← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 67

Sashe 27

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

🅿️ 57__58

```Manzon Allah (SAW) ya ce''ku kawata mazaunanku da yin salati gare ni ,lallai salatinku gareni haske ne a gare ku ranar Alkiyama''
Hakimu ya rawaito shi.```
Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama....
Gaba daya Maysam ta koma bangaren Murad kwana kawai ke kawo ta bangaren fulani....
De temakon bayinta take yin komi ...shi har mamakinta yake dan kuwa yanzu ta koyi komi kama daga shimfidar gado komin girmanshi gyaran daki ,wanki tolet kam ko wata babbar se haka ...
Tare suke shan ruwa suyi buda bakin su tare bayan sallar trawi kuma ta dawo ta tayashi hira ..kai atakaice de sun dan shaku ,,dukda har yanzu sweetbabyn shi na nan makale a zuciyar shi hasalima yanzu ya na jan Maysam jikin shi ne dan tana tsananin kama da ita ko shagwabar ma gani yake iri dayace kai wani zubin mantawa ma yake cewa wai Maysam ce a gabanshi dan jinshi yake kamar yana tare da sweetbaby .......shiyasa ma duk wata mugunta hanttara ya dena mata har Mahmud yana tsokar nar shi dan kuwa kusan duk futar da zeyi tare suke yi da Maysam idan
Kuwa wajen abokanen shine to se ya barta a cikin mota ya kunna mata game ya bata ......
Azumi kam tun tana jin wuyar shi har ta saba yanzu dayake acan garinsu bawani yi take ba Murza bata ma barinta a cewar al'adar qauyen seka fara menstrue ko kuma anyi maka aure sanna zaka fara duk da de ita inde har Malan Musa na gari to kuwa ze tadda ita tayi......
A kwana a tashi ba wuya yau har azumi ya kai biyar ....bayan sallar la'asr Murad ya shigo gaida fulani bayan sun dan taba hira fulani ta kalleshi tace wai ya najika shiru har yanzu ne....
Ya dago kai yana kallonta da alamar tambayta kwance a fuskar sa yace wani abun ne akayi ....
tabe baki Fulani tayi tace kana nufin baka san akan mi nake zance ba?
Cike da shagwaba yace to ni ina zan sani ne ?
Shikenan to zancen kai sucre(sugar)ne gidan sirrin kanka ne a bisa al'adar garin nan idan azumi ya kama to duk wani saurayi ko magidanci zeyi kokari ya kai sucre gidan surikin shi ....
Gyada kai yayi yace shikenan zuwa gobe zan saka akai musu .....
Caraf fulani ta katse shi da fadin kai ya kamata ka kai da kanka dan hakan yana cikin al'adar kuma yana nuna ka mutunta su....
To fa nan ake yinta yayi kicin2 da fuska sannan yace Momy kisan fa bana son futa zuwa wani gari a mota gudun kada....
Daga mishi hannu tayi tace kada ma ka soma ka shirya ai Allah ne me karewa .....idan kanaso kada ka fadawa kowa se Abbanka ....ko Waziri da Dogarai se zuwa safe kawai zaka sanar musu da tafiyan ....
In sha Allah babu abunda ze sameka se alheri kada ka damu Allah yana tare da kai ......muma kuma zamu tayaka da addu'a .....
Shikenan Momy Allah ya shige mana gaba ...
Ameen ta amsa ..nan suka ci gaba da hirar su ...
Har ya tashi ze fice tace kada fa ka manta Maysam gida biyu gareta wato can da nan gidan..
Waro ido yayi yace nan kuma ....
Ee ta amsa ...
To ai momy naga kunada shi isheshe ne mi kuma zakuyi da shi ...
Dariya tayi tace al'adar kenan ..sannan inada tawa tsarabar da zan bayar zuwa safe kafin ka tafi ka turo a dauka......
Dariyar yayi shima yace ok Momy ki kwantar da hankalin ki inde sucre ne se kin ture.....
Yana fita ya kirayi Mahmud yace su hadu yana son ganin shi....
Minti biyar ya dauki Mahmud ya iso ...nan Murad ya sanar mishi da komi.....
Mahmud yace kwarai wannan haka yake. ..yanzu kawai ka bari zanyi wa wani magana zuwa dare se ya kawo.......kamar katon nawa ya kamata muyi oder...
Murad yace kace kawai ya kawo 50. .....se na bawa Momy 25 ...can ma 25 ....ko ya kake gani....
Mahmud yayi dariya yace yayi tunda ko ankai za'a rarrabawa yan uwa da abokanan arziki....
Shikenan kawai kace ya kawo .....
Tun nan yayi kira ya sanar tare da jaddada yau yake son su.....
Bayan sallah isha'i kuwa sega oder da sukayi abangaren Murad aka jibge su .....
Maysam na fenêtre(window)tana kallon ikon Allah tun abun yana bata mamaki har ya dawo bata tsoro.......
Murad kuwa seda ya bari an tashi a fada sannan ya iske mahaifinshi bangarenshi ..nan ya sanar masa da komi ..ba karamin farin ciki yayi ba tare da saka mishi albarka sannan yace da safe a bude magazine a dauko bahun shinkafa 20 ..na makaroni ma haka.........
Godiya yayi kamar shi akayi wa kyautar ..
Yana komawa gida ya tarar da Maysam na tilawa qur'ani dan kuwa tun lokacin da wannan watan ya kama kullum cikin tilawar karatun ta take ...idan yana nan suyi tare ...ko tv sun dena kunnawa sede idan wa'azi ne zasu kalla
Zama yayi shima yana sauraren zazzakar muryarta har wani lumshe ido yake....
Can ta rufe quranin ta kalleshi tace yaya wai wa incan sucre din hala sadaka za'ayi dasu ne...?
Ba tare da ya bude idon shi ba yace na Abbanki ne gobe zan kai mishi ...
Be shiryaba kawai se ji yayi ta haye bisa cinyarshi tare da zagayo hannuta a wuyanshi tace dan Allah zanje ....
Girgiza mata kai yayi alamun a'a ..
E kuwa nan ta fara zuba mishi shagwaba ...
Bude idon dayake ya saukeshi cikin nata tarrrr...wani zut yaji zuciyar tayi da sauri ya rufesu ruf...yace shikenan ki shirya se mu tafi amman fa ki sani in baki fito da wuri ba zan tafiyata ne...
Da sauri ta gyada mishi kai cike da murna ta rungume shi eeee se kayi yayana ina godiya
Kara rumgumeta yayi yace se kinyi yar gidan Momy...nan sukaci gaba da tilawarsu har lokacin rakata bangaren fulani yayi ....
Maysam kam tunda tayi sahur bata koma bacci ba guddin kada ya tafi ya barta...
Lokacin da Madina ta samu labarin wannan tafiyar ba karamun bakin ciki ba dan lokaci ya kure mata bare ta cire musu burki kamar kullum ga Waziri ya juya mata baya....banda kai komo babu abunda take a dakin ...ta jiza yatsa wani zubin ta cije lebe...
A bangaren waziri kuwa koda ya samu labari be wani tada hankalinshi ba dan su yanzu jiran Boka kawai suke yayi aikinshi ...dan ko rakiya beyi musu ba..
Fulani kuwa kamar yanda tace da safe zata bada ta ta gudunmuwar kuwa atamfuna , ,da shadda ,yadina ta bada kala biyar biyar ga Malam Musa da Murza dukda de badan halinta ba taci albarkar watan Ramadan ne...se kuma wasu atamfofin sun kai 20 tace a rabawa matan garin....nan ma Murad ya jerowa fulani godiya kamar shi aka bawa ko kuma dangi shi ......
Maysam se Murna ake yau za'aga Malan Musa ...haka suka kama hanya wacce ta dauke su awa daya da rabi kafin su isa ...
Malam Musa besan da zuwansu ba yana kofar gidanshi se ganin motocin yayi ga yaran garin se ihu suke suna bin motocin...kafin ma su iso ya sheda motocin da sauri yayi tsaye yana jira yaga wanene yazo...
Dogarai suka fara fitowa sunata gyara kimtsi da kyau ......
Mahmud ya fara fitowa se kuma Murad ...yana nan tsayen suka iso da ido Mahmud yayi mishi alamar dasu duka su gayshe shi ...wani kallon bakada wayo Murad yayi mishi...
Shide Mahmud har kasa ya duka yana gaida Malam ganin hakane yasa shima fara dukawa da sauri Malam ya taro shi da fadin a'a ya isa haka ma ya rumgumeshi...nan Malan yace su shigo daga ciki...har ya juya ze shiga yaji an cukuiyeye shi daga baya..juyowar da zeyi yaga Maysam dinshi ce rumgumeta yayi shima yana dariyar farin cikin ganinta itama jitake kamar ta mutu dan murna..
Suna shiga yace ta shiga ta dauko tabarmi a dakinshi...
Biyu sabbi fil ta doko ta shimfida se dariya take ..
Bayan sun zazauna suka sake gaisheshi ..Maysam kam ta wani lafe kusada Malan ...
Can sega Murza tana can yawonta taji labarin zuwan su Maysam aai kuwa ta kamo hanyar dawowa tunda taga motocin tasha jinin jikinta ..dan ita ji take koro Maysam din akayi kamar yanda suka tsara batasan komi waziri ya canzashi...
Tana shigowa idonta ya saukan kan Maysam da inba farin sani kayi mata a da ba to kuwa baza ka ganeta ba.....wani abu taji ya tokare ma ta wuya bata gama wartsakewa ba taga ana jido kayyayeki...mutuwane kawai ya rage mata tayi..a lokacin saboda bakin ciki.
Nan sukayi mishi bayani tare da sakon Fulani dana Sarki..zo kaga murna wajen Malan Musa har rasa inda ze sakasu yayi nan aka sanarwa da me gari...kan kace mi anyi bambami kowa yazo ...haka aka taro a kofar gidankamar wani taron aure dayake ba wani yawane dasu ba haka mazan garin sukayi layi kowa yazo se abashi bahun shimkafa dana makaroni ,suga simkin nan me 5 aciki da turmin atamfa....can na tsinkawo Murtala(da fatan de baku manta shiba)duk ya wani jeme ya manyata saboda wahala..dan kuwa yanzu haka matanshi biyu da yara ukku....layi yazo kanshi can ya tsinkayi Maysam dake kusa da Murad se dariya abunsu suke..wata kwala ta taru a idonshi a ranshi yace yanzufa da Maysam matatace,,,, yace har yaude ina sonki Maysam dita(kuji fa )haka jiki ba kwari ya amsa ya fice yana me dana sani....haka har aka gama me gari ma komi biyu2 ya dauka amman dukda haka komi seda yayi saura har Malan Musa yace asake rarabawa mutane. se Mahmud yace a'a kawai ya rikesu ai daman shi aka kawowa ganin damane yasa ya raba..
Bayan sunyi azahar suka kamo hanya kamin la'asr sun iso ....lfy Lau suka iso
.
Hakade rayauwa tayi ta tafiya yau har azumi saura kwana goma à de de wannan lokacin kuwa Murad ya kai Maysam yayi mata shopping bana wasa ba kama daga atampa..lesh,abaya...etc...iya Murna Maysam tayi tamishi godiya har ya gaji da amsawa ....
Kwatsam ranar ana sallah saura kwana ukku ko hudu shida Maysam suna bangaren Fulani .suna ta hira can de fulani tace waini Murad ya akayi banga kayan sallar Maysam bane? gashi sallah na matsowa kada taje ta rasa dumki...
Sosa kai yayi yace kai Momy duka ma yau ko sati ba'ayi ba nakaita ta shopping kuma fa duka komi na sai mata..
Fulani tace to ai wannan ra'ayin kanka ne ba kayan sallarta ba ne...
Ya gaida kai kawai ..
Tace yauwa kaga ni to... yanzu se ka kaita ta zaba da kanta .
Maysam wacce tun dazu tana jinsu aman batace komi ba se yanzu tace kai Momy a barshi kawai sena bada wanda ya semin din dimkim..
Fulani tace bata san zancen ba ...
Haka ya fito tana biye dashi a baya ,,,,.mota suka shiga..driver be zame ko ina bisa umarnin Murad ba se wurin da ake seda pant da breziya duk dade basu wani fara fitowa ba.. da kuma takalmi da jaka dan dama sune kawai be sai mata ba.... Itade idon wannan shine nan ya biya kudin aka zuba su a leda ya barsu nan dogaren dake kofar supermarché din su suka kwaso kayan aka laftasu a booth.
Bayan sun dayo ne yace to gashi na se miki kayan sallarki yana fadan haka ya fice dan Mahmud ya dameshi fa kira...
Kuyangin ta suka kwaso kayan suka kai bangaren Murad suka zubesu a dakin Maysam na nan bangarennn...
Bayan sun fice ne ta fara duba kayan wata dariya naga tayi se kawai ta musu wuri a inda ya dace...
Love you all irin totaly din nan
Chapter 27 · 0% Book details