← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 67

Sashe 45

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maysam har ta kai kofa tace pls ku shirya kayan mu duka gobe zamu koma din ....sannan pls ku dau lecture da kyau koda ban samu zuwa ba se ku koyamun ..kunsan mu matan aure se a hankali..

Mariam tace wai yaushe kika fitsare kanane abun naki ya fara ruko ido..

Mufeedah tace kede barta bamu iya mata jeki seda safen .....

Haka ta fice suna ta barkwan cinsu...

Tana zuwa sallama kawai tayi mishi tayi wani kikam..

Amsa sallamar yayi yace ke shigo mutafi.gida..

Tana tsayen tace nifa babu inda zani ..kuje can kuyi zamku kaida amariyar ka na barmata kai..na hakura gaskiya..nifa ina ga ma fasa karatun nan zanyi na koma can gida..

Yar dariya yayi yace kai da kuwa kin bada mata inba abinki ba wa kika taba ganin ta barwa kishiya Miji ...harda barin karatun da kikaci buri akanshi...

Shiru tayi mishi dan itama tirjine kawai bawai dan zata iya bar matan ba..ayanda take jinshi a kokon zuciyar nan tata ai sede amutu akanshi

Murad ya sake fadin shigo mana..inada abunyi fa.

Zaga yowa tayi ta shiga se wani turo baki gaba take...

Hanyar gidan shi ya kama ...ganin taki sakin jikinta yasa ya kamo hannunta ya gama dashi yana tukin..yana fadin kai uar gidan Momy mi take bakine haka kikayi sauri girma ne...

Wani mayan shok ya ziyarci Maysam tun lokacin daya dora hannunshi a nata...

A ranta tace inda bari na gwada wani abu na gani.. ..

Kamo hannunshi guda tayi ta shiga wasa dashi ...kawai beyi aune ba yaji tasa yatsarsa guda cikin bakinta....

Eee oga Murad kusan sakin sitiyarin yayi yace ke bakida hankali ne .

Maysam tace to ni minayi ne kawai dama mutum ba wani iya tuki yayi ba. ...sallon a yarda mutum bayan ni din yarinya ce me tsada...a ranta kuwa cewa tayi ashe de da gaske ne wanan abun yana aiki .ai kuwa wly nima sena gana ma zuciyarka wuya kamar yanda kake yiwa tawa yanzu..

Murad kuwa cewa yayi ina tsada anan bayan amariya ta ma ta fiki tsada ..kinga kuwa koba kya nan ina da wata amariya me tsafta ,aji,etc. A ranshi kuwa fadi yake ee fa nina san irin tsadar ki....yar renota

Itade shiru tayi mishi tana dariyar mugunta ita kade...

Suna isowa suka firfito ..gaba ya shige tana gunguni tabi bayan shi ..har suka shigo falon Murad yace kin kyauta ci gaba da zagina..

Wani waro ido tayi tace zagi fa kawai cewa nayi nide kasan yanda zakayi da matarka dan kada ta bari mu hudu da ita..wly dan sak yarinya tayi mun sena kareraya ta ..

Dama ya sako? bazata iya zaginshi ba kawai de yaji tana ambaton martarka shiyasa yayi mata haka ....yace kin ga nan ma bangarenta ne naki yana baya ..dan bata nan ne tayi tafiya se bayan kwana biyu zata dawo kinga seki zauna nan kan ta dawo kuma kafin nan an gyara miki naki bangaren kuma wanan umarni ne nake baki na ki zauna anan din dan bana son hayaniya...kuma ai dama taya ma za'ayi ki ganta matata ai me ganinta seni kade dan tsada gareta ga zubin zallar kyauu....

Tayi dariyar takaici tace really tana da kyau har hakane dakaketa yabonta ne..

Murad yace ai fadin irin zallar kyau nata ma bata baki ne..

Maysam a ranta tace bari kaji yanda nake jide daure fuska tayi tace ta kai SWEETBABYN KA kyau ne?

Tofa kunji wata tsokana ko?
Muje de zuwa
Ina yin ku 😍❤❤❤

Fasma ce 🖊yar mutan zinder
[9/11, 8:41 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/11, 8:50 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

Love you my fans irin more din nan❤😍😍

Dedicated to all my fans😍❤

🅿87__88

```Manzon Allah (SAW)yace''kada ku yawaita dariya domin yawaita dariya yana kashe zuciya
Bukhari ya rawaito shi.```

[05/08/18 à 12:37] Cak ya tsaya daga murmushin ma daya ke ..wani kollo ya shiga watsa mata yace..'comment oses tu ki gamata da Babyna ?ita din banza ,,,yo ko kafar SWEETBABYNA ta isa ta kamane..ke ke...ke maganar ta makale mishi ya ma kasa fadar komi ..kadan2 ya tunkaro ta .yana nunata da yatsa yace wly ko sunan ta naji kin sake fadi na lahira ma se ya fiki jin dadi ...

Maysam ta tsine fuska tana kalloshi se kuma tace ai kam yanzu na fara fadi sunan sweetba...
Daga hannu yayi da niyyar wanka mata mari ..

Wani kallo naga tayi mishi tare da marerecewa hakan yasa shi aje hannun shi babu shiri yace kinci darajar Momy wly fuuu..ya haye strain yana huci shikade a ranshi fadi yake yo koke da kike kama da aljanan baki kai ko rabin sweetbaby na ba...mtsssss

Ta dan jima nan tsaye se kuma ta shiga nema kitchen da kyar ta samu inda yake. Komi na bukata akwai aciki kama daga..har zata dafa wani abunci dan wata bala'in yuwa takeji. ..se kuma tayi dariya tace baride na bashi wahala bade ni yayiwa kishiya ba ..to ai shima ze dandana yaji...

Itama mara mishi baya tayi tana fadin wly dani kake zancen ..

Dakin dake kallon wanda ya shiga itama ta shiga ..ganin daki tsaf dashi komi a gyare agoge tsaf..bude wardrop tayi taga kayan mace acikin wani abu yazo ya tsaya mata amakogaro tace kenan de da gaske bangaren matarshi ne ya kawoni dan tamakar banida galihu awajenshi...

Duk seta ji bazata iya zama ma a dakin nan bare har ta kwana ciki ....
Tana ta wanin ya mutsa fuska da kyar ta shiga tolet tayi wanka tare da doro alwala ..jakar ta ta dauko ta saka rigar bacci wacce da kadan ta fice guiwa ..tayi shafe2n ta ..sannan ta fice a dakin ....

Direct dakin data ga ya shiga ta shiga babu ko sallama ..

Shikam lokacin fitowarshi a wanka kenan daga shi se towel ....

Maysam kallo daya ta mishi ta kauda kai direct gado ta hau ba tare datayi me magana ba...

Shikam yanzu tsoro ma take bashi..

Shima shirin shi yayi tsaf ya kwanta a dayan bangaren....batare dayace ufan ba

Can da kamar minti 20 cukin Maysam ya fara kukan yunwa kuuuu kuuu...
Tun tana daurewa har ta kasa nan ta fara kiran yaya ...yaya..

Yana jinta yayi mata shiru...
Tace pls yaya yunwa nakeji....
Nan ma shiru...

Nan tashiga shure2 tana fadin ita yunwa takeji tama meda abun waka

Yace ke wai bakiga dare yayi bane kije kichen ki dafa abunda kike so ki banni ni nayi bacci na

Dan galgal ta zauna bisa gadon ta shiga rera mishi kuka ita yuwa takeji.kuma ai shawarma take son ci yanzu

Ganin fa da gaske ba barinshi yayi bacci ba zatayi ya sa ya daka mata tsawa...

A memakon taji tsoranshi se kawai ta koma ta kwanta tare da rushewa da wani sabon kuka tana fadin yanzu da Momy ce da ta san yanda tayi dani ...ke koda su Mufeedah ne da sun tashi komin dare su girka min amman abunda nake so kawai an kawoni ne daman dan a azabtardani da yunwa..

Dafe kanshi yayi ..yarinyar nan fa ta fara caza mishi kai ..yace wai ke bakya ganin dare yayi ne kibari har zuwa safe mana..

Maysam tace nide a'a wly yunwa nakeji kamar naci babu..da kasan baza na kulawa dani ba donmi ka kawoni....
?

Babu shiri ya zari jallabiyarshi tare da key ya fita..ai kuwa mi Maysam zatayi in ba binshi ba.ta zaro hijab ta kuwa goge hawayen da dama na rigimane kawai...be lura da ita ba seda yazo fita a fallon ...ze kulleta tace a'a tsayani mana mutafi tare...

Kare mata kallo yayi hijab ne kawai ta dora a bisa rigar yace ke ina zaki kuma ....da. Wannan kayan kuma....

Kai tsaye tace rakiya kawai zanyi maka ...
Be kara cewa komi ba ya shiga motar itama tashiga ya tada me gadi ya bude musu suka fice....

A wani restaurant yayi paking ..yana kokarin fito wa yaga itama zata fito da sauri ya koma ya zaune tare da kama hannunta yace ke bakida hankali ne zaki fita ahaka ?
Turo dan bakin nan tayi tace wai komi se kace bani da hankali...

Kallonta yayi yace to inba rashin hankali ba ya za'ayi ki fita da wanna shigar mtsss ya ja tsuka..

Maysam tace inde har baka so na fita to kiss me ...sena hakura nayi zama na a mota ...kai ko masu ficewa ma bazan kalla ba..

Waro ido yayi yace wai ke yaushi kika fitsare ne haka...

Far tayi da ido batare da ta bashi amsa ba tace pls yunwar fa se karuwa take .kai kuma se wani bata min time kake..tayi tirjin kamar zata bude ta fita ..

Da sauri ya jawota ya shiga kissing din nata ..su oganniya Maysam har wani lumshe idanu take burinta ya cika dan ita kam da zaya ciro bakin ma ya bata da ta yarda ..sun dan dau lokaci sanna ya saketa..

Maysam tayi Murmushi tace kokai fa ...yanzu jeka ina nan bazan fitaba ..

Bece komi ba ya fita a ranshi kuma fadi yake wai taya akayi yarinyar nan ta fitsare haka.shi yasa fa bayason karatun turan nan..?(ni kuwa nace babu wani turai ai renon kace ...ko ka manta tun bata san sunan abunba ma kake mata shi ,,ka saba mata da dorata cinya a kowani time ..se yanzu dan tana ramawa kace baka san ya akayi ba ku jiye mun shi....🙄)

Ice cream ,shawarma,snake ne ya sayo musu ..da kuma gassasun kaji😋..dan gashin su yana yi mishi dadi

Suna dawo wa dan iya shege irin nata shawarma daya kawai taci se ice cream shima roba daya tace ya ishe ta ..

Murad yace kai amma yarinyar nan kin raina duniya .. ..yunwar kenann...

Oya sauko kice ya bude kajin.....kikam tayi tace bataci ..
Murad yace walahi baki isaba dole se kin ci.. ki sani na fita da daren nan amma ki ki ci...
🤣🤣wai fans kusan miya hana ta cin kajin ne?
Wai fa ita tsoro take ko na amarcinta ne shiyasa ma taki ci bayan ta hada miyanta..
Chapter 45 · 0% Book details