Sashe 39
Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ayanda muke ki kasa fada muna kina da aure... A tare sukace muna miki fatan alheri tare da zaman lfy me dorewa amman mu kinga tafiyar mu tunda de baki dauke mu ba da mahimmaci...suka tashi zasu tafi Da sauri tasha gaban su tana basu hakuri kan bata yi haka ba da wata manufa kawai de Allah ne beyi ba zasu ji ... Nan ta zaunar dasu ta basu tarihin rayuwar ta ...kan ta gama ,ita kuka su kuka ..nan suka rungume junan su ..sun jima a haka sannan Mahmud ya meda su gida ya kai Maysam airport ta dawo gida.. ,,,shugaban makaranta su Maysam ya kirayi iyayen su bayan yayi musu barka se kuma yayi musu proposing din a aje musu takardun su inda rabonsu gwamnati zata iya tura su kasar waje karatu... Da farko fulani bata amince ba amma ganin Maysam ta kwallafa rai yasa ta amince amma fa tace sede in England kusa da mijinta. Itade Maysam burin ta ta amincen ... Allah cikin ikonsa suka samu su duka ukkun kuma England duka aka tura su ....dadi kashe su ne kawai beyi ba ....zasu kara hadewa a makaranta daya.. Dan haka fulani tasake tutubar Mahmud da yasake koma wa England ya gani .ya kuma sanar mishi matarshi ta samu gwamnati ta turata England karatu.. Wannan karon Mahmud shi kanshi ya tsorata da lamarin ..dan Murad nunawa yayi da de duniya besan shi ba kwata2 ya manta dashi... haka Mahmud ya dawo zuciyarshi cunkushe da wasi2 iri2 .....shi be masan ta inda ze fara gayawa fulani cewa ga irin cin mutunci da Murad yayi mishi ba......dan haka tunda ya dawo ya shiga wasan buya da. Fulani.... Ranar wata litinin ana gobe tafiyar su Maysam England dan Mahmud ya cike mata takardun ta. Bangaren Abbanta ta nufa dan yi musu bankwana shida Murza sun jima Mallam Musa yana yi mata nasiha da kuma ta kare mutuncin ta da na aurenta ... duk sai jikinta yayi sanyi taji kamar ma ta daina tafiyar amman tuno wa da tayi yayan ta na can sai ta samu kwarin guiwa har zuciyarta tafara azzalzalata dan zumudi Dakin Murza ta nufa da niyar yimata ban kwana amma mi cak ta tsaya a dede kofar shiga palon banyi aune ba naga hawaye sun fara zarya a kumatunta cike da mamaki na matso na kara kunne na dan ji mi yasata kuka sai naji Murza tana waya tana fadin ee kadan ma suka gani wly ni nan zan zama ajalin Murad de Maysam (kuji fa da allah kamar ran a hannunta yake ) da ba ma rashin sa'a ba da yanzu sun dade da mutuwa ai..., ke nifa haukata shi naso ayi yabi duniya bama a raba shi ba da dangin ba fadar madina da ga bangaren layi , shewa Murza ta kwasa tace wannan shine target din mu na gaba sai kinyi uwar dakina shugaba Madina matar sarki shugaban masarauta gaba daya kai ko makirar Fulani ba ta isa ta taka miki birki ba dole ne ki taka wanda kikeso a garin nan dan duk wanda yayi miki kan kara za kiyi mishi ta itace abuga dake a barki anan waziri ma yayi nashi babin an shafe shi. Dafe kirjinta Maysam tayi cike da mamaki da kyar ta lallaba ta koma bangaren fulani dede zata shiga taji muryar Mahmud na fadiwa Fulani kaf abunda yafaru shida Murad, yakara da fadin amman fa ina ganin ba a hayyacin shi ba yake dan a gaskia wanan al'amari akwai ayar tambaya a ciki jim Fulani tayi tana jinjina maganar sai kawa Maysam ta fado ba ko sallama tana gwanjin kuka cinyar Fulani ta fada ta saki wani sabon kuka mai cin rai cike da tashin hankali fulani ke tambayarta miya faru .? kukan yakasa tsayawa ta shiga fadin Momy kada kiyi fushi da yayana ba laifin shi bane wly sune kuma sunce ma sai sunga bayan mu nida shi Cike da tsoro Fulani da Mahmud sukace suwa din? Yanzu nan naji Inna Murza tana waya da wata Madina matar sarki nan ta kwashe kaf abunda taji ta fada musu. Mahamud dey mamakine ya cika shi har yawun bakinshi ya kafe ya rasa mi zai fadi. Fulani batayi wani mamakiba dan dama bata yarda da tuban Murza ba kuma ta gane sare Madinar da take fadi sai tayi shiru. A fusace Mahmud ya tashi yana fadin kafin su kasheku ni bari nakashesu .. ,dakatar da shi fulani tayi da fadin zauna muyi magana Bayan ya zauna tayi mishi nasiha kan illar a bunda yake son aikata wa takara da fadin ''maintenant on a aucune preuve en notre disposition qui va prouver leur actes. . Mahmud ya ce''Mais Momy ,Maysam a tout entendu non?.'' Fulani ta sake fadin''Meme si elle a tout entendu c'est sa parole contre celle de Madina kuma ma babu wanda zai yarda saboda iya makircinta dan tana gwada kamar ta goya Murad gaban mutane in baka mantaba waziri ma fa yaka yafada amma babu wanda ya yarda .... Yanzu de mu fara da kubutar da Murad din daga baya se musan yanda zamu bullo musu....in su da adiri suka dogara to mu da Allah muka dogara Nan Mahmud ya bada shawarar ayi ta saukar qur'ani tare da zuwa makarantu su taya su da addu'a...ya kuma cewa muma kuma zamu rage bacci mu zanki rayashi da nafilfili da addu'a .. Sosai sukayi na'am da shawarar nan ..... Maysam tace Allah ya bamu nasara akansu..nima na samu Mijina ya dawo kusa dani..muyi.... Tsit tayi ganin irin kallon da suke mata .. Se lokaci ta tuna ashe fa a gaban Surikarta fulani take ..ai da gudu da shige kuryar daki tana dariya ga kunya kamar kasa ta nutse ta shige .. Dariya Mahmud ya shiga yi mata ... Fulani na fadin yaki dawo y'a ta ai bama yar haka dake... Amma ina Maysam ta ware .. .nan Mahmud yayi mata sallama tare da jaddada mata gobe2n nan zesaka a fara saukar alqur'ani..sanna ya fice. Fulani tabishi shi ma da addu’a dan a gaskiya samun aboki kamar Mahmud a yanzu se an tona.. A ranar su duka ukku baccin da sukayi kadan ne dan kwana sukayi suna rayashi da nafilfili da addu'a Allah ya basu nasara akan su Murza ya kubutar da Murad da ga sharrin su ... Love you all Yawan comment dinku shi ze bani kwarin guiwar yin typing me yawa Fasma ce