← Book details Saraki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 64

Sashe 50

Saraki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin ba wanda ya ja da hakan tunda dai ba wai ƴaƴan su mata akace su dinga bayar wa ba haka kuma tun daga lokacin ma babu wanda ya kuma yadda ya sauki baƙuwar budurwa se sau biyu da hakan ya faru kuma duk se da aka aiwatar da sharaɗin boka wassai aka kaiwa lamiɗo su turaka tsawon sati ɗaya kafin ya sallame su......................✍️.

Ƙaƙa ƙara ƙaƙa!!!!

Wata sabuwa in ji É—an caca,
ga Kisnah ga lamiÉ—o ga Kuma Saraki,

shin me kuke tunani bayan an tabbatar wa da lamiÉ—o cewa Kisnah budurwa ce?

Shin kuna tunanin Saraki ze Bari a mallakawa lamiÉ—o Kisnah ne na tsawon kwanaki bakwai?

Shin kuna tunanin Kisnah da Saraki zasu bar ƙauyen Banda ne ko kuwa?.

Ni dai nasan...............ban san komai ba😝😂.

©️ Ouummey 📚✍️.

☑️Ote, Comment and share fisabilillah.

Ouummey 33 (8/24/2022 10:08 PM )

💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠

Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey

*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*

______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

_________________________________

Page 3️⃣3️⃣

*Wannan PAGE É—in sadaukarwa ne gare ku my best commenters*

*Itx_ammin_halimatou*
*Maman nabeehat*
*Maman Mu'awiyah*
*Mom Islam*
*Mom misra*.
*Amina tijjaney*
Zainab Habib*
*زينب*
*Ihsana*
*Real bloom*
*Da ma duk wanda ban ambata ba ina godiya da ƙauna, saraki da Kisnah sunce a faɗa muku You Are really amazing and loving*

_________________________📖 "Mun sami labarin ka sauke budurwa a gidan ka arɗo, ko za mu iya sanin dalilin hakan?".

Da sauri arÉ—o ya gyara zaman sa yana share zufa da hannun rigar jikin sa da taci datti kamar ba gobe

"Allah yai maka tsawan kwana na tsinci wasu matasa biyu mace da namiji kwana takwas da suka wuce, a yanayin da na tsince su suna tsananin buƙatar taimako, a nawa idanun se na ga kamar ma'aurata hakan ne ma yasa na ɗauke su ba tare da wani tunani ba, yanzu haka ita macen ta sami lafiya har ta iya fita jiya shine suka haɗu da lamiɗo, shi kuma namijin yana jinyar karaya ne a hannu duk da cewa hadda gocewar ƙashi a ƙafa amma tuni wanann ya warke, tun ɗazu da aka sanar dani abinda ya faru da har lamiɗo ya nemi na zo fada nasan nayi kuskure, nayi kuskuren ɗaukar matasan matsayin mata da miji haka nayi kuskuren rashin sanar da kai labarin su, a yimin afuwa baffa arɗo, hakan ba zata sake faruwa ba nayi alƙawari".

GyaÉ—a kai kawai baffa arÉ—o ya dinga yi har arÉ—o ya gama bayanin sa kafin ya amsa shi

"An maka afuwa arɗo sedai kasan ya zama dole a miƙa wannan budurwa ga lamiɗo yau ɗin nan ba se gobe ba dan kaucewa fushin rauhanai".

"Yanzu za ayi hakan baffa arɗo, ina komawa gida zan rakota gare ka se a miƙa ta ga lamiɗo, Allah ƙara tsawon rai ina godiya da sassaucin faɗa gare mu".

******

Cikin rashin daɗin rai arɗo yake taka ƙafar sa kan ƙasa a hanyar sa ta komawa gidan sa, be taɓa sanin yarinyar budurwa bace da baze ɗauko su ba badan komai ba se dan guje mata shiga turakar lamiɗo sedai aikin gama ya riga ya gama dan ba yadda za iya tsallakewa umarnin baffa arɗo da boka wassai, dolen dolen sa ya kai ta ga lamiɗo dan hakan ne zaman lafiyar su daga shi har su.

Ko da ya ƙarasa gida zaune ya samu su Bingel da Nenne cikin fargaba, yana shigowa suka bishi da kallo cikin son bayani sedai bece komai ba har Nenne ta kasa daurewa ta tambaye shi da baki, shiru yayi na wasu lokuta kafin ya buɗe baki ya fara musu bayanin abinda ke akwai cikin rashin daɗin rai, fargaban su ce ta ƙaru jin abinda ke faruwa dan Allah ya saka musu ƙaunar Kisnah cikin zuciyoyin su, ba zasu so abu makamancin haka ya faru da ita ba sedai ba yadda zasu yi.

Arɗo ya daɗe zaune wajen ƴar sa da matar sa nan ƙofar bukkokin su dake kusa da kusa da juna kafin ya yi ƙarfin halin miƙewa ya shiga ɗakin da Saraki yake dan ya sanar dashi abinda ke faruwa kuma dama Nenne ta sanar dashi Kisnah na tare da Saraki a ɗakin.

Da sallamar da ya koyo a birni da yake kai kaya ya shiga ɗakin fuskar sa ɗauke da damuwa ƙarara, da sauri Saraki ya buɗe idanun sa da ya rufe yana kallon shi tare da ƙoƙarin gyara zaman sa

"Sannu da shigowa arÉ—o, sannu da zuwa".

Be sami zarafin amsawa Saraki ba ya samu waje ya zauna daga gefen damar Sarakin yayinda Kisnah ke gefen dama, shiru suka yi a É—akin ba wanda yace komai kafin arÉ—o ya daure ya tambayi jikin Saraki

"Ya jikin naka?.

"Da sauƙi arɗo, ina iya motsa hannun ma a hankali baba".

"Angodewa Allah, Ina maka fatan samun sauƙi cikin sauri".

Da Amin Saraki ya amsa suka sake yin shiru na tsawon lokaci

"Kayi haƙuri Ahmad, ban ɗauka za'a sami matsala ba da zaman ku a nan shiyasa ban sanar daku wani abu ba dangane da garin namu sedai gashi wata matsala ta Kunno Kai da tafi ƙarfin magance wa ta, ban san ya zan maku bayanin abinda ya faru ba dan shigowa ta ɗin nan daga gidan baffa arɗo nake wato me garin mu".

Zuba masa ido Saraki yayi cikin son matsalar da yake maganar tana son faruwa, fatan sa ɗaya Allah ya sa ba a fitar yarinyar can bane taje ta jawo musu wata maganar, shikam be san ya ze yi da ita ba, in suka bar nan ina zasu je, har yanzu ma basu san takaimaimai a wane garin suke ba su dai sun farka sun gamsu a wannan ƙauyen kuma be wani damu da ya tambayi ina bane tunda ba lafiyar barin garin gare shi ba.

"A shekarun baya munyi fama da wata annoba sanadin wata budurwa mayya da ta shigo mana, a cikin neman masu maganin da muke ne Allah ya kawo wassai garin nan da ya zama sanadin samun sauƙin al'amuran har muka dawo muka cigaba da rayuwa kamar da sedai ya kafa mana wasu sharuɗa da muke rayuwa a wannan ƙauyen akan su, sharaɗin shine ba karɓi baƙuncin budurwa mara aure ba in kuwa hakan ya faru to za mu miƙa ta ga Sarkin gobe lamiɗo auta ga Sarkin yanzu ya tare da ita a turakar sa na tsawon sati ɗaya.

Kayi haƙuri a lokacin da na tsince ku na yi zaton mata da miji ne shiyasa ban ji ko ɗar ba na ɗauko ku zuwa wannan garin, a fitar da yarinyar tayi jiya suka haɗu da lamiɗo kuma ya gane budurwa ce ba matar aure ba saboda wassai ya basu maganin da zasu dinga gane budurwa da matar aure shi da baffa arɗo dan gudun yaudara, yanzu haka baffa arɗo da lamiɗo suna jira ne na miƙa wannan yarinya ga turakar lamiɗo a yau, shine nazo na sanar da ku".

Kallon sa kawai saraki yake yana fassara dukkan bayanin sa tare da miƙa shi matatar bayanai wanda cikin lokaci kaɗan ya fahimci me arɗon yake nufi, in akace tashin hankali to kaɗan kenan, taya ze yarda haka ya faru? Ta ina ze iya zuba ido har hakan ta kasance? To meye ma amfanin guduwar su daga waɗancan makasan, meye banbancin wannan sharaɗin da bindiga hannun ƴan ta'addar kawu, in hakane ma gwara da ace tsayawa yayi aka kashe su gaba ɗaya, a ganin sa waccan mutuwar ma tafi sauƙi kan wannan batu dan mutuwar tsaye ne kawai.

A hankali ya juya ya dubi inda take kwance tana bacci peacefully, baccin da kana gani zaka san ta kwana biyu bata samu irin shi ba.

Dawo da duban sa yayi ga arɗo dake zaune ya duƙar da kai ƙasa, abubuwa da yawa ke zuwa ransa sedai ya rasa wanne ze yi, me ze yi da zai cece ta, ya sani baze yiwu yace zasu bar garin ba dan bashi da isasshiyar lafiyar tafiya dan har yanzu ba wai hana taka ƙafar sa bane an dai kunce ɗaurin ne, to idan ma zasu tafi ina zasu nufa su da basu san a ina suke ba haka kuɗi fa, su da basu da ko sisi dame zasu tafi, dole ya ajiye ma wannan batun dan ba mafita bace.

"Yanzu babu wata mafita ga hakan arÉ—o dan bana tunanin zan iya yadda da wannan sharaÉ—in na garin ku".

Girgiza kai arÉ—o yayi cikin son tabbatar wa

"Kayi haƙuri samari amma babu wata mafita se hakan".

Sake yin shiru suka yi ya rufe idanun sa cikin karanto duk addu'ar da ta zo bakin sa, fatan sa Allah ya bashi wata mafita da zata kange wannan matsalar dake neman kutso kai rayuwar su banda kuma wadda suke ciki.

Tunani yake yi sosai har yayi zurfin da be san lokacin da arɗo ya tashi Kisnah ba, ƙoƙarin fita da suke yi ita da arɗo ya sa ya farga haka kuma a lokacin ya yanke shawarar da yake ganin ita kaɗai zata kore wannan musiba dake neman danno kai gare su, da sauri ya dakatar da arɗo dake neman bin bayan Kisnah da ta riga ta fita

"Zan je fada arÉ—o, Ina son na biku dan Allah".

Tsayawa arɗo yayi cikin ɗan ƙure shi da kallo kafin ya girgiza kai

"Ta ina zaka iya bin mu Ahmad, har yanzu ba wai ƙafar ka ta gama lafiya bane".

"Kayi haƙuri amma dole na biku bana, akwai abinda nake san sanar da Sarkin ku".

Ganin ya dage yasa arɗo nemo me amalanke ya biya shi sannan suka kama Saraki suka taimaka masa ya shiga kafin shima da Kisnah suka shiga me amalanken ya ja, tsakanin su da gidan Sarkin akwai tafiya sosai sedai gare su ba wata tafiya bace, rashin lafiyar Saraki yasa ya biya amalanke da da ƙafar su zasu taka su je.

A ƙofar fada suka sauka nan ma arɗo da me amalanke ne suka taimaka wa Saraki zuwa cikin fadar Kisnah na bin su tana ƙare wa gurin kallo.
Chapter 50 · 0% Book details