← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 67

Sashe 62

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maysam tace am sorry nima basan haka abun yake ba da ban yi korafi akai ba...ko kadan banji haushiba se ma dadi dana ji cewa inada suna iri daya da Sweetbaby ..ina sonta nima duk da bantaba ganin taba aman ta shiga raina nima ..Allah yaji kanta...Allah kuma ya kara ma hakurin rashinta babyna....

Ko yanzu seda ya lumshe ido dayaji ta kira sunan.

Ai kafin ya bude Maysam tayi kissing din idon tace ''so handsome''..ina sonka dayawa mijina...

Bayan ya bude idon yana murmushin jin dadi yace i love you more MAYSAM..

tab ai jitayi gaba daya duk duniya yafi kowa iya fadin sunan har wani ruwa2 taji a sunan lokaci da ya fadi..wata irin ajiyar zuciya tayi tare da lumshe ido dan sunan ya shigeta ba kadan ba...jitayi kamar ma shi ya kirkiro sunan(ni kuwa nace kika sani ko shi din ne ma)

Lakice mata hanci yayi yace to waima ke miye sunanki na gaskene dan Maysam ba suna bane fa..ke kuwa naga har cikin takardunki haka a kasa...

Zatyi magana wayarshi tayi kara ganin sarki ne yasa ya daga...yana ajewa ya zame daga jikinta yace dady ne ke kirana kiran gaggawa kissing dinta yayi ya fice da dan sauri2...

Ita kam tagumi tayi tana tuna magagan nun su na yanzu ....

🌹🌹🌹🌹 🌹🌹🌹🌹a gurguje pls

Abude yazo dan gobe ne birtday dinMaysam da tsohon ciki se shiga da fice ake dan ma fulani na tilasta mata hutu ..su Mufeedah da Maryam ma sun zo suna ta murnar ganin juna. ..kowacen su kuwa da dan karamin cikinta....

Awani hall na cikin masarautar za'ayi ...

Bayan sallar isha'i Maysam na bangagarenta se dube2 take da alama de wani abun take nema
..can kasan wasu kaya ta hango kayanta da Malam Musa yace da su ya tsince ta....

Tana kallon kayan ta ce ko yanzu ina mahaifana suke ?mi nayi musu suka rabu dani?to ko da gaske ni shegiyar ce kamar yanda inna Murza ke fadi ?..tana daga kayan Zoben nan ya fado ...cike da murna ta dauko ta saka a hannunta tace ashe nan na boyeka muka sha wuyar dubaka..cuwat ta mike tana fadin bari na kira babyna na sanar mishi...

Wayarta a palo ta fito ta dauka ..kira na daya na biyu ya daga cikime da jin dadi suka shiga hirar su ta masoya Maysam tace wai kana ina ne kaga wani abu ?

Yace gamu dawo wa daga tarben su Mom. ...to miye za'a gwada min ..

Maysam tace devine quoi?

Seda yayi yar dariya yace to waya cemiki ana fadin gift din dazakayi bawa mutum ai seki bari har zuwa gobe tukon ko..

Dariyar tayi tace to waya fada maka gift dinka ne zan fadama ..

To in bashi bane minene?

Tace yanzun nan ina duba wani abu na ga Zoben nan dana taba baka labari gashi nan ma a hannuna in fadama maka ....

Wata irin faduwar gaba yaji yace gani nan zuwa yanzu in gani kada ki fidashi daga yatsarki ...

Zatayi magana taga shigiwar Murza palon fuskar nan ba annuri kamar kullum ..

Murza tace shigen ciki me taurin kan tsiya irin na ubanka da uwarka ..ashe kananan baka zube duk irin maganin dana baka ...to ai yau gani nan da kai na yau me rabani da kai se Allah..
Itade Maysam cike da tsoro take kallonta kuma tana jin irin maganganun da Murza keyi suka dada tada mata hankali ..Murad de yana jin magana kasa2 aman bayajin abunda ake cewa ...yana ta kira Maysam3 aman ba amsa ..

Ita kuwa Maysam ganin Murza ta tunkarota ta wata wuka tana fadin yau sena kaiki lahira dake da shegen cikin nan yasa ta kwalla wani uban ihu kan kace mi tuni ta zube nan kasa sumamiya (nasande baku matan da yanda Maysam ke tsoron Murza ba)gashi kuma babu bayi duk Murad ya koresu

Jin irin ihun da tayi yasa hankalinshi ya dada tashi gashi kuma da dan tazara kafin su iso ...ya sake kira yaji sweet off

Dan haka ya kira Mahmud ya sanar mishi daya je bangarenshi ya duba mishi Maysam yayi sauri ...

Dayake yana cikin masarautar dan haka da sasarfa ya fice part din..
Yana shigowa lokaci Murza ta kaiwa cinkin Maysam Halbi da kafa ta daga zata kara Mahmud yayi kukan kura ya damki kafar ya cillar da ita can....kafar me lafiya ta bugu da wani karfe kuma kanta ma ya bugu da da wani da center table a take ta sume...

Tana sumewa nima nace bari nayi nan .....

Se mun hanu a next page wanda nake sa ran last page ne.......ina sonku irin dayawan nan kuma ina kara baku hakuri ...❤❤❤❤❤❤😍😍😍😍😘😘😘😘

Nice de taku har kullum

Fassouma ce🖊(yar mutan Zinder)
[9/14, 9:14 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/14, 9:24 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

*Sakon gaisuwa dubun godiya da kuma ban girma zuwa ga yan groups din*
ZURI'ARMU FANS2
MEERAH FANS GROUP
UWAR RIKO FANS
KALAR TAWA UWAR FANS
SALMA FANS
NOVEL CAT BY YA-YUSUF
SURBAJO FANS
HAUSA NOVELS
RAYUWATA FANS NOVEL
PLM TRUE LOVLY FANS
GENTLE LADIES HAUSA NOVEL
FATIMA (AS)HAUSA NOVEL
NISA'UL KHAIR
DON AMARIYAR SATIN NAN
BRILLANT NOVEL FANS
NOVELS LIBRARY
ANSHOLLY NOVEL
M.HAUSA NOVEL
AYSH NOVEL
HAUSA NOVEL AYAU
004HAUSA NOVEL BOOK
FANS NOVELS ..
🤣🤣 *kai walahi kuna da yawa fa kuyi hakuri wanda ban ambata ba kusan kuna raina kuma ina yin ku irin more completly totaly din dan ❤😍😘😘* 😘😘

Dedicated to all my fans😍❤😍😍❤❤

🅿111__112
( _First of last page_ )

```Manzon Allah (SAW) yace''marowaci ba zai shiga Aljannah ba ,haka ma mai mako.''
Al-Khatib ya rawaito shi``` .

'' _Dayawa suna korafin sunan Sweetbaby to sunanta MUNIRA ....kuma Maysam yana nufin SWEET,Murad ma yanada nashi ma'anar ..zaku gane komi a last page'''..and kuma ai in kun lura kaf tunda littafi ya fara sunan mutanen_ _cikin yana farawa da 'M'' ne yake kamar su Ma'u,Murtala ,Murza,Musa etc..so ku bini zaku gane don mi na zabi sunan MUNIRA .. Thankx da tambayoyin ku_ .. _dan wanan yana mun nuni da kuna bibiyar book din_ 😍❤❤😘😘

[09/09/18 à 23:31] Mahmud kam gashi likita aman ya rasa irin temakon da ze bata ..kira yayi aka turo nurse din cikin asibitin masarautar..haka de da kyar kafin su iso ya dedeta nutsuwarshi ya shiga neman ceto ta ..ya jima kafin numfashinta ya dawo ..cikin ikon Allah kuwa tana farfadowa nurse din suna shigowa sede mi jini ya ballewa Maysam kamar mi..da sauri akayi emergency da ita kusan kaf doctororin masu fanin haihuwa wato gyneco da kuma sage femme dake asibitin suka shiga dan ceto rayuwarta...

Abunka da gidan sarauta kafin ma Mahmud ya sanar da su fulani tuni labari ya isar musu
Kan kace mi tuni fulani ta iso asibitin ganin Mahmud na kai komo yasa hankalinta kara tashi ..ta iso tana tambayarshi abunda ya faru..nan ya sanar mata tundaga kiran Murad har bugon da Murza tayiwa cikin. Nan ta shiga fadin inna lillahi wa inna ileyhi raji'un tare dayin salati ....se kuma ta bada oder da atafi a kama Murza a kai a kulleta kafin ta kudu ...

A bangaren Murad kam hankalin shi ba karamin tashi yayi ba jin faduwar wayar Mom da suke tare itake tausarshi tana bashi baki kan babu abunda ze sameta ...gudu yasa aka kara dan duk iya hakurinshi ya kasa gashi in ya kira Mahmud din ma baya daga wa ......

Lokacin daya iso direct bangarenshi ya nufa dan yana da yakinin nan ze tarar da ita huyangi nayi mishi bayanin aman be masan abunda suke fada ba shide fatanshi ya saka wifyn shi a ido ..

Ai kuwa abunda ya gani ne ya qara daga mishi hankali dan jini ne kamar wanda aka yanka kaza a tsakar falon ...ga kuma wasu kuyangi suna aikin gyaran gurin ..

Nan suka zube suna gaishe shi aman ko takan gaisuwar bebi ba ya shiga tambayar su ina Maysam ...kasa magana sukayi dan suna tsoron hukuncin daze musu inyaji wanan abun ta bakin su..

Wata tsawa ya daka musu ai ba shiri daya daga cikin su ta shiga yi mishi bayani kan sude sunga an fice da ita asibitin nan kuma tana zubar da jini ..

Be ma bari sun karasa ba ya fice se asibitin su Mom dake bayan shi suma suka mara mishi baya duk da ita ba wani dadin jikinta take ji .....

Tun daga nesa ya tsinkayi su Mahmud harda gudu2 ya hada dan shi yama manta da shi yarima ne bare ya tuna da wata sarauta har ya kai ga tuna da bayi a gurin ....

Ganin yanayin su fulani yasa jikinshi yin sanyi ko ba 'a fada ba yasan wifyn shi ce ba lafiya..da kyar ya hada miyan bakin shi yace Momy ina Wify ta ?miya sameta ?

Fulani kam ta rasa ta inda zata fara mishi bayani..se Mahmud ne yayi karfin halin rumgumeshi yana mishi nasiha kasa2 kan yayi hakuri da komi na rayuwa sanan ya sanar mishi yanda abun ya kasance ..beyi aune ba yaji lema a kumatunshi koda ya shafa yaga ashe hawayene yake Mahmud ya kalleshi yace pls kayi hakuri ai ba ancemaka ta mutu bane addu'ar ka take bukata kuka baze anfane da komi ba...

Kara rumgume Mahmud yayi yace baka ji yanda zuciyana ke mun bane jinake kamar zata faso kirjini idan na rasata nima na tabbatar da binta zanyi ...

Mahmud yana dan bunbuga bayanshi alamun lallashi yace ka rumgumi kaddara kamar ba musulmi ba ...haka kayi lokacin sweetbaby har ka kusa halaka kanka ..pls ka meka lamuran ka wurin Allah komi se ya zo maka cikin sauki. . ...fulani da Mom ma suka matso suna bashi baki tare da nasiha har yaji zuciyarshi ta fara dan saki bisa kulewar da tayi ...

Nan kuma ya tada rigimar seya shiga ..babu muso suka barshi ya shiga ..ai kam seda yayi dana sani dan ganin irin bakar wahalar da Maysam ke sha ....
Chapter 62 · 0% Book details