← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 67

Sashe 3

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🅿️ 07__08
```Mazon Allah (SAW) yace''lallai mamaci anayi masa azaba saboda kukan masu rai''
Ruwayar Bukhari da Muslim ce```
Washe gari da matse nanci ciwo kai ta tashi saboda kikan datayi dayake babu school tayi shara da wanke2 gidan tana kiciniyar d'ora break Malam da Murza suka fito da alama tafiyar kasuwancin shi zashi bata san lokacin da hawaye suka zubo mata a ranta tace yau kuma ko wata azabar zansha ....nan ya bawa Murza kud'in cefane ita kuwa Maysam dari biyar ya bata tunda yanzu ba school ..ko fita daga gidan beyiba Inna Murza ta kwace kud'i tayi shigewarta d'aki ashe Malam Musa ya gani dan yayi mantuwa ya dawo ....bece komi ba ya d'auki abunda ya manta ya sake yiwa Murza sallama sekuma yace Maysam ta biyoshi ze aiketa wani gu......Murza bata kawo komi a ranta ba..
Bayan sun fita ya kalleta yace yar Abba ki zanki hakuri da Innarki wata rana se labari ki qara hakuri da ita kinji ko...ina sane daduk abunda take miki dan qawarki Ma'u tana sanar dani komi yayi zafi maganinshi Allah dan baze yuyu na dinga tafiya dakene ba ..
Wani hawaye taji ya zubo mata magana ma kasayi tayi se gyad'a kai kawai ta iya'yi ...
Share mata hawayen yayi ya rumgumeta yana lallashi har ta fasa kukan ..ya ciro dubu biyu ya bata yace ki sayi duk abunda kike so kada ki bari innarki ta gani bare har ta kwace miki kinji kuma daga yanzu zan ringa baki kud'in da zakina kashewa ...
To tace Abba na gode Allah ya kara bud'i ya bada sa'ar abunda aka tafi nema...
Sosai yaji dadi addu'ar yace ameen yar Abba Allah ya albarkaci rayuwarki....
Ameen tace ..
Nan ya tafi ya barta tana d'aga mishi hannu har ya bace ganinta...a bakin zaninta ta kulle kudin ta koma gida...
Tana shiga taga inna da tulu a hannunta tasan mi hakan yake nufi dan haka da duka da niyar karb'ar tulun ai kuwa ta daka mata duddu tace shegiya annamimiya har da wani kukan munafurci dan Malan yayi zaton ina cin zarafin ki in bayanan ko.....
Itade batace mata komi ba ..
Dungura mata tulun tayi tace saura kitsaya inda kika saba tsayawa .....
Biyawa Ma'u tayi sukatafi tare ..a hanyarsu ta dawo ne suka gamu da Murtala shida abokanan shashacin shi....
Nan suka taresu har sun tatare zanin su zasu arce Murtala yace wly in kuka gudu kun jawowa kanku ..cak suka tsaya ...
Ya matso daf da Maysam yace matana ya kike ...kin san banso kina daukan ruwan nan bara natayaki ..yayi niyar sauke tulu daga kanta nan taja baya da sauri ..ma'u tace wai miye hakane kun wanizo kun tsare mu a hanya har kana wani kiranta da matarka kota ina ma...
Daka mata tsawa yayi yace ke kuwa asuwa ...kinci darajar kece yarinyar da abokina ze aura wly da yanzu na keta miki haddi...tsit kake ji Ma'u tayi...
Suka kwashe da wata arniyar dariya ya sake matsowa daf da Maysam wadda ita alokacin tuni hawaye keta zuba....yace haba tawan nan yasa hannu ya share mata hawaye se kuma yayi niyar rumgumeta wai azuwan lallashi ..
Efa nan ake yinta nan kokowa ta barke har rigarta ta cire daga gefen ai bata san lokacin da yarda tulun anan ta arce a 60.....zasu mara mata baya Murtala yace a'a ku barta ku muje idan zamu kawai ....
Seda ta isa kofar gidan su tukon ta tsaya duk jikinta karkarwa yake ...se kuma ta sake fashewa da kuka ...ga abunda Murtala yaso yimata ga kuma tulun Inna ya fashe wanda jiya2 nan ta sayeshi ta jima nan tsaya sannan ta shiga gidan se rarab'ewa take..
Inna na ganinta ba tulu tayi dariyar mugunta dan ta fad'i gassasa yau....
Game hanunta tayi tace dan Allah inna kada ki dokeni walahi su Murtala ne nan ta kwashe yanda sukayi ta fad'i mata..
Wani ashar tayi ta rarumo icce ta fara buga mata tace kicede yau asirinku ya tunu keda shii wurin gudu kika barar mun da tulun ga sheda nan harda cirewar riga ..dukan ta take baji ba gani ai kuwa dubu biyun da Malan ya bata ta fad'i kasa ..
Salati Murza ta shiga yi tace munafuka asirinki ya tunu ashe karuwancin naki me degree ne harda dubu biyu ...nan ta dauke kudin ..ta d'ago fuskarta za zazzabga mata mari ta kuma sa hannun a kwalmin idon ta dunga kyarkyarta saman idon har seda taga jini yana fita tace shegiya me kama da mayu wata ran sena fidda miki idon nan kowama ya huta ..sanan ta cigaba da duka har seda taga bata motsi tajata ta yar a tsayar rana..lokacin kiwo nayi ta sheka mata ruwa ta tashi tace maza tashi ki fice kiwo..
Tasan kotace zatayi sallah baza ta barta ba setace Inna abincin nafa?
Abinci fa ai kedashi se gobe kuma tunda yau kinyi kari ...
Haka ta fita gwani ban tausayi...
Haka rayuwa tayi ta tafiya wanda kullum se Murza ta caje Maysam inde harta fita ...ga kuma takurar da Murtala ke mata kullum inde sa had'u to seya nemi tab'a jikinta...shiyasama bayan anyi auren Ma'u ta sati ta gayawa Malan itama gwara asaka nata auren dan saboda tsaro..
Haka kuwa akayi nan aka saka ranar goma ga sabon wata kenan nanda kwana goma...
Iya tashin hankali Murza tashiga dan ga dukka alamu auren nan ba fashi gashi kuma da gani yarinyar zata huta idan ta auri d'an megari tunda ko kayen lefenta ya kere na kowace budurwa nanfa ta fara shige da fice ta ciru ta kullu dan ganin auren ya fasu ..
Nan ta wanke qafa taje gidan me gari har d'akin uwar Murtala ta shiga dayake sunsa sirukarsuce sesuka mata tarba ta kirki ......bayan gaishe2 tace dama wata magana ce take tafe dani...
Uwar Murtala ta gayra zama tace ina sauraronki..
Nan ina ta tsara karya da gaskiya ta fad'i mata wanda harda cewa ai yarinyar bin maza take yanda kasan kariya haka take bin maza ....
Inna Murtala tayi jim ...can tace shikenan barin zan sanar dashi Murtala kinsan yaran yanzu se abunda suka sa gaba sukeyi....
Nan ta kakab'e zane ta fito...dede kwanar gidan ta gamu da Murtala ..nan ya gaydata gatse2 bata wani damuba tace yauwa d'an albarka daman akwai maganar dana keson muyi ......
yace to ki fad'a kawai danni sauri nake..
Yauwa dama ba wani abu bane gayamaka ne zanyi kasan de yarinyar nan karuwace ko...?.
Ta 'aza zeyi mamaki seta ga ko aka sema cemata yayi toni ina ruwana...
A ranta tace kaji shegen yaro amma inkasan wata bakasan wataba..tace ai ba wanna ne matsala taba ai yarinyar tana d'auke da cutar nan me kashe garkuwar jiki ...
Wani uban ashar yayi yace ni za'a cuta a had'ani dame kanjamau...wly da sake..
Murza tayi wata dariyar cin nasara tace ai shi yasa nace gwara na fad'a maka tun wurin amma ka bari se ana jibi auren sekace ka fasa ..
To kawai yace ya fice se banbami yake..
Zuciyarta fari tas ta tafi gida...
Hakan kuwa akayi ana jibi d'aurin aure Murtala yace shifa ya fasa auren inkuwa har aka d'aura auren to a ranar ze saketa...nanfa yayi d'an jinjinb'in haukanshi har seda yaga an fasa zancen ...
Maysam tayi farin cikin wanan abu dudda batasan miyasa yace ya fasa auren ba..shima Malan da fari abun ya b'ata mishi rai aman gani Maysam bata damuba yasa shima jin saukin abun
Bayan sati da faruwar hakan ta dawo daga rafi taga su Murtala ...abin mamaki seta ga suna gudunta sab'anin da daze dunga famar fa'damata....daga d'an nesa da'ita suka tsaya Murtala yace karuwa Allah ya toni asirinki ashe kina dauke da cutar HIV kikaso na aureki danki gogan ko ..to ta Allah bata kiba...
Nuna kanta tayi tace ni kuma...
Kwarai ke Maysam har gida Innarki ta iskeni ta gayamun...
Batace komi tayi ficewarta..
Ranar kwana tayi tana kuka bata san mita tsarewa Murza a rayuwa da bataso taga farin cikinta...
haka rayuwa tayi ta tafiya inda yanzu har takai 13 years aman ba me zuwa wurinta da sunan saurayinta koda kuwa yazo to baya sake dawowa inkuwa kaga har ansa ranar aurenta to fa baqone shima kuma da zarar yaji labari zakaga ya d'auke kafarshi..anyi haka yafi sau biyar..dan haka ta daina sauraron duk wanda yazo mata da sunan saurayi
duniya tayi mata zafi ga wata rama data 'karayi ga jaraba da wahalar Murza kullum qara gaba ke..duk gari ya d'auka karuwace kowa gudunta yake wurin Qawarta Ma'u kawai take samun sauki se kuma Malan..
..shima Malan tausayin yarshi yake gashi babu damar ya tashiga cikin mutane ..dan zakaga mutane nata nunashi abunka da karamin gari...
Duk cikinsu Murza ce kawai wanen abun yayiwa dadi dan karenta takeci babbabaka..mugunta duka muzguna kuwa da ana sabo dasu da yanzu Maysam ta saba
Murza ayide a hankali duniya ce...
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:11 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:13 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 3 · 0% Book details