← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 67

Sashe 28

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*FASMA* *Ashe haka masoyan wannan book din kukeda yawa haka...kai amma naji dadi ina alfahari daku alherin Allah ya kaimuku a duk inda kuke wa inda na sani da wa inda ma ban sansu ba ... Allah ya bar kauna ya kara dankon zumunci...ina yinku irin sosai din nan ...* Dedicated to all my fans 59__60 ```Manzon Allah(SAW) ya ce''ka bar duk abinda kaga ya shiga maka duhu ,ka kama abinda yake warai a wajenka Tirmizi ya rawaito shi.``` Bayan sun fice ne ta fara duba kayan wata dariya naga tayi se kawai ta musu wuri a inda ya dace... Yau da gobe se Allah yau har daren sallah gaba daya Maysam ta sauyawa bangaren Murad sanffari ..ta juya dakin shi kanshi ogan gyaran ya burge shi .... suna zaune bayan sallah isha'i shida Mahmud suna ta hira can yace inji de baka manta da alkawarin ka..... Murad yayi kasake yace ummm inajin na manta de dan tuna min man.... Tab ..to bari na tuna ma kace duk lokacin da kayi aure to ranar sallah zaka gayyaci goma daga cikin abokanan mu .... Se lokacin ya tuna yace kai amma kacika aboki na kwarai na gode kwarai kawai yanda za'ayi ka gayyaci wanda suka daci ni bari na sanarwa da Momy ...nan suka rabu....yana me jin dadi samun aboki irin Mahmud Yana shi gowa ya tarar da Maysam tayi daidaya a cinyar Fulani..se shagwaba take zubawa. Shigowar shi ma bata sa Maysam fasa abunda take.yi ba...ya zauna ya gayshe da fulani...Maysam ta dago da nufin gaidashi taga ya zabga mata harara ta turo dan karamin bakinta tace Momy kin gandhi ko... Kafin Momy tace wani abu....se kuma cuwat ta tashi taje tana famar hayewa cinyarshi ...... Be hanata ba ta kuwa haye ko kunyar fulani bata jiba ...shima kuwa ko aka se ma ya shiga yi mata rada a kunne ai kuwa se ga shi tana kyalkyalewa da dariya .....abun se ya burge fulani ta girgiza kai da taga abun bana karewa bane ta tashi zata bar musu wajen ...caraf Murad yace Momy wajenki fa nazo .. Fulani tayi dariya tace to ai naga tunda kazo ku manta dani ne ai... Dariya Maysam ta kyalkyale tace haba Momy mu mun isa ne .. kawai fa cewa yayi.wai... Da sauri ya rufe mata baki da hunnun shi..yace Momy daman gobe nake gayyatar abokane nane bayan a sauka a sallar Idi ..to shine nake son ayi musu wani abunn Fulani tace wai ni kake fadamawa ko kuma da matarka kake ne... Kicin2 yayi da rai.... Fulani tace to ai naga Martarka ta iya ne .... Yace Momy fa abinci mutum goma ne Maysam zata iya ... Dariya ta subcewa Maysam tace tab yo sosai ma zan iya ...kuma ma walahi tunda kace haka ni zanyi shi ko yayi dadi ko akasin haka tanayi tana murguda mishi dan karamin bakin ta ... Shi abun ma dariya ya bashi yace shikenan meda wukaken yar gidan Momyn ta ..amma fa idan beyiba nida kene a gidan nan... Itama ta cafke da fadin in kuma yayi fa nida kaine nima .. Fulani de banda dariya babu abunda take musu...nan sukaci gaba da hirar su gwanin ban sha'awa... Washe gari Sallah duk wanda kaga fuskarshi sake take da annuri Maysam tun asuba bata koma ba tana kitchen da kuyanginta se oder take basu kamar wata uwar mata ... Kan kace mi har sun gama sun jere komi bisa dinning table ...jus ma kala biyu tayi natural se kuma na gwangwani .....gida ya kaure da kamshi ni kai na ina mamakinta yanda take komi kamar ba yar sha hudu ba...tana jin alamar saukar idi ta shige tolet ta zabga wanka ta zauna nan ta fara kwaliya dankuwa an koya mata ado lokacin datake koyan girki...tana nan taji haya niyar su ...ya shigo da kanshi yace ta shirya ta fito yayi présenté(introducing)dinta ...to kawai tace da shi ...... Nima ina ganin futarshi na mara mishi baya ...samari ne zuka2 masha Allah .....Mahmud kawai na sheda sauran duk ban sansu ba ....suna nan sunata hira sun shafe 15 minutes shiru ba labarinta daya daga cikin su yace wai M² matar ka baza ta fito mu ganta ne ......dayake haka suke kiranshi tun suna secondry Shima abun ya bashi mamaki har ma zuciya ta fara daukanshi yana ganin kamar ta raina shine .... Dariya yak'e yayi yace bari na dubota .... Tashi yayi yana tafiyar nan tashi ta tamaka.da kasaita. Tunda ya hauro ya fara kiranta cikin fushi da karaji ....dama tana bakin kofar dakinta jin ze shigo itama se tayi kamar daman zata fito ne a dede bakin kofar sukayi karo ita tana famar fita shi kuwa ze shigo ... Wani waro ido naga Murad yayi ya nunata da yatsa yace miye hakane.?..... Se lokacin na kalleta wai fans kunsan miye a jikin ta... Hum ina kayan daya sayo mata wato pant da bresiya ,se takalmi da bag babu kaya jikinta se su ta kuwa ci uban ado .... Maysam ta jujuya tace mi kuma nayi naga kowa ranar sallah kayanshi na salla yake sakawa to miye na wani kallona ne harda tambaya...tana gama fadar haka ta raba ta jikin shi ta fita ... da gudu ya damko ta yace wai kina haukane zaki fita a haka... Tana kiciniyar kwace hannuta ita a dole seya saketa tace dan Allah barni na tafi na gaisa da bakin mana daga baya mayi magana...... Cimak ya dauketa ya shiga dakin ya meda kofa ya rufe harda sakata cike da bacin rai ya fara fada ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba kamar ze daketa yakeji... Aman mi maysam ko ajikinta se ma kara turo dan karamin bakinta take ..ta haye gado kwalla ta cika mata ido ....can kawai sega hawaye shar2... Nan da nan ya dakata da fadan zuciyarshi ta fara bugawa da sauri se kuma ta fara mishi zut2 beyi aune ba ya ji kwalla ta cika mishi ido shima .....da sauri ya haura gadon shima ya rumgumeta ya shiga lallashi da kyar ya samu ta tsayar da kukan yana sakinta ta juya mishi baya se turo baki take.... Juyo da ita yayi yace yar gidan Momy miyasa bakya jine wai .. Cike da shagwaba da yarinta tace to ni minayi ne?naga de kayan sallar daka siyo mun ne kuma kaida kanka kace sune kayan sallana se yanzu dan na saka kuma za'aga laifina... Goge mata hawayen yayi yace shikenan laifi nane ki saka wasu kayan zuwa gobe zan siyo miki kayan sallarki...cike da murna tace shikenan ta mike ta nufi wardrop dinta ...tana dubawa Murad yace zokiga wani abu ....bayan tazo ta tsaya gabanshi yace yanzu ke Maysam da na barki se ki fita a haka .... Tace e man ... Ya nuna kirjinta ta da ita yanzu ne ma ta fara kirgen su Murza da Malam Musa lol yace bakya ganin kin fara girma ne ... Se a lokaci ta kai idonta wajen hannu daya ta sa ta kare dayan kuma ta rufe idonta dashi wai taji kunya tana dariya kasa2 tace nima fa da gangan nayima haka shiyasa ma naki futa seda naji zaka shigo .... Shima dariyar yayi yace to kawo na saka miki kayan kinga mun bar baki a falo... Girgiza kai tayi tace nide a'a..stil bata fidda hannuwanta ba Leka fuskar tata yayi yace nine fa yayanki yanzu kuma kunyar yayan ake.... Se asan nan ta fiddhannunnu ta dauko wata narkekiyar shadda wacce tasha zubi tare da hijab kalar shaddar ta kawo mishi ..shi ya saka mata har hijab din ... Se kuma yace wai wannan adon da kikayi ina zaki dashi yana magana aman idonshi akan dan karamin bakinta..ya doko tissu ya fara goge mata girar datayi tas ya goge ta ...sannan ya fara kiciniyar Goge mata jan baki se mita yake nan fa ake yinta Maysam tace bata san yaren ba ta fara kuka ita ya bar mata adonta ..... .. Kawai kallon dan karamin bakin yake bata yi aune ba taji bakinshi cikin nata tsit kakeji tayi banda muzzurai ba abunda takei...nan fa Murad ya ci gaba da abunda yake inda tsayuwa ta nemi gagarar Maysam tana famar sume mishi cak ya daga ta ya cigaba..da abunda yake se wani lumshe idanu suke.. .seda ya tsotseshi tas tukon ya saketa se haki suke su duka ..zatayi magana yace shiit yajata suka fito palon kasa bakinta banda zafi babu abunda yake mata tana mamakin wannan abu a ranta tace komiye wannan kuma oho dukda abun yayi mata dadi amman tana ganin kazanta ne ai wannan.. Hannun sarke cikin na juna suka shigo falon ...nan fa aka fara kallon kallo har abun ya qullar da Murad yayi tsaki ciki2 ..har kasa ta duka tayi musu sallama tukon ta gaishe su zata qara yin wata maganar se kawai Murad ya tari numfashinta da fadin ya isa haka nan...ya jawo kayanshi bisa daya daga cikin kujerun ya zauna ..cinyarshi ya dorata ita kuwa se mutsun2 sauka take can de ya harare ta...tukon ta zauna abunta amma kanta a kasa saboda kunya.. Nan aka fara magana kasa2 ..Mahmud daya gaza hakuri yace to ai de zaka barta tayi serving din mu ko ... Wani kallo yayi mishi ....daga bisani kawai seya danna wani abun nan kusa dashi kan kace mi ukku daga cikin kuyangin suka shigo nan suka zube gaban yarima Murad suna kwasar gaisuwa ........sun kai 3minutes nan su basu tafi ba kuma shi bece su tafi ba....... Rada naga yayi wa Maysam ......bayan ya gama ne .....Maysam ta basu oder dasu kwaso abincin sukawo nan falon (to fa mulki ya motsa)..kan kace mi sun shimfida leda sun zube kulolin anan .....suna gamawa tace zaku iya tafiya.... Mahmud yace to tunda kin kora su se ki sauko ki zuzzuba mana cike da tsokana yayi maganar dan yasan gogan baze bari ba ..... Kamar yanda ya zata ne dan kuwa ita de har ta sauko Murad ya riketa tare da girgiza mata kai ..tasan mi hakan yake nufi ....ya kalli Mahmud yace ai idan sauran baki ne kai fa ...zaka iya serving dinsu ......amma kai ma kasan bazan bari mace ta shigo cikin ku tayi serving dinku kuma macen ma mat......maganar ta makale mishi jin yana
Chapter 28 · 0% Book details