← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 67

Sashe 46

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga baya kokarin guduwa daki ma tayi ..aman Murad yayi saurin kamota ...ya dorata bisa cinyarshi(to baga shi nan ba🙄 )ya shiga bata tun tana dari2 har ta sake jiki taci abunta..

Bayan sun gama ta tattare komi takai kitchen ...
Brosh sukayi sukabi lfyr gado...

Maysam kam matsawa tayi ta shige mishi jiki kan kace mi bacci me dadi yayi awon gaba dasu..
Tun asuba bata koma bacci ba kamar kullum...
Murad yana shigowa ya ganta bisa sallaya se karatun alqur'ani take..sata gaba yayi ya tankwashe kafafu ya wani rufe ido wai muryar tayi mishi dadi..a hankali yake bin ta suna yi tare..

Seda takai aya ta Rufe ta ajeshi tace yaya g. morning...da fatan ka tashi lfy...

Murad yace ina fa na tashi bayan duk kinyi ta laftamun kafa ni duk jikina ma ciwo yake mu..kai dole ma ki koma dakin ki.

Maysam ta turo baki gaba sede batace kalaba..amma a ranta fadi take babu inda zani ina nan .dan bazan iya kwana a dakin waccar abar ba ehe

Sun danyi shiru .Maysam tace kai yaya babu ko dan Morning kiss din nan ma ..

Kallonta yayi yayi yar dariya yace waike bakya gajiya ne..

Kara turo bakin tayi ta tashi ta shige tolet tana zuwa dede kofar ta murguda mishi baki tace e din ai duk renonka ne kai ka koya mun...

Wanka tayi koda ta fito baya nan ya fice dayan dakin yin wanka tunda taki zuwa ita.haka tayi shirin ta na school dan gudun magana se tayi irin shigar dayake so wato hijab nikaf da safa....

Dukda kuyangin da suke nan sun yi musu abun break aman Maysam da rigima seda ta sake girka wani a ranta tana fadin kenan ma harda kuyangi ya samarwa matarshi ko ...humm..(kya de ji da kishinki🙄)

Mafi saukin break tayi wainar kwai,da plainted se ruwan tea ..nan palo ta saka kuyangi suka jere mata su...

Ta zauna kenan ya fito daga room da shirin shi shima ..zama yayi a kasa kusa da ita

Maysam tace yaya ga naka can fa wannan nawane wanda na girka fa ...

Murad yace to nakin zanci nima me rowa kawai.
Shiru tayi mishi nan suka fara break din ...suna gamawa ya kaita har kofar school din su ..ya shiga wurin principal din yayi mishi bayanin komawar su can gidan shi...

Abunku da jami'a kuma ma ta turai dan haka sugaban be wani nuna wani abuba ya bashi autorisation din zasu iya komawa ... Daga nan ma ya fice wajen aikin shi...

Haka kuwa akayi bayan sallar isha'i suka tattara komi nasu suka zuba a motar Murad hann se gidan shi...

Ganin barin mata su kad'e a bangare daban hatsarine duk da akwai dedekun dogarai a gidan amma it is a risk dan haka ya basu dakuna biyu na nan kasan bangaren dayake ikirarin na kishiyar Maysam ne ...

Shikuma suna dakunan sama da Maysam ..

Har Maysam na tambayar shi to in me bangaren ta dawo fa mi ze ce mata ne...

Ya bata rai yace ke ina ruwanki ne..

Haka sukayita zama a nan gidan Murad cikin kwanciyar hankali suna kuma karatunsu sosai da sosai....shakuwar su ma kam se abunda ya karu

Ana haka bayan two week ya shirya ze tafi ganin gida ..Maysam kamar tayi hauka ba dan ta kwallafa rai a karatun nan ..da babu abunda ze hanata zuwa gida ganin fulani..ranar daze tafiya sha kuka har yaji kamar ya tafi da ita da kyar ya samu ya lallabata ya tafi ..

Ko su su fulani dirar bazata yayi musu dan ko jiya Mahmud daya kirashi kan cewa yana so in ze taho ya zo mishi da camera kamar goma haka hight class nacan ...koda ya tambayeshi yaushe zezo se ce mishi yayi kawai se sun ganshi ..
Zo kaga murna wajen Fulani kamar mi tama rasa inda zata saka shi nan suka gaisa ya kara neman yafiyar ta...

Tace dashi yanzu de ya shiga ya gaida dadyn shi se ya tafi yayi wanka yaci abinci ya huta daga baya sa yi magana ..

Babu bata lokaci ya cika umarnin ta ..

Fulani se kara godiya take ga Allah ..tana me kara addu'ar ya kare su daga sharri masu sharri..

Yana shiga wurin Sarki ya tarar da Madina acan da alama de wani muhimmin abu ya kawo ta dan basa shigowa fada a yini rana sede da dare..
Wata zabura da babu shiri Madina tayi cike da mamaki take kallon Murad a ranta fadi take yau ni naga jarababbe dawo kayi..in ba ma mas...

Bata gama fadiba Sarki yace lfy de ko..?
Wayence wa tayi da fadin farin cikin ganin d'ana ne nake yayi mana zuwan bazata ne tana wani dariyar yake amma da ka ganta kasan bata da gaskiya se wani fiki2 da ido take.
Sarki ma shareta yayi dan murnar ganin Murad din ya rumgumeshi yana jin dadin ganin tilon dan shi..

Madina ta danne abunda ya taso mata tare da cewa bari na baku wuri zamu karasa maganar daga bayama ..sum2 ta fice tana saka da warwara...

Sun jima suna hira da dadyn shi .....sanna yayi mishi sallama ya fice..Yana zuwa bangarenshi ya tarar da Mahmud yana jiran shi..

Rumgume juna sukayi suna me jin dadi ..nan ya sake bashi hakuri kan abunda yayi mishi ..

Mahmud ya nuna mishi komi ya fice ......
Murad yace ga camerorin ka daka damen da zancen su ..

Cikin sauri da hanzari Mahmud ya karbe yana fadin kai amman na gode Allah ya biyaka ..

Murad yace wai ni mi zakayi dasu ne haka da ka wani azalzaleni ne akansu. .kaida ko budurwar taka ma na can England se ko yan gida zakana dauka halan ..

Mahmud yayi dariya yace kaide yanzu ka yi me wuyar sauran zance zakaji shi wajen Momy ..yana fadar haka ya sa kai ya fice tare da fadin Allah ya hutas da gajiya..

Murmushi yayi shige bathroom..

A bangaren Maysam kam bata san ta shaku da yayan ta ba se yau ta saka waya gaba tana kallo.. jiran kiranshi kawai take ya shigo amma shiru...ta kirayi Fulani bayan sun gaisa take sheda mata mijinta ya iso lfy ..sun fan tattaba hira tukon suka kashe.wayar..

Shikam Murad dayayi wanka yaci abinci sanna yazo yabi lafiya matela amma kuma se bacci ma yaki zuwa se lokaci tunanin yar renon shi yazo yayi mishi katutu besan ya kara shakuwa da ita ba se yanzu ..duk se yaji gadon yayi mishi fadi..wayarshi ya jawo ya danna mata kira ..

Maysam da rigima wayar na hannunta fa aman se akira na ukku ta daga ...

Sallama yayi kafin ma ta amsa yace ina kika shiga ne kikabar wayar ina ta kiranki...

Turo baki gaba tayi kamar yana gabanta tace ina na shiga ko ina ka shiga ..bayan ma kai ka manta da ni din..

Dafe kai yayi yace inji wa kekam bakya rabuwa da rigima. Fa..

Ai nan ta shiga zaba mishi shagaba kamar ba gobe da kyar ya lallabata ......
Suka taba hira sanna ya kashe wayar
Se lokacin ya samu baccin ya dauke shi ....bashi ya tashiba se gabbanin azahar alwala yayi ya fice masalacin masarauta....

Daga nan kuma ya fice bangaren Fulani..
Tana lazimi ya shigo da alama itama yanzu tayi sallar seda ya bari ta gama sannan ya sake gaisheta ...nan suka cigaba da hirar su har tana tambayyar yar ta Maysam tace inji de baka matsa mata ko..

Murmushi kawai yayi aman a ranshi fadi yake ai yanzu kam ita take matsa min abu kadan se take kiss me ..gashi ko kallon banza bana iya mata ...

Fulani ta katseshi da fadin nasande Mahmud ya sanar maka da komi ko..

Kalar tunani yayi yace akan mi fa ?

Nan fulani ta sanar mishi da komi kan su Madina kafin ta gama hawaye na tazuba ..kamar karamin yaro ya rarafa ya dora kanshi bisa cinyar ta yana kuka ..

Nan ta kara yi mishi nassiha tare da gaya mishi plan din su sosai yayi na'am da shawarar nan yakara shima tashi fasahar .......sosai yaji dadin irin yanda Mahmud ya nuna bajintar shi lallae ya cika aboki.......

A washe garin ranar aka saka camerorin anan bangaren Fulani dana Murad ..kai harda na bangaren Murza ma ..na Madina ne kawai yayi musu saura...

🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹
A bangaren Madina kam tana fita ta dannawa Murza kira ...babu bata lokaci da shigo bangaren nan cike da zafin rai da bacin rai take sheda mata Murad ya dawo gida yanzu nan ..

Murza tace kai ni wannan jaraba da mi tayi kama ..yaro nan dan bala'i ne ..yakama wanna karon muyi mishi me kan kat kawai..

Madina tace kawai kice ya haukata muna shi kiga kawai ma may be mota ta kadeshi ma ya mutu a yawon haukar tashi ......

Murza tace karai kuwa kawai hakan ma za'ayi....

Nan ta sake zube mata kudi .Murza ta faki idon mutane tayi satar hanya ta fice ...se gidan boka yankan adda...

Tofa ya kuke gani ?shin zasu sake cin nasara ne akan Murad?

Senaji comment dinku👆

Fasma 🖊yar mutan Zinder
[9/11, 8:50 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/11, 8:51 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

*Ohh my Aisha tu me manque déja ...wish you all the best😍❤❤❤❤...* love you irin sosai din nan

_My Mimsqueen Allah ya baki lfy ya sa zakkar jiki ne...🙏.._

Dedicated to all my fans😍❤

🅿 89__90

```Manzon Allah (SAW)ya ce''idan wani daga cikinku ya tashi daga wajen zamansa sannan sai ya dawo to shiyafi dacewa da wajensa.
Bukhari ne ya rawaito shi.```

[06/08/18 à 20:29]Ba ta dau lokaci ba se gata gaban boka yankan Adda ....nan ta kwashe dawowar Murad ta gaya mishi tare da sabon kudirun su....
Ya dan jima yana dan tsibacce2 shi har wata zufa take karyo mishi........can ya dago yace wannan aiki baze yiwu ba dan yaron a tsare yake ya fice inda kuke tammahani..

Murza tace to kawai ka haukatar mun da matar shi Maysam. .
Chapter 46 · 0% Book details