← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 67

Sashe 37

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Story&Written
by
*FASMA*
*Alherin Allah ya kaiwa masoyan wannan book din a duk inda kuke ..hakika* *ina jin dadin comment din ku kuma yana bani kwarin guiwa ...daya wa naga sakon ninku..wasu* *suna cewa ina jan aji da rai ..to bahaka bane muma muna da uzuririka a gabanmu .....Allah* *ya bar kauna da zumunci ina yinku iri more totaly din nan*
*Pls masu juyamun littafi ku dena bana so . ...kun san kanku base na tona ku cikin jama'a ba so tun kafin abu yayi nisa ku fasa ....*
Dedicated to all my fans
75__76
```Manzon Allah (SAW) ya ce''babu d'a'a(biyayya)ga kowa cikin sab'on Allah''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi.```
Murad kam fushi ya dauka da Maysam ..ga zuciyar shi na azalzalarshi kan ya kira ta amman yayi biris da ita seda yaji ta fara mishi zut2 din nan sanna ya kira office din ..lokacin sun gama lecture kenan ...
Da sallama ta amsa .. Tu nan yaji wani mayen sanyi yaji a zuciyarshi amma wani bangare yana tunatar dashi cewa yayi fa fushi da ita .. Dan haka
Amsa sallamar yayi a dakile kamar ba shine ke daukin kiran ba.
Cikin sanyi jiki ta gaishe shi tare da tambayar ya aiki. .
Da kakkausar murya yake amsa mata fada2..
Maysam ta sake cewa yaya mi akayi ne ?ko nayi maka wani laifine,?
Cike da kaguwa cikin fada yace au baki ma sani ba shikenan..yana fadar haka ya katse kiran..
Gaban Maysam ya bada dam ta fara tunani ...ji take kamar tayi kuka dan ita bata san lefin ta ba kuma gashi shi be fada mata ba...
Har ta juya zata fita ya sake kiran dan zuciyar shi ta hanashi sukuni tana ayyana mishi cewa Maysam na can na kuka ..shiyasa ya kasa resister ya sake kira..
Tana dagawa taji shine yayi sallama bata jira taji me ze ce ba ta saka mishi kuka....
Tirkashi nan ya dafe setin zuciyarshi yana fadin why nayi mata fada gashi yanzu na sakata kuka..beyi aune ba yaji kwalla ta cika mishi ido..da kyar ya daure ya rarrashe ta ...
Maysam tace shikenan amma yaushe zaka dawo nayi missing dinka fa....
Dan jim yayi dan shifa baya ma jin ze dawo kasar..
.
Yace ni kaina bansan ranar dawowata ba kai inaga ma bazan kara dawowa ba ...
Bata kawo komi ba dan ta zaci dan ya tsokane ta ne kawai dan lokacin daza suyi bankwana ya jaddada mata baze yi 3months ba ze dawo shi ya sama bata dau abun serious ba...
Zata sake jefo mishi wata tambayyar ya katseta da fadin kin ga se anjima inada aiyuka ...be jira mi zata ceba ya katse kiran dan kwata2 ma baya son ta mishi zancen.......haka ta koma aji jiki ban kwari dasu Maheeba suka tambayeta ganin mood din ta ya sauya aman se cewa tayi ai bata jin dadi ne...
Sarki kuwa ba karamin dadi yake jiba kasancewar Malam Musa wazirin shi ...
Lokacin da labari ya isa kunnen Maysam harda kukan dadi tayi tace gashi yanzu SANADIN ACCIDENT ta samu gatan da ba kowa ke sa'an samun shi ba..da tana cikin 'KUNCIN RAYUWA(littafi na na gaba in sha Allah).na azabar Murza aman yanzu...ta samu Mahaifiya wato Fulani ..ga karatun boko da islamiyya. Gashi kuma yanzu anyi wa Abbata Waziri.ita kam in bata godewa Allah da wannan ni'imomin ba dayayi mata to mi zatayi ...har Fulani ta kiraya ta shiga yi mata godiya har seda ran fulani ya soma baci tukon ta dena..
Haka rayuwa tayi ta tafiya inda zuwan Murza ya kara sa zuciyar Madina kara yin baki yanzu bata da wani buri na taga Murad ya mutu...sabon boka ma yace mata hakan bame yiyuwa bane amma taki hakura kullum da irin plan din datake shiryawa....
Murza kam ta zama tabarya me baki biyu ko nace me fuska biyu ma ..dan yanzu tana yawon shiga bangaren fulani tana nuna mata ta shiryu ta dena abunda take alhali tsegumi ne ke kawota dan ta kai wa Madina rahoto. ..duk abunda ta gani ko taji a bangaren fulani to seta gayawa Madina shi. Amma har yanzu ba'ayi katari taji Fulani ta kirayi Murad a gabanta shi yasa suke kara jin dadi .
Basu san duk safiya se Fulani ta kirashi a waya ba ...kuma kullum seta nemi ya dawo amma se ya fara kawo mata kabli da ba'adi ..kullum cikin yi mishi addu'a take .
Ita kam Madina zuwan nan Murza yayi mata dadi tana samun information akai2..
.
A banagaren su Muheeba kuwa bayan sun ji sauki amma fa fuskar ta bata dedetu ba duk tayi wani tabo2 babu kyan gani ...
Kullum cikin kuka take ganin haka yasa Mahaifiyarta ta cira musu ticket zuwa wajen danginta na Ghana ..(safe journey du Muheeba Allah ya raka taki gona )
A bangaren su Maysam kam itada kawayenta sun dage ba kama hannun yaro karatu suke sosai....
Cikin sa'a suka kawo makin da ake so dan haka shugaban makarantar ya ce vacation din 1 month ne kawai garesu dan wani lecture za'a fara yi musu dan kada susha wuya....
Har lokacin Murad be dawo ba kullum intayi mishi zancen se ya katseta da wani zancen ........yanzu kam ciwonshi har tashi yake kadan2 dan kuwa Maysam kuka take saka mishi kan se ya dawo tayi missing dinshi ..
Shi kanshi baze ce ga taka meman abunda yake hana shi dawowa ba ...kullum cikin rarrashi yake ...Fulani ma kullum cikin bata hakuri yake....
A na sakin su Fulani tayi mata booking jirgi ta dawo gida...
Ba karamar Murna sukayi ba itada M.Musa ba da suka juna ..rasa inda ze sakata yayi ..Murza na gefe se tabe baki take tana tsuka kasa2 amma da taga Maysam ta kallota se ta fake da dariyar yake wai ita a dole nan ta shiryu ta fara son Maysam.....
Tun Maysam na dari2 da ita har ta saki jikinta kadan ..
Lokacin da Maysam ta sanarwa da Fulani yanda sukayi da shugaban ba karamar murna tayi ba dan haka tana cika watan ta fara shirye2 komawa. ..
To fa ranar wata samedi(Saturday )ana gobe komawar Maysam .....suna falon Fulani ,Maysam,Murza,da ita Kanta Fulanin ...
Hira suke wacce duk ta karatun Maysam din ce . Murza se wani tarerayar Maysam din take amma fa k'asan zuciyar bakin cikine fal dan ji take kamar ta rufe Maysam din da duka ganin irin yanda take zuba shagwabarta a cinyar fulani ..ita kuma se lallaba ta take. ...
Ganin abun bana karewa bane yasa fulani fadin bari de inkira mijin ki may be shi ya lallabaki ki barni na huta da shagwabar nan.
Gaban Murza yayi wata irin mummunan faduwa ta shiga wuwurga ido ..
Kamar wasa Fulani kuwa ta danna mishi kiran ..
Murza ta kashe kunne kuwa. ..
Bayan ya gaisheta ne ta sake tambayar shi yaushe ze dawo ..nan ya fara yi mata kame2 ..
Fulani tace to ka bude kunnuwanka da kyau kaji ina son ganin ka a week din nan wannan umarni nake baka maza2 ka taho ....
Cike da tashin hankali yace to Momy zan zo ..
Wani farin ciki ya mamaye zuciyar Maysam da ta fulani tace to se kazo Allah yayi maka albarka.
Sabanin Murza datayi mutuwar zaune zuciyar ta cike da wasi2 a ranta tace daman suna waya ko kuma yau ne suka fara kawai. ..bata gama tsinkewa ba seda taji Fulani na fadin pls ka lallaba min yarinyar nan ysa duk ta hanani wali...
Shata da baki Murza tayi ganin Maysam ta karbi wayar tayi cikin kuryar daki tana dariya kasa2 ...wani dunkulelen bakin ciki taji ya to kare mata wuya a ranta tace kada fa Yaron nan ya fara son aljanar yarinyar nan......babu me bata amsa dan haka ta danne bakin cikin ta gaban Fulani ta tashi tana fadin barin koma akwai wasu ayuka da zanyi ...nan tayi ma Fulani sallama ta fice ..
Itade Fulani tana kallonta ne amma bawai ta yarda da tuban Murza ba..
Tana fita kuwa ta fada bangaren Madina ......
[9/2, 10:42 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 10:45 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 37 · 0% Book details