking É—in mu da wata gwanganin motar ki, ko baki da idanu ne da baki ga motocin mu ba lokacin da zaki yi parking?

Sakin baki tayi tana kallon shi jin wai ita yau wani useless being ya Sami bakin zagi, bata gama dawowa daga duniyar mamakin ba ta ga wani ya zo ya tsaya gefen wancan yana hararar ta kafin ya fara magana

"Kayi mamaki ne Haroon, kalle ta fa, da ganin su kaga ƴaƴan talakawa masu shegen buri da fafa, anje an aro kaya da mota an shigo cinema dan a sami wani me ɗan maiƙo a liƙe masa, bana tantama ta ga shigar mu shine bari tayi blocking ɗin mu dan tayi driving attention ɗin mu towards her, sedai bata san tayi a banza ba, mara hankali kawai".
Chapter 3 · 0% Book details