← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 67

Sashe 52

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[14/08 à 00:02]
Be dawo gidan ba se wajejen 7 na safe ...lokacin tana kiciniyar hada mishi break.. Yana son ya iske kitchen din kuma baya son bayin shi su ganshi shi da kanshi ya shiga wai kitchen ..yarima guda ai se su rena shi ..
Dan haka wanka ya shiga yayi abun mamaki kafin ya fito ta fito mishi da kayan da ze saka amma kuma bata room ....jiki a sanyaye .dan da ta saba mishi da ita ke shiryashi aman yau ko dan goge jikin ma be samu ba bare aje ga zancen shafa mai da saka kaya..duk se yaji ya damu ..haka ya shirya yayi komi ya fito da jakar computer shi a hannu lokacin bakwai da rabi tayi ...tana break a dinning dan haka shima zuwa yayi yana zaunawa ita kuwa tayi cuwat zata bar mishi wajen..hannunta ya rike yayi kalar tausayi yace to yanzu baza ma ki gaisheni ba kuma wa kike so ya serving dina ....

Tana kallon gefenshi tace g.morning da fatan ka tashi lfy?tana fadar haka ta fara zuba mishi abinci...har ta gama ko kallonshi batayi ba ..zata fice yasake rukota yace yau kodan morning kiss bazan samu ba bare aje ga zancen feeding dina...taya kike son na tashi lfy bayan kin juya kin baya

Ba karamar jarumta tayi ba, dan kad'an ya rage ta sheke da dariya amman seta mazge ga kula tausayin shi daya dirar mata..tana wani ya mutsa fuska tace dama na sani jikina ya dame ka bani ba ..tana fadar haka ta fara kokarin kissing dinshi da sauri yace a'a ki barshi kawai ..shima yana fadar haka ya fara cin abincin shi ...

d'aga kada tayi irin na i don't care din nan ....room ta shiga ta fito cikin shirinta na school babu laifi irn shigar daya ke so take hi....itakuwa tayi hakane dan kada ya samu abunda ze fake dashi yayi mata magana. .tace dashi mun tafi se anjima.

Tana saukowa ta gamu dasu Mufeedah suma cikin shirin su dan haka suka fita driver ya kaisu ...

Murad kam tana ficewa yaji abincin ma ya fice mishi a rai dan haka office ya fice abunshi duk jikinshi yayi sanyi......

Haka ya wuni ba tare da yaci komi ba ..kuma da dare ma komi na bukatarshi ta aje mishi tayi ficewarta kasa wajen du Mufeedah sukayi exercice din su dan ita kam hankalinta a kwance yake ..abunda take so yana sonta shima.wajejan karfe goma suka gama ...tana hawa tayi wankanta tare da shirinta kamar jiya .....dakinshi ta shiga ta tarar da shi ya zabga wani uban tagumi yana can yana tunani da alama be san ta shigoba dan yayi nisa cikin tunanin ..daga nan take jifanshi da kallon kauna wanda shi bema san tanayi ba...seda tazo gaf dashi kamshin turarenta ya fargar dashi daga kai yayi ya kalleta tare da sake mata wani tsadaden murmushi ..ita kanta seda gabanta yaba ras..har jikinta ya fara sanyi ..aman kuma setayi ta maza tana wani ya mutsa fuska tace dama zowa nayi naji ko kana da bukatar amsar hakkin naka yau ne dan bana son fadawa cikin tsinuwar malaiku..

Yayi yar dariya ya girgiza mata kashi yace wai so nawa kike so na gaya miki ne ..kije kiyi kwanciyar ki kawai ki barni da abunda ke damuna ....kamar jiya yauma a palon ta kwana shima kuma da wahala bata kare mishi ba kamar jiyan haka ya kwana .a zaunen..seda sukayi kwana ukku a haka duk ya fara ficewa hayyacin shi ..har wata rama yayi abunka da dama ragowar damuwar sweetbaby ne..ga kuma Maysam na gasa mishi aya a hannu .gashi batada aiki yanzu ta dawo kissing din ta kamar da ..kuma daya meda mata setace ai dama abunda yake sone ...dole tasa yanzu inta kissing dinshi yaki medawa har ta gama abunta abunka ga wanda be saba jin wani abuba a jikin mace se akan Maysam ..shi se yanzune ma yasan yana da lfy dan da har su Mahmud suna kokonton ko bashida lfy na shiyasa mata basa gabanshi..to gashi yanzu abun yazo kuma wacce yake da bukatar ta nuna bata san zancen ba..wani lokacin in tayi wani style din da shafa wani turarenta me sunan Feminism har mararshi take kullewa yashiga ciwon cikin da babu shiri ..
Yauma kamar kullum Maysam data dawo daga school din safe ta tarar dashi a palo yana kallon wani film da alama shima be jima da dawowa ba..wanka tayi kamar ko yaushe ta cakare da kayanta ta shafa kuma turaren dan da gayya take komi...kiciniyar dora mishi mafi saukin lunch take, dan tanada lecture yamma..shiga da fita goma dazatayi daga kitchen inta zo ficewa se ta biyo ta bayan kujerar dayake kai ..ta kamo kanshi ta sama ta duko ta bashi light kiss .daya meda martani se tace to ko kewa yowa zanyi ne ka anshi hakkin nakane..

Sede ya girgiza kai yayi murmushi..a haka harta gama ta jere a dinning din sannan tace'' ton dejeûne est prêt''..

suna tsaka da lunch din yace wai dan Allah mikike sone nayi miki ki dawo mun kamar da ...bazan iya jurar wannan hukuncin naki ba...

Spoon din ta aje tace inaso ka nuna min irin kalar son dakake mun i mean ka nuna mun irin taka kalar soyyayar ka koma mrs romantico..😉

Dan murmushi yayi yace aman de kin sani ban iya soyyaya ba ko?hasalima banta ba soyyaba bayan wacce nayiwa sweetbaby na kuma kinga ita tun ina secondry da rasu ..ita kuma tana nursing..kinga kuwa wasu kallaman ma na soyyaya bamu sansu ba......tunshi ban taba soyyaya ba se yanzu dana fada tarkon sonki .....

Dan murmushi ta jinjina kai se kuma tace to ai se kaje ka koyo tunda de yanzu wai kace kana sona kamar yanda kake fadi ..

Yayi saurin cewa son da nake miki ya fice wai ..

Tace kuwa inde har hakane zaka iya kenan..

Jinjina kai yayi .suka ci gaba da cin abincin su ..kowa da abunda yake sakawa ..ita tana jin dadi har cikin ranta cewa ta samu wani gurbi a zuciyar shi..shi kuma yana tunanin ta ina ze fara...

Suna gamawa ya fice a gidan ...sedaya fita a unguwar ma se yasamu wani guri yayi parking sannan ya dannawa Mahmud kira..
Bayan sun gaisa yace wata magana nake so muyi aman banda dariya fa..

Mahmud yace to ina jinka..se kuma ya ra sa ta ina ma ze fara gayawa Mahmud maganar ..

Cande yace soyyaya nakeson ka koya mun..

Haba ai Mahmud ya shiga kwasar dariyarshi...harda rike ciki yake...

Tsaki Murad yaje yace matsalata da kai kenan ...

Mahmud kam da kyar ya tsagaita yace to ai ita soyyaya ba koyawa mutum ita ake ba kowa da irin nashi salon soyyayar ..bankiba de kace kallaman ta to suma zaka iya kirkirar naka kalaman specifique a toi seul .....nan de ya dan bashi yan shawarwari tare da yan kallamai ...

Mahmud yace welcom to the lovers word ..ina tayaka murna....

Tsaki yayi ya kashe wayarshi... Se kula shi kade yake yiwa kanshi dariya

Be koma gidan se bayan isha 'i lokacin har sun fara exercice aman dataji motsinshi seta sullube ma su Mufeedah tayi tafiyar ta .....ya fito wanka kenan ta shigo bata damu da towel ne kade jikinshi ba dan tama saba da hakan ..kaya ta fitar mishi zata tafiyar ta ya komo hannunta yana fadin ina zukekiyar babyna data dara zinaria haske da kyalli zata tafi haka tabar dan bawa Allah da zuciyar shi ta tsunduma cikin kogin so da kaunar ta ne.harta na falar tarwatse mishi a duk lokacin dayai gamdakatar da ita.yana wani lumshe sexy eyes dinshi...yake fadar hakan.

Lumshe ido tayi dan kalaman direct cikin zuciyarta suka caka ..ba karamin namijin kokari tayi ba wurin kin nuna mishi taji dadi kallaman shi har dadi na kusan tarwatsa zuciyanta ba ..ta wani yamutsa fuska tace au yau kuma ni na amsa sunan BABYn kenan?na aza sunan nan sweetbabyn kane .kade.ni kam ai bankai wannan matsayin ba ..tana fadar haka tayi waje dan inta tsaya zata iya bada kai yanzu nan..
Murmushi yayi yace mujede zuwa ...

Itakam tana fita ta shiga yi wa Allah godiya ai da shoki ta shige dayan dakin dadi kamar mi......

Haka daza su kwanta ya bad'eta da kallamai na soyyaya har taji kamar ta rungumi abunta amman se ta mazge ...seda sukayi kwana ukku kullum da iri salon soyyayar dayake bullowa da ita ..kusan wuni yake yana kawo mata flower,gift iri daban2 ,,a ko ina na gidan yabi ya rubuce shi da I love you Maysam ,kai har mirrow na gidan basu tsiraba ..kota goge kafin ta dawo ya sake rubutawa .....kaf draf din su ya sake sabbi kuma duka an rubuta I love You Maysam ,wasu an rubuta ''je ne vis que pour toi.my Princess'' wasu kuma je t'aime et je t'aimerai pour l'eternité aka rubuta ajikinsu..kai takai ta komo ko tolet din su yabi ya rubuce su da kallaman shi.....se kuma uwa uba riritata dayake da mayatatun kalamai na safe daban.,na rana ma haka ,na marece ma haka,shi kanshi mamakin kanshi yake bare akaje ga uwar gayyar....

Amman fa dan rigima har yanzu taki saukowa yanda yake so ba leifi ta dan rage shareshin datake ..

sede kuma daga jiya zowa yau kamar ciwon shi ke san tashi dan yau kam asibitin ya wani amatsayi majinyaci ba docto ba.abunda kuwa ya tashi ciwon be fice wata waka da Maysam din ta tsira wato setaga yana aiki seta zo tana wakarta tun abun baya damunshi har yazo ya fara ..wakar itace
🎼 _Abun son zuciya shine kasamu me kishinka ,_
_Gobe inta samu hakika. Babu zancen rabewa_ 🎼.shi duk gani yake rabuwa zatayi dashi ....Mark yayi ya gaya mishi damuwarshi aman yaki fadi har ya gaji dan haka ya kira Mariam bayan sun gaisa yanemi yayi magana da Maysam ..bata musa ba..itakuwa lokacin tana ta tunanin shi dan kwana biyun nan ta lura da akwai abunda ke damunshi..ta kuma yanke shawarar yau zata zubadda kayan yakin ..ta rungumi Muradinta ..haba yayi ma kokari ai ...
Chapter 52 · 0% Book details