← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 67

Sashe 11

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🅿️ 23__24
```Mazon Allah (SAW)ya ce''Babu wani daga cikinku wanda aikinshi zai shigar dashi aljanna,haka nan babu wanda aikinshi zai tserar dashi daga azabar wuta ,har ni kaina sede don rahamar Allah''
Muslim ne ya rawaito shi.
```
Kamar wanda aka hankad'o shi ya fad'o cikin motar se huci yake beyi wata2 ba ya ware yatsun shi biyar da Allah yayi mishi ya zabga mata mari seda taga Star ze qara mata Mahmud ya rike hannun ya ce haba Murad miye hakane ...jinake yanzu nan mahaifinta ya damka maka amanarta .....
Bece komi ba ya dunkule hannun tare da juya. Kai...
Maysam kam tana lulub'e ciki mayafinta taci gaba da kukanta kasa2
Mahmud kuwa ya ba driver oder su tafi ..
Sun kama hanya ko ida fita daga garin basuyi ba Murad ya ce arrête(tsaya)...
Suna tsayawa Gaba daya motocin suka tsetsaya suma..
Da sauri dogarai suka kewaye motar yarima suna jiran suji dalilin tsayiwar ..yafi 5mn sannan ya bud'e motar ....nan ma ya dau kamar 2 mn da kyar kamar wanda bakinshi yake ciwo yace '' je besoin de laver mes mains ''(ina bukatar wanke hannu na)
Kan kace mi tuni dogarai sun kawo ruwa. sabulu da 'eau de javel' da alama dama sun tanadi hakan nan ma yakai 5 mn yana wankewa tukon ya koma cikin motar ...
Mahmud ya ce wai wani irin abune wannan muna tsaka da tafiya ka tsayar damu saboda wani wanki hannuka ...
Wani kallo Murad yayi mishi yace bakaga hannuna ya taba jikin kazamar nan ba so ina tsoran daukan wata cuta ne...
Bece komi ba se tsaki dayayi suka cigaba da tafiya..
Sunci rabin tafiyar amman Maysam bata dena kuka ba ..
Wata sangamemiyar tsawa Murad yayi mata yace walahi ki rufe min wanan kazamin bakin naki ko na tattaka yanzu nan(jifa kaida ma baka ganta ba taya kasan bakinta kazami ne )in bama iskanci ba ni banyi kuka ba da aka kakaba minke ..seke dan kin raina mu zaki tasamu gaba kina kuka ..to tun wuri kiyi muna shiru konayi waje dake yanzun nan dakikiya kawai..
Tsit kakeji tayi shiru kamar wanda ruwa ya cinyeta
Mahmud ya girgiza kai kawai yayi a ranshi yace a dake ka a hanaka kuka kenan
Har suka isa babu wanda ya sake yin magana ....
Zo kaga yanda fulani ke shiga da fice tana bada oder yau sirikar ta zata zo shirye2 ake ainun ....
Wajejen sha biyu na rana suka iso
Madina dake lab'e tana jiran taga an fito da gawar su Murad amma se taga ya fito ya na tafiyar nan tashi ta kasaita ...dogarai da kuyangi se kwasar gaisuwa suke ...
Kukane kawai ya rage mata tayi amma iya bacin rai tayi ..jitake kamar taje ta kasheshi ...a fusace ta koma d'aki tana huci tace walahi ya zamo dole kabar duniyar nan matukar ina numpashi to se na ga bayan ka...dana zauna in ga an nad'aka sarki na tashi a tutar babu gwara na kashe kai na.walahi...kafin hakan ta faru kuwa zan kawar dakai daga doran duniya...(ji wani jahilci.....Allah ka shirye mu)
Tana cikin haka sega Waziri ya shigo shima fuskar nan ba annuri ...nan ya labarta mata duk yanda akayi ...
Ta ciza yatsa tace ba komai kaje kawai zan san yanda zan b'ulowa abunn...kabarni dashi kawai......
Direct b'angaren Fulani a kayi da Maysam su Murza se kale2 take anshigo binni se wani washe baki take ta ma manta gidan Maysam tazo...
Babu wani kyakyami fulani ta rungume Maysam...
Itama kuwa batayi kasa a gwiwa ba ta kankanmeta tasaki wani sabon kuka...
Rad'a naga fulani tayi mata se kuma tayi shiru tanagoge hawayen ta.har da yar dariya..
Murad daketa kallonsu tun d'azu a ranshi yace na kusa fasa hawa cinyar Momy tunda har ta rugume wanna kazamar(jifa kai ko kunya baka jiba wai ka hau cinyar Momy. )
Tarba ta gani ta fa'da akayi musu ..Murza an samu kafar kaza se guiguiya take ..tana zuba santi...tama manta da bakin cikin da take
Maysam kam d'aki na mussaman aka kaita ana bata kulawa ....itama yanzu har ta fara d'an sabawa da bawa kuyangi oder duda ita tafi sontayi komi da kanta ..
Kamshi kam duk idan ta zauna se ta bar kanshi a wurin ..
Kyau kam har wani yellow 2 tayi kyawunta da tsantsar yarintar ta ya fito shar da ita...
Karfe hud'u dede aka fara walimar inda mutane da dama suka halarta ...anci ansha inda uban gayar da kyar aka shawo kanshi ya zo wanjen shima albarkacin abokanen shi na wajen aikinshi da sukazo .....amma fuskar nan a d'aure tam...haka aka gama gabani magrib sannan kuma bayan isha za'ayi paty...
Zaune take se kuka take yi anyi2 tayi shiru takiya kuma taki shiga tayi wanka har ana kiran sallar isha'i.
Dasuka ga abun banayi bane se suka kirawo fulani nan suka fita gaba d'aya aka barsu su biyu . ....
Fulani tace Maysam2
Ta d'ago kai idanunta har sun fara yin ja saboda kuka
Goge mata hawayen tayi se kuma ta rumgumeta ..tana d'an bubbuga bayanta tace haba Maysam kukan nan ya isa haka ko so kike ki jawowa kanki ciwon kaine?ko yunwa kike jine?
Ta girgiza kai tace a'a
Wani abun kike so ?ko kuma wani ya b'ata miki rai ne yanzu ya fuskanci hukun ci .
Nan ma girgiza kai tayi alamar a'a
To mi ya saki kukane wai..
Cike da yarinta tace ni bana son zuwa patyn nan ...ni walahi ina jin tsoran shi kada ...se kuma tayi shiru...
Momy tace kada mi?fad'i mun mana ''ma fille'' ....mi Murad d'in yayi miki ne?
Yo ba d'azu damuna zowa ne kawai.....se kuma ta sake yin shiru tace shikenan ma Momy manta kawai bari nayi wanka..
Kan tace wani abu tuni ta shige tolet dan kada tasata dole ta gaya mata..
Batace komi ba itama ta fice a d'akin a ranta tace lallai Yarima yayi sa'ar mata ..tun ba'aje ko ina ba har tasan ta rufe sirrisu duda karanci shekarunta,....kai alhadulillah ..cike da nishad'i ta shiga part d'in sarki dan yau ita ke da girki...
Bayan ta fito aka fara cancad'a mata kwalliya ...wata dakyakiyar shadda fara ce dumki doguwar riga aka bata tasa aka kashe mata daurin dan kwali ...komi na jikin ta ''rouge'(ja) banda rigar kama daga d'an kunne takalmi etc...se dan mayafi me kama da net shima rouge ta yafa ...rigar dama daga sama ta dan matse se daga guiwar aka bude ta ....dukiyar fulanin da hips din nan sun fara fitowa dan bazaka bata su a shekarunta ba.....
Tubarikallah masha Allah abunda yan cikin dakin suke fadi ...inde har baka yiwa Maysam farin sani to baza ka tab'a ganewa ita ce ...Fans naso kuganta kukanku da se kun saki baki da hanci ...kuyangi se zuba mata kirari suke
Takwas saura suka fito ..lokacin kuwa su Murad sun jima suna jiran su....duda acikin masarautar ce za'ayi amman dayake abun nasune se amota za'a tafi ..
Zo kuga bakin ciki kiriri wurin Murza dan har kasa hakuri tayi ta cewa Maysam wly ina bakin cikin wannan auren kuma se nayi duk yanda zanyi na raba auren nan shegiya Mayya me kama da aljannu ..waya sanima ko diyar sarkin wani aljanin ce...ta bankad'e ta ta fice..
Itade Maysam idon wannan shine bata ce da ita komi ba ...se addu'ar neman tsari datayi ..
Ran Murad in yayi goma ya bace banda tsaki babu abunda yake dan ya tsani african time....
Gabanshi ne yayi wani mummunan faduwa sakamakon yin tozali dayayi da fuskar Maysam dake nufo so ...baki da hanci ya saki (kamar Halima da Samira sunga MIP .)ya zubawa sarautar Allah ido banda wata barakallahou fi.........babu abunda yake ambato wani abu yaji ya d'asu me a zuciya kafin ya lalibo yaji miye
Mahmud ya katse shi da fadin kallon ya isa haka kada idon su fad'o sanan yasa hannu ya rufe mishi baki...
Wani haushi ya ji ...Mazgewa yayi ya buga tsaki Mtssss to uban mi zan kallan a jikin yar kauyen ne ...
Shide Mahmud dariya yayi yace ashe shegen ka iya zab'e wannan kyau har haka gata kuma yarinya danya sharat haka ..amma kake wani basarwa kamar baka son auren..
B'ata fuska yayi yace ya ishe ka haka fa to..
Kafin yace wani abu su Maysam suka iso..
Mahmud ya fito ya bude mata baya inda Murad yake yace bismillah amarya
Tana d'ari2 ta shiga motar ya rufe ya zagawo ya shiga danshi ze tuka su..
Wani ni'imtaccen kamki shi ya daki hanci Murad besan lokacin daya lumshe ido ba .....
Itama hakan ta kasance a ban'agarenta a hankali ta bude baki zata gaishe shi gudun kada tayi laifi amma mi?
Wata jibgegiwar tsawa Murad ya daka mata yace d.....
Wash kuyi manaje da wannan..
Fasma
Ahmed Gumel
[8/17, 1:39 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:41 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 11 · 0% Book details