← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 67

Sashe 48

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[09/08/18 à 23:26] karfe Biyu saura na rana jirginsu ya sauka a England ..lokacin su Maysam suna school basu sauko ba. Amman ko ina tsaf2 da shi duk da kuyangi ke gyara dukuna aman banda nata da na oga Murad..
Yana shiga dakin wani sanyi kamshi ya buge hancinshi besan lokacin da da lumshe ido ba tare da yin ajiya zuciya. ..wanka ya shiga yayi ya fice masallaci ..dayake bashida yunwa dan haka can yayi zamanshi har akayi la'asr anan suka gamu da Mark suka gaisa yayi mishi sannu da zuwa har yana jaddada mishi aiki na nan jibge a office din shi. .suna ta hirar du har suka iso. kowa yayi gidanshi duk da har yau Mark beyi aure ba aman yana da gidanshi anan kuma kusa dana Murad yake . ...

Yana zuwa kawai ya hau gado ga gajiya yana ji amma yasan baze iya yin bacci ba ..dan besa ba baccin bayan la'asr ba..

Gadon kawai ya hau ya shiga chat a whatsapp....

Katsam yayi karo da number Maysam kuma gata online..a ranshi yace karatun kenan?

Salut(hello) ya aika mata

Ai kuwa se gashi ta medo mishi da salut yayana comment vas tu?ita kam bata ma lura da wata numbershi ce suke chat din dan duk numbers shi MURADINA ta rubuta akai wasu da manya haruffa wasu kuma da kanana .shiyasa bata babanta su. ..

Be amsa mata ba se cewa ma yayi karatun kenan. ..kuma ma ashe da gaske ne kina chat dinko?

Wani yawu ta hade tama rasa irin amsar daza bashi .. ..dan ta kawar da zancen tace kai yaya wly nayi missing dinka dayawa kuma ma Momy tace tabaka sakona pls yaushe zaka dawo ne..brcause i need it dan wanda nazo da su sun k'are .

Ya ganeta sarai amman seya biye mata dan yana jiranta yau seta gaya mishi tun yaushe ta fara .....

Sun dan taba hira inda take sanar mishi ai har sun tashi ne driver suke jira bezo ba...amman yanzu zasu koma gida ...sallama sukayi tana ta murna abunta jin yace mata cikin satin nan zezo...

Su Mufeedah kam se tsokanarta suke tana ramawa..

Tun nan palon taji kamshin turaren sa amman seta basar..ai kuwa tana haurawa stair hancinta ya tambbatar mata da kamshi da karfi2 cikin hanzari ta tura kofar dakin ...

Tana hangoshi da gudunta ta isa batayi wata2 ta fada kanshi dan murna tana yayana sannu da zuwa yaushe kazo ne...

Rumgume juna sukayi ..sun dan jima a haka sannan ya saketa suna kallon juna tace ina Momy na ?.yanda ta wani langwabar da kai se yaga tayi mishi kyau .

Yace tana nan she is fine ..tace tayi missing din ki .itama.

Kwalla har ta ciko idonta tace nima nayi missing dinta a lot..

Goge mata hawayen yayi yana kallon dan karamin bakinta yace me rigima yau babu ko dan kiss din ma na welcom back..

Ya tsine fuska tayi tace ee..saboda na gaji da abun...

A ranshi yace kenan de taji zafin maganar dana yi mata ranar nan..

Basarwa yayi shima ..ya dan daure fuska yace ban wayar ki ...tunda de ke bakya jin magana ....dan na san a chat din nan kika koyi wani salo2 ..

Bashi wayar tayi ba tare da ta musa ba. Se kuma tayi haramar tashi ta bar mishi wurin ..

Dawo ki zauna yace da ita..

Ya shiga duba wayar ..whatspp kawai ne take shima numbers fulani data shi seta su Mufeedah ....jikinshi yayi sanyi ganin da alama ma yaune ta bude shi kuma Momy ce tasakata dan tayi mata baya nin sakon maganin data bada akawo ma ..se tana turo mata photon duk magani tare da yanda zatayi anfani da shi. Kamar su Misk, bagaruwa,ganyen magariya dade sauran su se kuma advise din ta zanki shan fruit a kai2... Se kuma turarikana wuta dana shafawa kamar su humra,kullacca etc..

Ita kam se turo baki gaba take tunda har be yarda da ita bane harda yake tamata bincike a waya..koma yana gane mata sirrinta na ita da Momy

Murmushi yayi ganin fa tayi fushi ...bakin ya dan buga kadan yana fadin ke bakinsan wata dununuwa kike komawa inkayi fushi ne...

Kamar wasa kawai yaga hawaye shar2 a idonta .....

Hankali tashe yake tambayar mi akayi mata daga dan bugan nan se kuka...

Maysam tace dama yaya baka yarda dani bane ...

Waro ido yayi yace in jiwa ?kinjiki da wani zance . .ke kam bakya rabuwa da rigima..

Maysam tace ba gashi nan ba har da wani min bincike a waya..

Murad ya sauke ajiyar zuciya tare da matsowa ya rumgumeta tsam yace ba haka bane yar renota ki fahimce ni ...

Yar reno kuma ta maimaita a zuciyarta ..

Yacigaba da fadin social media yanzu abun tsoro ne ..na fiso kimeda hankalinki ga karatun ki......''ce n'est pas ce que tu crois parce que je te fais confiance a 100%....

Se lokacin ta sauke ajiyar zuciya itama tace ''merci yayana...''se kuma tace naji kace yar renonka ,..mi kake nufi da haka ido cikin ido take maganar ....

Kauda fuskar shi yayi duk ya wani daburce .......dan ya kawar da zance yace idan zaki mun magana kada ki kara saka idonki cikin nawa...

Cike da mamaki tace 'pourquoi?still ta kafeshi da ido..

Juyowa yayi da niyyar bata amsa hallau sukayi ido hudu..

Fasa maganar yyi sema tashi da yayi ya shiga tolet jin ana kiran sallar magarib ...amma a ranshi fadi yake anya yarinyar nan ba wani abu take sakawa idonta ba...tun tana ya karamarta inde har mukayi ido biyu da ita to bana iya mata muso akan abunda take so.....se in wani dirirce gaba daya ...mtsss ya ja tsaki shi kade .a bayin ...

Yana fitowa fuuu ya fice ba tare da yakalli inda take ma..

Maysam alwalar ta shiga ta doro amma tunani ne fal ranta ..kawai mutum daga tambayya se ya hau fushi ..to Allah de ya kyauta .
Niko nace ameen

Sanin baya dawowa se bayan isha'i yasa tashiga kitchen ta hada mishi d'an specialité girki da jus..
Komi cikin sanyi jiki take yinshi ganin yayi fushi da ita .....bayan ta gama tayi sallah tazo dakin su Mufeedah ...exercice sukayi tayi har goma saura tukon sukayi sallama ..Mahmud ya kira Mufeedah suka fara zuba soyyayar su..

Itama Mariam babu laifi ta dan fara kula Mark dan ko kwawarshi ta isa a fara biye mishi. Ba laifi ta dan fara sonshi ..sede bataso ta zurfafa tunda tasan an riga da anyi mata miji a gida.....

Murad kam har lokacin be dawo gida ba..iya tashin hankali Maysam ta shiga..wanka tayi tayi shirin bacci ta bade jikinta da humra..tana jiranshi anan palo har baccin yayi awon gaba da ita.....

Se sha daya ya shigo .gidan.ganinta nan a takure bisa kujera se kuma ta bashi tausayi..dan yasan jiranshi ne take ...daukanta yayi da niyyar kaita cikin room kamshin humrar ya bigi hancin shi harda wani lumshe ido.... firgit ta farka ai kuwa tana sauke idonta akanshi ta saki mishi kuka ...

Shima se zuciyar shi ta tsinke ..zama yayi tare dayi mata masauki a cinyarshi yana goge mata hawayen yace ya isa haka to mima nayi miki da kin ganni kawai ki saki mun kuka....

Cikin kuka tace to ba kai bane kayi fushi dani banyi maka komi ba...harda wani tafiya kayi dare

Dan murmushin gefen baki yayi yace to ai ke ce se ki wani kafeni da ido ni kuma idon mu na sarkewa sena loosing control dina .ki dena bana so ''parfois j'ai l'impression que tes yeux me dominent même''..don suna sani yin abun da banyi niyya ba
Se da yayi maganar ya farga ..amma seya mazge

Itakam kankameshi tayi tace ba zan sake ba pls kada ka kara yin fushi dani .tana yi tana wani shafa mishi fuska ..ta kuma ji dadin kalam manshi

Shima rumgumeta yayi nan ya shiga kissing dinta yau kam har da romance yayi mata sede bata hanashi ba kuma bata meda martani ba saboda tsaro😎...dan kada kuma yayi fushi da ita ma...da taga da gaske birkice mata zeyi ne sannan ta raba jikinta danashi lokacin idonshi har sunyi dan ja..

Tace nasan bakaci komi ba pls na kawo maka kaci ko,.?
Yanda tayi maganar seya birgeshi gyada mata kai yayi dan babu bakin magana ......

Sosai yaji dadin abinci seda ya gama cika cikinshi ta hada mishi ruwan wanka yayi ..sukabi lafiyar gado.....
Har bacci ya fara daukansu kamar wanda aka tsikara cuwat ta tashi ta zauna tace wai yaya har yanzu matarka bazata dawo ba ne...
Cikin magagin bacci yace mizaki mata in tazo din ..wai ma mi yakawo zancen nan cikin dare ...

Turo dan baki tayi tace kowa da abunda ya dameshi a rayuwa nikam itace damuwa na..kuma kawai ina son ganinta ne inga nida ita wayafi wani kyau.sanna da alama bawata katuwa bace tunda naga kayan dake wardrop kamar ma zamuzo kai daya...kaga kuwa wly tanayi mun in kareraya yarinya .....ehe

Yace kai yama za'ayi ahadata dake ai kin kere mata akyau bazama ta kama kafarki. Yanzu de barni nayi bacci a gajiye nake..

Ai kam kamar ya zugata tace ba wani nan kawai dan na kyalleka kayi bacci ne kace haka..bayan ranar nan kace ta nada zallar kyau Harda shure2 tana ita bata yarda ba...

Dayaga dagaske bazata barshiba tashi zaunan yayi yace to kiss me sena Gaya miki gaskiyan magana..

Yatsina fuska tayi tace a'a barshi kawai bana so ni na gaji da abunan ..

Murmushi yayi a ranshi yace na jawa kaina da yanzu ina more abuna ..rumgumeta yayi yace to ''dort bien '' yayi kissing forhead dinta..
Meda kanta tayi bisa kirjinshi tace'' passe une excellente nuit yaya..'''

Yace da ita shima '' pareil aussi et ne m'oublis pas dans tes rêves''..

Murmushi kawai tayi ta kara makalkale shi . har bacci me dadi yayi awon gaba da su.. ..

Asuba ta gari

🌹🌹🌹. 🌹🌹

Wai fans ina labarin inna Murza ne?..yanzu kam tayi dan sanyi amma fa mumunan kudiri ta na nan makale a zuciyarta tana tunani sake taku ne tunda taga abun se kome musu yake. ..gashi kuma bata da kudin dazata na bawa bokayen ..
Chapter 48 · 0% Book details