← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 67

Sashe 38

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🅿️ 77__78 *FASMA* _jinjinar ban girma Momyn Mufeedah ,ina tayaki murnar kammala littafinki hakika kin fadadakar da nishadan tar damu Allah yasa sakon da kike son isarwa ya isa ,Allah ya bamu ikon yin aiki da shi ke kuma Allah ya biyaki da mafificin alherinsa ,ya yafe miki kurakuran dake ciki.._ _Up.up.up muna tare dake se mun jiki a sabon littafin ki..._ *congratulation my lovely sis SARAH hakika ina tayaki murna samun Bac din ki Allah ya riqa ya sa ki amfana da* *shi ....ina me kara jinjina miki .* *Ban manta dake ba kanwata ta kai na Balkissa kema ina taya ki murna samun Bepc ki matuka Allah ya rika ya sanya alheri* ... *Kai da duk ma wanda suka zana jaraba wa ina muku murna tare da fatan alheri ..* *Wanda kuma ba su samu ba ne baissent pas les bras ,du courage and wish you bonne chance* .... _Ilou Ado Safaraou&Rabe Idi Salamatou Magaria ..les fausses jumelles ba ..ina jin dadin yanda kuke nuna kaunarku ga book din nan Allah ya bar kauna Maysam tace ta gaishe ku_ Dedicated to SARAH&BALKISSA 77__78 ```Manzon Allah(SAW)ya ce''Musulmi dan uwan Musulmi ne ,kada ya cutar dashi. Muslim ne ya rawaito shi``` . Murza na fita ta fada bangaren Madina ..bakin ciki kam kamar ta mutu take ji ... Tana zuwa ta fara zayyanawa Madina komi har da yar kwalar ta bakin rai .. Wata zabura Madina tayi tace what?dama suna waya amma bamu sani ba ... Tirkashi zancen dawowar shi ma bata taso ba kawai abun yi yanzu base gobe ba ki tashi yanzu ki koma wurin yankan wuka ki sanar mishi ..se kuma ki ce mishi ayi mishi asirin da ze manta da zuri'a tashi ma gaba daya ya yanke alakarshi da su ... Murza bata yi kasa a gwiwa ba ta tashi ta fice bayan Madina ta cika mata jaka da makundan kudi... A bangaren Maysam kuwa shagwaba wacce tafi ta Fulani ma take zuba ma Murad .. Shi kuma se lallabata yake kan tazo mishi koda vacance din nan ne.. Se lokaci ta sanar dashi cewa ai wani lecture za suyi dan za ayi musu tsalaken ss2 .. Shima nan ya tayata murna tare da yi mata fatan samun nasara ... Hira tayi dadi har take tambayar shi sunan likitar dayake aiki a can ... Sedayayi murmushi yace to keda ba zowa zakiyi ba miye na wani tambayya... Kukan shagwaba ta sakamishi ..... Dolen shi shi ya gaya mata kai harda adress din gidan dayake..... Sun jima suna waya cike da jin dadi ga shi kuma yace zezo cikin sati se murna ta hade mata biyu... . Murza ce tayi wani zaman dirshen a gaban boka Yankan wuka tana gaya mishi duk irin makircin da suke so ayi musu tare da kara jadda da cewa arabashi da famylin ma gaba daya .. Boka ya sheke da dariyar jin dadi yace kai ina jin dadin aikin ki ...raba d'a da iyayenshi abune ne dayake bamu matukar wahalar aiki bare ma Uwa ...amma dole muke jajir cewa muga irin wanna danyan aiki ya yi tasiri badan komi ba se dan mun san yanke zumunta ma bashida kyau ,,bare yanke alaka tsakani da iyaye. ....(kuji wani shedanci ) Dan haka muna bukatar kudi masu yawa dan asiya wa aljanan da zayi aiki jini ..,,kuma ma ba anan garin suke ba se an tafi wani gari wanda ake kira da''DOGON DOUTCHI''ake siyo su wato Aljana 'DOGUWA'....sune masu yin wannan aiki ba tare da an samu matsala ba....ya kwashe da wata dariyar hhhhhh... Murza se wani washe baki take tace kudi ba matsala bane inde bukata zata biya ...nan ta zube mishi su.. Cike da murna da kwarin guiwa ta koma gida dan Boka ya jaddada mata cewa baze taba dawowa ba..(jifa se kace shi keda ikon duniyar ..Allah de ya shirya in me shiryiwan ne) Lokacin da Madina taji bayanin boka ba karamar murna tayi ba tace Mulki ne de Murad baza ka taba hawanshi ba...saura shi kanshi sarkin ina nan zuwa lokaci kawai nake jira.... Wannan kenan . Washe gari Maysam tayi tafiyar ta Maradi karatu da zumar in Murad ya zo tasan de ze je ganinta tunda ya san tana school. Amman mi shiru kake ji kamar malan ya ci shirwa ...tun tana tammahani zowarshi har ta dena ...yau har watan su biyu .. Bayan ta dawo gida ne kafin su koma rentren Ss3 take yi wa Fulani mitar yayanta be zo ba .har yau Fulani ma dauriya kawai take yi...tana lallashin ta amma mamaki ne fal ranta ....da farko in tayi kira tana samun shi sede baya dagawa .,,kai daga baya ma wayar ta dena shiga.. Ta dau waya ta sake danna kiran shi amman kamar kullum bata shiga . Maysam kam zuciyar ta banda lugudan zut2 babu abunda take mata ..se kawai ta fashewa Fulani da kuka .. Da kyar itama ta nutsu ta shiga lallashinta .. Dama sati biyu ne zatayi ta koma school amma duk ta wani fige ta rame Fulani kam tana tausayin ta ..ganin abun na gaba yasa tace wa Sarki tana son zuwa England wurin Murad. Da kyar sarki ya lallabata da fadin bari Mahmud ya tafi ya gani.. Cikin satin Mahmud ya shirya ya daga se England ...lokacin da ya tafi akayi rashin sa'a Murad baya nan likitarsu ta tura su qarin karatu kasar Europe kan wata sabuwar cuta data shigowa kasar ..kuma formation din ze dauki 5_6 months.... Murad kam yana can yama manta da wasu wai su Fulani dan kuwa tun bayan kwana biyu dayin hirar shi da Maysam har ya fara shirye2 dawowa amma me kawai rana tsaka ya tsinci kanshi da son rashin dawowar . abun beyi nisa ba seda yaga Fulani tana kiran shi a waya amman ya kasa dauka...wani irin abu yake ji a zuciyar shi se kawai yama canza layi gaba daya ,,,kai da ga karshe ma dayaji tafiyar tura karin karatu se kawai ya saka sunan shi ama su son zuwa ..ya koyi sa'a aka tura sun.... haka nan Mahmud ya dawo ba dan ya so ba tun dade lfyr sa lau aiki ne kawai ya rikeshi...... To fa muje de zuwa Lokacin da Mahmud ya sanarwa da su Fulani se a sanan suka dan saki ransu .jin an turashi karatu ne .. Maysam ta koma Makaranta abunta . yanzu kam sun kara girma komi na cikar budurci ya bayyana a jikin su....se wani jiji da kai suke wai su yan matan Ss3 ...yanzu kam sun kara wayo Maysam yanzu bata da wani buri na ta ganta kusa da yayata Murad .. Ga karatu suke babu kama hannun yaro ... kullum su ke cinye ta daya ,biyu da ta ukku a ajin,,wannan abu ba karamar haushi yake bawa sauran dalibai ba dan ko wata competition se de a zaba cikin su ukku ...gaba daya kansu a hade sun shaku da junan su,,,class,diri ,kyau tsafta ,ilimi duk sun mallake su ..dan ko a islamiya ma kadan ya rage musu su sauke Alqur'ani....... Kullum zaka gansu cikin walwala da tsokanar junan ,,,har suke kiran kansu da tripleM.. . amman fa har zuwa lokacin su Mufeedah basu san cewa Maysam matar aure ce dan bata wani nuna musu alama ba...wani lokaci har sukan tsokane ta da fadin sun yi wa yayansu kamu .... Itade sede ta kallesu tayi dariya.. Bayan 6 months nan ma su fulani suka dinga diba hanyar ganin Murad amma ji kake shiru ...Fulani kullum cikin yi mishi addu'a take .. Maysam ma kam yanzu bata wani samun isheshen bacci,,,duk dare tana yawaita yin nafilfili da rokon Allah yayi musu zabi na alheri tare da karesu da duk wani me binsu da sharri mutum ko aljan.. Amma fa yanzu idonta ,kunnenta bakinta kai har ma gangar jikinta ba suda wani buri na su jisu tare da oga dan Murad ya rigaye ya koya ma ta sonshi ..dan haka ita da soyyayarshi ta girma cikin ranta ....mafi yawan cin lokaci zata dau photon shi ta saka gaba tana ta zance ita daya (umm su maysam an fada tarkon so ....sede lokaci ya kure miki .) . Tafiya tayi tafiya lokaci nata tafiya Bayan sunyi saukar Qur'ani da sati suka fara final exam .. Cikin ikon Allah suka gama lafiya suna jiran saka mako.. Gida ta dawo zaman jira..... Fulani na lura da ita tun dawowarta ta kaura bangaren Murad gashi da ka ganta kasan tana cikin damuwa ...fulani kam ba karami tausaya mata ba take..bz. Ana haka resulta din su Maysam ya fito ..gaba dayan sun ci harda mention exellente .. Zo kaga murna wajen su Harda wata yar kwarya kwarya walima suka shirya su ukkun ...acan gidan Maysam na Maradi akayi ta inda Mahmud ya taka rawar gani wurin yi musu komi dan ganin basu samu wata matsala ba..... Washe garin walimar su ukku suna ta hira Mariam tace yauwa dama akwai wata magana dana ke son yi muku.. Nan suka nutsu ta ce dama abbana nane yayi mun muji .. Wani ihu suka kwasa a tare suna fadi wai da gaske dan Allah .. Tace ee wly wani dan abokin shi ne sunan shi MA'ARUF. Kuma a England yake aiki docteur ne... murna fal ransu suka yi muta fatan alheri tare da fadin kice kawai da mun sha biki se England .. Mufeedah ma tace kai nima fa Maysam yayan nan naki ya fara damuna ,,..bakiga jiya daya kaini Super market siyan kayan damuka sa ....ya wani tsareni da surutu kai daga karshe ma seda yayi mun wayo na bashi number ta .. Maysam ta kwashe da dariya tace kawai kada kija wani aji inya nuna yana so kawai ki amince Mahmud bashi da wata makusa ,kyau ne ,kudi ne,kamala ce, duk ya hada kawai ki yarda musha biki.kemz.. Cike da zolaya Mariam tace kai kede kawai dan yana yayankine kike wani yabonshi .. Dariya tayi tace haba ba wani nan .gaskiya de na fada.kuma ma abokin MIJINA NE A tare sukace miji ... Tace ai koda na shigo makarantar nan da aurena ...kuma wannan wanda yazo lokacin da bani da lfy wato Yaya MURAD shine mijina...gidan nan ma nawa ne .. Mufeedah tace amman kin san baki kyauta ba ko ace
Chapter 38 · 0% Book details