← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 67

Sashe 60

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar ma akayi decharge din su direct dakinta na bangaren Fulani ta koma dan acewarta mutumin da bayason jin muryarka ma to ai in ya ganga abun se yafi haka ..dan haka ta kudurta zata bashi space kamar yanda ya bukata ..kuma bazata kara nemanshi ba inde har bashine yazo da kanshi ba......ta sani ya kwallafa rai akan cikin nan to aman ai ya dace yayi bincike kafin ya yanke hukunci . ita aganin ta koshi ai be kaita san cikin nan ba ..dan babu wanda ya kai uwa son danta se mahalici mu ..to wai ma tayaya ze ce wai ita tasha magani zubar da ciki ..wata zuciyar tace ai dan kin nuna tun farko bakyaso ..badan haka ba ai da baze zarge ki ba..haka de tayi ta tunanin ta..

A bangarenshi kuwa se bayan yayi abun yayi nadama ..ai ko ba komi wifyn shi ce ..ya kamata yayi mata uzuri sannan ya lallabe ta ko zata gaya mishi miyasa ta aikata hakan ..se kuma wata zuciyar tace batada wani hujja .kawai dan ta bata maka rai ne.....

Se kuma dayar zuciyar tace to ai rabin zuciyarka ce kaga yanzu kasakata kuka may be ma tana can tana yinshi . ..ai da sauri ya juya ze koma se kuma ya tuna maganar Momy cike da sanyi jiki ya koma cikin masarautar..

🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹

A bangaren Murza kam ba karamar murna tayi ba da taga anyi likita da Maysam dan tana labe daman .Allah2 take taji labarin barewar cikin aman setaji akasin hakan..ranta yayi mugun baci aman kuma data ga yanda Murad din ranshi ya bace se ta danji dadi2 acewarta kafin su shirya zata hada wani target din ta zubar dashi gaba daya ..inya so se ya koro ta....tun nan ta shiga tsara yanda zatayi. .

Dan munafinci so biyu tana zuwa duba Maysam da tana likitar kuma tunda aka sako su kullum.setaje .

🌹🌹🌹. 🌹🌹

Malam Musa kam da me martaba basu san wainar da ake toyawa ba ande cemusu bata ji dadi bane..kjma sun mata ya jiki
...

Bayan sati da faruwar hakan Murad yaji baze iya jure rashin Maysam kusa da shi ba....duk ya fara dan ramewa dan bawani abinci kirki yake ciba dan ya saba da nata se yake jin wannan din bashida tast...dukda kuyangi na gyara mishi bangaren aman ba kamar yanda wifyn shi keyi ba .. dan kuwa ko tsohon cikin ta baya hanata gyara bangaren tsaf ..shi kanshi ya san yayi dace da sa'ar mata ...dan haka yau tun safe wurin Fulani yaje .yayi ta bata hakuri kan sharin shedan ne hakan bazata sake faruwa ba ..sannan ya bukaci data bashi matarshi..

Fulani tayi murmushi ..tace har ka gama fushin damu kenan ....to nide bakayi mun komi ba kaje ka bawa matarka hakuri sanan intace zata koma dakinta to ni mi nawa a ciki ..kajede ka lallasheta kawai..nan tayi mishi yar nasihohi

Cike da kwarin guiwa ya nufi part din ..lokacin tana tolet ..zama a bakin gadon yayi yana jiranta ..

Tana fitowa taganshi ai kafin yayi wani yunkuri ta koma ta datse kofar ....nan ya shiga kiranta ta bude mishi aman yanda kasan bada ita yake ba..haka ya gaji ya fita..

Murad be san abun nayi ne ba seda yaga ya shafe wata guda harda kwana ishirin Maysam taki kulashi kai rabon daya ganta ma har ya manta dan bata fitowa. Se yabar bangaren ..har karar ta yakai wajen sarki ..wata rana da dare suna hirar su shida fulani kamar kullum ya shigo bayan ya kwashi gaisuwa ne ...yake gayawa sarki shi fa ya a meda mishi matarshi ..

Sarki ya kalli fulani da alamar tambaya ..wayen cewatayi da fadin mistake ne suka samu a tsakanin su ita kuma tayi fushi ta dawo bangarena ..ta kalleshi tace ko ni na rike maka mata ne..

Ya sadda kai tare da girgizawa..
Murmushi sarki yayi irin nasu na manya yace to kai son kawai kaje ka lallabeta mana..kasan su mata seda da lallaba

Yace Dady nayi fa taki hakura kawai kasa baki ta koma..

Sarki yace bazan tirsasata ba itama ya ce kuma bansan mi ya hadaku ba ..kuma ma ai ba'a gajiya da lallaba mace ..kaci gaba da rarrashin ta zata sauko bare ma su mata akwai su da tausayi da raunin zuciua....yayi kasa da murya yanda Fulani bazata jiyo ba yace bari na gaya maka wani secret irin na mu na maza yanda zaka shawo kanta cikin sauki ..

Kasa2 sosai yake mishi maganar wanda ni kaina banjiyo ba . nade ga Murad na wani sunne kai irin na inkaji kunyar nan ..yana kuma murmushi kasa2..

Fulani kam kallosu kawaitake cike da birgewa ..

Yana gama fada mishi ya mike ya fice har ya kai kofar futa Sarki yace kada kaji komi zanji da tanan din ..wuf ya fita a palon dan yau dadyn nashi ba karamar mamaki ya bashi ba ..daman tsofi ma sun iya soyyaya haka..(ni kuwa nace zauna de nan ai fulani da sarki se a hankali dan ko kallon juna suke zaka iya hango tsantsar kaunar da sukewa juna..😝..)..

Direct bangaren fulani ya fice ...lokacin Maysam zat shiga dakinta ..

Be bari ta ganshi ba ..tana shiga direct tolet tayi ..shima kuma wuf ya shigo dakin ..ya saka key ya kulle....dede kofar tolet din ya labe bayan labule dan kada ta ganshi ta koma.....

Tana fitowa ya shaki kamshin turarenshi ....har wani lumshe ido tayi dan tayi bala'i missing din turaren ...batayi zato ba taji an rumgumeta ta baya ...ta kuwa bate baki zata yi ihu da sauri ya rufe mata baki tare da fadin nine mijinki ..

Ai kuwa ta shiga kiciniuar kwace kanta. ...

Ganin haka yasa ya sake ta dan kada taji ciwo...tana kallon shi kallonirin na mi kake yi mun a daki ...

Kalar tausayi yayi yace.

To nima de nace Happy sallah my fans..
Love you all❤❤😍

Barka da sallah ..
Bonne fete de tabaski a tous❤❤😍

Fassouma ce🖊(yar mutan zinder)
[9/14, 9:13 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/14, 9:14 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

*Ina me bawa masoyan wannan littafin hakuri na rashin jina da kukayi hakan da farune sakamakon exam da aayi satin daya huce ..am so sorry na rashin jina kwana biyun nan shiyasa ma zan cire labarin na rage shi dan nayi na gama dan koni kaina bana jin dadin yanda bana typing kullum.....*

*Wanda suka yi kirana da wanda suka mun text na gode Allah ya qara dankon zumunci .. Wanda kuma bansamu damar dauka ba ina me baku hakuri kun sani ina yin ku irin more totaly din* *nan* 😍😍😘❤❤

*Yan kungiyar mu ina alfahari da ku ina godiya da irin karfin guiwar da kuke bani Allah ya qara hada kanmu .ina yinku gaba da baya* ❤😍😘

_I miss you a lot my in law Xaynap queen keda my Arfat da kuma Momun Mufeedah Allah yasa kuna cikin koshin lafiya.._

Dedicated to all my fans😍❤ _special my zee'' Xaynab Idris ''ba shaharariya marubuciya ..kada ku bari abaku labarin littafinta dan akwai fadakarwa tare da annashuwa da ilimantarwa (kuneme shi me sunan RAYUWAR FADILA)Allah ya barmin ke_ 😘😍❤

🅿109__110

```Manzon Allah (SAW) ya ce''za a tayar da mutum akan abinda ya mutu a kai(gobe kiyama)''
Muslim ne ya rawaito shi```

[06/09/18 à 00:10]
Kalar tausayi yayi yace haba my lovely wife ..am.so sorry nasan banyi dedeba aman hakan bazata kara faruwa ba..ni kaina bansa don mi nayi miki haka ..aman ga fuska ta ki rama marinki ko zaki huce dan na gaji da fushin nan ..

..yi tayi da daya duniya bada ita yake ba ..dan ko kallonshi bata kumayi ba ..se ma ya yan wake2n ta ma take ...

Kara matsowa yayi kusan ta ya rike mata hannu kamar zeyi mata kuka yace kiji tausayi na ciwona na gab da tashi . .ya aza hannunta bisa zuciyarshi yace ji kiji yanda take bugawa ..pls ki mun ko magana ne ko naji sassauci akan abunda nakeji ..kin sani zuciyata bazata juri rashinki ba...nayi nadama kuma lokacin idona ya rufe ne ...

Se lokacin ta dan kallo shi ..aman batayi magana ba ..setaga har ya rame kamar yanda ta rame itama ..gaba daya tausayinshi ya mamaye ta .,.jitake kamar ta rungumeshi aman se taga kamar tayi saukin saukowa ..baride ta nan kara garashi dan ko gobe kada ya kuma yi mata haka

Dan haka bata ce komi ba ta bi lafiyar gado ma....

Yajima nan yana bata hakuri sanan ya tashi ze fice ganin ko kalloshi ta dena yi....
Dafe zuciyar yayi dan wani irin zut4 take mishi😝 ....har wani layi yakeyi kamar wanda yasa wani abu dan dishi2 ma yake gani.....

Yana gab ta fita yaji Maysam ta rumgumeshi ta baya

A tare suka sauke ajiyar zuciya ...Rikeshi tayi tsaf kamar wanda akace za'a kwace mata shi ....

Da kyar ya jiyo da ita face dinshi ..sun kusan minti biyar suna kallon juna kowa yana kokarin aikawa da dan uwanshi sako ta kwayar ido..

Can Murad ya bude baki zeyi magana da sauri ta sa hannunta ta rufe mishi bakin tace ya isa haka ..nima am sorry da yanda na shareka ..ta kai hannuta wuyanshi tace duba min wanan rama da kayi kamar wanda baka cin abinci ....

Dan murmushi yayi yace to ai kece abincin nawa..ganin ki kade ma kosar dani yake ...
Chapter 60 · 0% Book details