← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 67

Sashe 8

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

🅿️ 17__18
*Jinjina ga MAMAN SHUREIM hakika kin cancanci* *yabo na ban girma ...Allah ya* *miki jagora a lamuran ki ....thanks for all .*
. *wannan page d'in* *na kine ke kad'e Fasma tace kiyi* *yadda kike so* *da shi*. .. _Allah ya qara donkon zumunci _
17__18
```Manzon Allah (SAW) ya ce''Sallar jam'i tafi sallar mutum guda daya da daraja ishirin da bakwai''
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi``` .
Wani mummunan fad'uwar gaba yarima Murad yayi dan danan zufa ta karyo mishi duk da AC da ke kunne yace Dady two week fa ?kamar zeyi kuka .
Me martaba yace kwarai kuwa kuma bazan karb'i excuse d'in kin rashin zowanka ba dan haka sati me kamawa ina son ka tattaro ka dawo gida....
Beyi iya cewa komi ba se to in sha Allah zanzo..
Sarki yace yauwa Allah yayi ma albarka ...
Ameen yace lokacin idonshi har sun kad'e sunyi ja kamar wuta ..
Suna gama wayar da Sarki ya kuwa dannawa fulani kiran .
Sallama kawai ya iya yi mata ya fashe mata da kuka..kamar wa'i qaramin yaro
Bata hanashi ba seda yayi me isar shi sanan tace Murad ..
Jin ta kirashi da sunanshi yasa ya nutsu ta wayar kamar yana gaban ta dan bata fiye kiranshi da sunan ba se de inhar maganar dazata fa'da tanada matuka mahimmaci
Fulani tace Murad ina so kayi hakuri ka zama me biyyaya ga iyayen ka ..kasan baza mu tab'a zab'a maka abunda ze tab'a cutar da kai ba.......ina son ka zama me tawakali a rayuwarka .....kaza me karbar da kuma yin imani da kaddarar rayuwa au ta alheri wala ta sharri ....
Na sani ba tun yauba kake kai bazaka tab'a yin aureba .....kasan kuwa aure sunna ce babba ....Manzon Allah SAW ya na ce wanda baya son sunnata to baya tare dani ...shin kana son kasance wa cikin mutanen da basa tare da Manzon tsirane...?
Kamar yana gabanta yake girgiza kai ..yace Astagafirullah....Momy kiyi hakuri daga yau banza sake ba. ....
shikenan Allah yayi mana zab'i na alheri..
Ameeen tace Allah ya maka albarka.....to baza ka tambayyi wacce yarinya ce ba?
A'a Momy duk wacce kuka zab'a min tayi mini dan banida zab'in da ya huce naku....
Shikenan Son Amma ko sunan ta bazaka so sani ba?
Bayason Fulani ta fuskancin wani abun kawai se yace ...ina so mana ..
Sunnata MAYSAM
seda gabanshi ya fad'i jin sunan aman ya dake yace ..shikenan Momy inada aiyuka anan Office ...next week ganinan zowa in sha Allah..
Cike da murna fulani tace Allah ya kawoka lafiya a ganinta ita ya sauko ya amince da auren daga nan bata san qarfin hali kawai yake yana danne zuciyarshi..
Ranar wuni yayi yana tuno zancen auren ..gaba daya ya kasa qarasa aikin dayake se gidanshi ya koma ...yana me bakin cikin wannan al'amari..
.
A b'angaren su Malan Musa sun isa lafiya ...Murza se kaf2 da Maysam take tana tsoron Malan Musa yayi mata maganar karayar Maysam amma se taji shiru hakan yasa ta saki jikinta dan duk a ganinta Maysam bata gaya mishi yanda akayi.ba..
Ai kuwa Malan Musa na fita koda massalaci ne to fa seta san duk yanda zatayi ta muzgunawa Maysam koda rankwashine kuwa...
Bayan kwana biyu da dawo warsu da dare tsakani magarib da isha'i suna zaune suna hira Malan Musa yace Murza dama akwai wata magana danakeson muyi.
Gyara zama tayi tace ina jinka Allah yasa muji alheri ..
Murmushi yayi ya ce alheri babba ma....
Ai kuwa cike da zumud'i tace har na qagauta ka fad'an mana
Yauwa dama Maysam ta samu mijin aure ne .
Wani turnikeken bakin ciki taji ya taso mata aman ta danne tace miji ..a ina dan ita jira take taji yace dan shaye2 ne ko kuma wani dan daba ko barawo wanda de Maysam zatasha wuya..
Ai kuwa yace Yarima MURAD dan Sarkin Mustapha me damagaram..
Kasa boye bakin cikinta tayi har seda tace na shiga ukku ni Murza Yarima Fa?dan sarki kake nufifa?se kuwa ta fashe da kukan bakin ciki..
Shi abun ma mamaki ya bashi..be iya cewa komi ba se girgiza kai dayayi a ranshi yace tsanar da take yimata har takai haka?to Allah ya shiryeki inme shiryiwa ce..
Kiraye2 sallah isha'i aka farayi ..Malan Musa bebi ta kanta ba ya fice mosque..
Tana gani fitarshi ta fad'a d'aki Maysam na sallah lokaci se jin saukar dorina tayi nan ta dinga jibgarta harta kaita kasa ..ita kukan azaba ita kukan bakin ciki..
Ta rasa miza tayi se kawai ta kama dantsen Maysam ta gantsara mata cizo har sau ukku har ta fitar mata da fata tace walahi baza ki tab'a auruwa ba ..senayi duk yanda zanyi na hana wannan ma..
Wani sabon kuka ya zo mata ta d'aga hannun da niyar kaymata mari taji Sallamar Malan Musa da sauri tace yi mun shiru munafuka sauran ki gwada wani alamu har malan ya fahimci nayi miki wanin abun (kuji fa keda yau har da cizo)...
Maysam kam kwna kuka tayi da ga bisani ta dauro alwala ta rinda jero nafilfi tana roqon Allah ta mata zab'i na alheri
Murza kuwa kwana tayi tana neman mafita shawara kawai ta yanke taje wurin boka ya hana auren tunda tasan sharri baze yiyu ba tunda sunga irin wahalar da tasha a hannuna..da wannan shawarar ta kwana
Washe gari kuwa tayi waMalan Musa karyar zuwa gidan su ta kuwa fice han se wajen boka ''yankan wuka''
To fa Fans ya kuke gani zata kasance ?Murza zatayi nasarar hana auren nan?
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:31 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:34 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 8 · 0% Book details