← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 67

Sashe 21

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🅿️ 45__46
```Manzon Allah (SAW)ya ce''duniya kurkukun mumini ce kuma aljannar kafiri ce''
Muslim ne ya rawaito shi
```
Kafin su isa tuni har ya sume ...direct emercency a ka shi ga dashi ..
Nan docteurs suka duqufa dan ceto rayuwarshi a bunka da turai kayan aiki birjik dan haka kan kace mi cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo normal ....amma fa idanun sa a rufe da alama bacci yake.....Be farka ba seda ya kwana yayi rabin wuni har wata rama yayi ta kwana daya .......Mark na zaune kusa da shi da yake shi ke jinyarshi ya ga bakin shi ya na dan motsawa kamar me sonyi magana ga kuma idon shi a rufe suke...
Kusanto kunnenshi yayi dede bakin se yaji Murad na ambatan sunan Maysam.... Maysam...
Cike da mamaki Mark ya dago kai yana kallon Murad dake kwance yace Maysam?to ko.....
Kafin ya gama tunanin Murad ya fara bude idanunshi Tar ya bude shi se akan Mark ..yayi karfin halin yin dariya ..
Mark ya kamashi ya kaishi tolet yayi wanka tare da doro alwala ..........yana zuwa ya saka jallabiya ya kabarta sallolin da ake binshi bayan ya gama Mark ya gabatar mishi da abinci ....kadan yaci shima dan ya samu ya kama karfin jikinshi ....
yana tsakada ci . Mark ya kalleshi ya ce .....waccece Maysam ???
Tambayar a bazata tazo mishi dan kuwa har seda ya kware .....
Mark ya tsiyayi ruwa yabashi
Da tarin ya lafa yace Maysam kuma ....''.non je ne la connaît pas ''...(ka ban santa ba)
Mark yayi dariyar gefen baki yace shikenan idan baka santa ba amma ka sani sunan dakayi ta kira kenan ......
Ya mutsa fuska yayi yace nide ban santa ba ..ya kauda fuskar shi...
Mark yace bazan tambayeka abunda ya tado maka ciwon ba amma abunda zance maka kayi gaggawar mallakar ko hakura dashi dan kuwa idan ka bari zuciyar ka ta sake bugawa kamar yanda tayi jiya tofa the best solution se amma ka opération kuma kasan irin ''risque''(hatsari) din dake cikin opération....
Gyad'a kai kawai yayi amma badan ze iyaba dan ko yanzu dayaji sunna ta seda yaji wani zogi a zuciyar shi ....shi yasa tsanar yarinyar yake kara yawa a zuciyarshi.......
kwanan shi ukku aka sake shi ya dawo gida ....ran na hudun ma ya koma aikin shi duk duk dade be wani kama karfin jikinji kamar da ba...
. .
.Abangaren Maysam kuwa karatu take ka'in da na'in ba kama hannu yaro ......dayake kuma ta hadu da masu son karatu Mufeedah da Mariyam ga kuma ilimi ..duk inda bata fahim ta ba suke ganar da ita daya ke su sunyi jss1 ..a duk inda ka gansu to fa zaka tarar suna biya karatun sune na bako ko na arabi........
Akulum kuma Maysam idan ta tuna cewa SANADIN ACCIDENT ne had'uwar su da Fulani har ta samu gatan zuwa école ga islamiyya taci me kyau ta sha me kyau sannan ta saka me kyau ga soyyayar uwa da Fulani ke nuna mata ...se kwai ta fashe da kuka tare yi wa Allah godiya .su Mufeedah de se suyi ta bata baki da hakuri dan su ji suke idan ta tuna rabuwa da yan gida ne take kukan.........
Haka de rayuwa tayi ta tafiya yau da dadi gobe akasin haka inda yau har su Maysam suke zana exam na karshen shekara wato pass to jss1......sun dage karatu suke bana wasa ba ..sati suka jera sunayi se kuma sati me zuwa za'a fada musu résultat se kowa ya tafi gida hutun wata ukku......lfy lau suka gama question din kuma basu bata wahala ba ....tsoran ta daya kada tazo ba ta daya ba saboda har yanzu bata manta da sharadin Murad ba...
A wannan lokacin kuwa Fulani har ta gaji da fadan rashin zuwan Murad tayi fadan tayi fushin ta gaji kullum maganarshi daya ce cewa zezo .....kai daga baya in ta kirashi da sun gaisa seyace mata yana dakin tiyata ko kuma aikin sun mishi yawa ze kirata da ga baya kuma ba kiran zeyi ba..tun abun baya damunta har yazo yanayi....se de kawai ta bishi da addu'a..
Shima anashi bangaren yana so yazo dan yayi missing dinsu barema Maysam zuciyarsa na matukar son ganinta amma besan miyasa baya son dawowa garin ba ba .....gashi har yau zuciyar na mishi zogi lokaci zuwa lokaci......
. .
A bangaren Waziri kuwa duk ya bi ya fige ya rame saboda diyar shi MAHEEBATOU dake cikin mawuyacin halin sakamakon kama mahaifinta wato waziri cewa da sa hannushi akayi wa Murad asiri ya bar kasar ita kuma tunda ta taso ta mallaki hankalin kanta bata da wani buri da ya huce ta ganta a garakal mulki tanayin yanda taso kamar Madina dukda de tanada kuyangi har biyu amma ita tafi so ace gaba daya masarautar a hannunta take........lokacin kuwa hanya daya take ganin zata bi ta cika burinta hanyar kuwa itace ta auri Murad idan sarki ya mutu tana da yakinin yarima Murad shi ze gaje shi tunda shi kade ne danshi na miji ...
Mahaifinta waziri ya daure mata gidin se abunda take so takeyi kasancewar ita daya Allah ya bashi bayan shekara da shekaru da yin aure shi yasa ya dauki karan so ya dora mata .duk abunda zatayi baya ganin laifinta ....koda ta sameshi ta sanar mishi burinta se ya goya mata baya ...a lokacin ya samu me martaba da yanaso akara hada zumunci wato a hada yarima Murad da diyarshi Maheeba aure ...
Sarki ya sa aka kira Murad a lokacin sannan ya sanar masa idan har yana da ra ayin aurenta ..
Bude bakin Murad yace a'aaa kiri2 yace shi baya sonta ...wannan magana tayi matukar batawa waziri rai amman ya danne zuciyarshi...
Koda ya sanarwa da diyarshi yanda sukayi se kawai ta fashe mishi da kuka har dasu birgima ..... .....duk da haka seta fara shigewa tana nuna mishi so ...shi kuwa Murad be masan tana yiba duk inda yayi se taje ........ganin haka yasa ya tattara ya koma England da zama bayan ya sha fama da fulani.....
Wannan tafiyar tashi gaba daya Maheebatou ta fice a hanyacinta dan a rayuwarta ba a saba ce mata a'aa ba dole tasa waziri ya turata kasar Mali karatu wajen dangi mahaiyarta da alkawarin idan ta dawo ze cika mata burinta .....
To fa ranar da tazo ne ta riski Maihaifinta na zancen asirin shida mahaifiyarta ...tun lokacin ba agane mata ba ..dan dama saboda cikar burinta ta dawo....
Ganin abun bana qarewa bane Waziri ya wanke kafarshi ya tafi ya sanarwa Madina halin dayake ciki ..amma Madina fir ta kiya ..babu irin rokon da beyi mata ba kan a karya asirin Murad ya dawo daga baya a san yanda za'ayi aman tace bata san zancen ba ..
Rai a bace ya fito kamar wanda zetashi sama a ranshi yace baki san ko biye miki danake saboda Maheeba bane dan na samu na zama sarki sena barta ta taka wanda take so...
Haka ya isa gida yanata banbami amman mi abunda ya tarar ya kara daga mishi hankali dan kuwa Maheeba numpashinta ya dawo sama2...
Ba shiri ya fita ya kama hanyan se wurin BOKA gobe da nisa ...
Makuddan kudi ya zube mishi nan yace yana son a karya asirin Murad ya dawo gida kuma idan ya dawo kawai a daura aurenshi da diyarshi Muheeba...
to fa fans kunji wata kuma.....
Shin ya luke ganin zata kaya ne?
Fasma ce
Ahmed Gumel
[9/2, 9:49 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 9:50 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 21 · 0% Book details