← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 67

Sashe 34

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

🅿️ 69__70
Story&Written
by
*FASMA*
*Ho.ho.ho MIMSQUEEN hamshakiyar shahararar marubuciyar ..ina murnar tayaki karasa littafin ''KARSHEN ALEWA KASA ''hakika kin nishadan tar damu kin fadakar damu ..Rabbi ya kara miki daukaka .da Baseera tare da zakin hannu ..sosai muka ji dadin littafin nan Readers kada kubari abaku labari ...zamuyi missing dinshi ..Amma abun murna da farin ciki shine muna nan tare dake a KALAR TAWA UWAR wanda shima ya dauko dadi and other dazasu biyo baya..muna biye dake ..love you irin totaly din nan.*
Dedicated to all my fans
69__70
```Manzon Allah (SAW) yace''kauracewar musulmi da dan uwansa musulmi kamar zubar da jininsa ne''
Ahmad ya rawaito shi``` .
Hakan kuwa akayi Madina tasa akayi mata Kiran waziri ...dede kofar shiga falon ta kuwa barbada maganin ,,,,da farko yaso yaki zuwa amman ganin in betafi ba zata iya kulla mishi wani sharrin yasa ya tafi amma a ranshi fadi yake komi za'ayi sede ayi amma bazan biye mata ba kan auren nan ...tunda aka zuba maganin aka hana kowa shigowa bare fita ....bakam2 waziri ya shigo babu wata bismillah sallamar ma se da ya tsallaka har ya tura kanshi sanan yayi ta ...(a raina nace ai kuwa hakan be dace ba kana namiji ke koma macen ..wai se ka tura kai cikin falon mutum tukon zakayi sallama..kasan a wani hali zaka tarar dashi..ne... Ko dayake may be daga wazirin har Madina basu karanci hadisin ma'aiki SAW daya ke cewa''baya hallata ga musulmi ya leka gidan ko dakin wani ba tare da izini ba..Bukhari ya rawaiti shi....
...kuma ai ita madina ta sake mishi fuska har haka)
tunda ya shigo yaji jikin shi ya saki haka ya karaso ya zauna ..
Madina ta shiga tsarashi cike da makirci da nuna cewa komi ya fice a wajenta har da nuna jin
Dadin ta ga wanna auren koma ta na goyon bayan shi kan abunda yayi
Wai shi me diya ..se kawai ya saki jiki da ita nan ya shiga ga zayyana mata yanda auran ze gudana ...
Madina daga kasa se dariyar mugunta take mishi kai daga karshe ma tace ta dau nauyin kayan dakin amariya ...
Abunda ya kara tunzura waziri da yarda da ita ....kamar gaske tasa aka kawo mishi lemo . abunka ga wanda murna ta cika shi ya ma manta da Madina ce matar Sarki ...Kawai be kawo komi ba ya bude cikinshi ya kwankwadi lemun shi .....yana gamawa sega kiran wayarshi ya shigo ...Maheeba ce da sauri wai yazo zasu kara tattauna wa ya fita tare da yi mata sallama ...
Yana fita Madina tayi wata makirar dariya tace dani kake zancen ...
A bangaren su Fulani kuwa ita da Sarki suna zaune suna hirar su dan tunda akayi maganar auren Murad da Maheeba ya sa Madina ta dena shigowa .akai2 ...suna tsaka da hirar Fulani tace daman akwai wata magana dana ke son muyi akan auren nan ...a gaskiya yanzu bana goyon bayan auren nan kai hasali ma nifa ban masan yanda akayi na amince ba ba ...kuma ....jiya da dare kawai nayi wani mummunan mafarki kan auren nan ...nide gaskiya a fasa tunda de ko kati ba'a buga ba bare ace garin yasan mi ake ciki ...kuma ko jiya jiya nan da safe babu irin magiyar da be munba ...kasan kuwa har kwantar da shi akayi a england ciwonshi yayi wani mummunan tashi Allah de kawai yasa da sauran kwanakin shi nan gaba ...da yanzu mun ras ...se kawai ta kasa karasa kuka yaci karfinta ..
Sarki ma hankalin shi ba karamin tashi yayi ba ..yace nima de kin sosa mun inda yake mun k'ayk'ay dan har ga Allah bazan ce ga yanda abu ya faru ba kawai de na tsinci kaina nane da amincewar auren ....amma yanzu kirawo mun shi a waya shi Murad din muji ta bakinshi...
Kallon lokaci tayi taga goma har gifta amma dayake maganar me mahim manci ce yasa kawai ta danna mishi kiran ...
Lokaci kuwa yana bangarenshi shi da Maysam se shagwaba take zuba mishi kan seya kaita shopping gobe Se burgima take ajikin shi duk ta yakuna mishi kaya..
.shi kuwa ya kyaleta ne dan yasan yanzu babu idan zashi dare ne ...kuma shi badan baze iya kaita bane a'a kawai futar ce ma baya son yi kwata2 dan baya son ya gamu da wani ma Wanda ya san zancen wannan aure ...
Suna haka kiran ya shigo shiit yace da ita ya dau kiran da sauri ganin lokaci ya san ''quelque chose ne va pas'' lamo tayi a jikin shi tana jira ya gama ta cigaba daga inda ta tsaya....
Cike da ladabi ya dauka ya gaishe da fulanin..
Bayan ta amsa tace ya zo nan fada dadyshi yana son ganin shi ....
Da sauri Maysam ta shiga ta dauko mishi wata riga .jin Sarki nason ganinshi ...kuma be kamata ya fita da rigar nan haka ba..
..lokacin data dauko har yakai kofar fita dan sauri..
..
Itama Da sauri tace yaya tsaya..
Ya tsaya tare da juyowa yana fadin minene kuma cikin fada....
Turo baki tayi tace to ba riga na kawo maka ka sauya ba..
Shi se lokacin ya tuna da rigarshi ashe duk ta yakune se kuma jikin shi yayi sanyi gani tayi fushi...karba yayi ya saka ita kuwa ta anshi waccar din tayi shigewarta wai ita nan tayi fushi...
Girgiza kai yayi ya fice dan lokacin bashi da time din biye mata...
Su biyu ne palon kamar yanda ya zata nan ya kwashi gaisuwa wajen dady ...
Sarki ya ansa cikin sakin fuska ...se kuma yace dama game da zancen auren ka ne yasa nayi kiran ka
Kafin ma yaji mi za'ace ya shiga bawa Sarki hakuri kan shifa baya son auren nan hasalima auren dole ne ake shirin yi mishi har da yar kwallarshi....
Sarki yayi jim yana kallonshi..can yace to dama dan mujine ta bakin ka ..tunda baka so baza ayi ba ..kana iya tafiya...
Nan kuma hankali shi ya tashi dan jiyake ko yayi fushi ne...ya shiga bada hakuri ..
Sarki yace a'a daman muna da niyyar fasawa ..to mun tambayaka ne dan kada aje ko ka fara sonta...
Da sauri ya kalle shi yace ..so..?fa Dady ai ni so daya kawai nayi Shima wa SWEETBABYNA.
Fulani tayi dariya a ranta tace ita kuwa Maysam din fa...kayi ka gama mude idone namu ..
Sarki yace to shikenan kana iya tafiya Allah yayi maka albarka . .
Nan fa kawai ya rumgume Sarki yana zuba godiya harda kwalar murna ...
Fulani ma ta shafi kanshi tace hankali ya kwanta ko....
Cike da farin ciki ya fice ...
Sarki ya kalli fulani yace wai ashe har haka yake kin auren nan jibi fa ko lokacin auren shi da Maysam be nuna kin amincewarshi ba haka..
Fulani tace ashede da mun cutar da dan mu da kanmu ...
Sarki yace Allah ya kara tsare mu tare da yi muna zabi na alheri aduk lamuran mu
Ameen fulani ta amsa .
Wani sauri ya ringa zunkudawa kamar wanda ze tashi sama ..
Yana zuwa ya ma manta cewa Maysam tayi hushi dashi kawai tana zaune se ji tayi yayi sama da ita yana juyi ..
Itade tana mamakin miyasa ka shi murna haka take ..
Yana sauke ta yace ''devine quoi? ''(Ci aruwa?)
Tana turo baki tayi kalar tunani ...tace na baka gari
Yace to an fasa aurena da Maheeba ....
Be gama fada bama tayi wani uban tsalle me game da ihu ta dare bisan shi tana me jin dadin wannan abun...
Nan fa dadi kamar ya kashe su ...ya kirayi Mahmud ya sanar mishi ...
Shima ba karamar murna yayi ba .
Murad yace ki shirya gobe mufita yawo ba shopping kade ba ....
E fa murna ta gamewa Maysam bibiyu ...
Can yace ta tashi ya rakata bangaren fulani ..
Nan Maysam tace bata san zancen ba ..kawai dan yayi mata wayo ne yayi tafiyarshi shi kade ya barta... ji wani shirme....
Be hanata ba ... Ta shige dakinta na nan bangaren tayi wanka tasaka kayan baccin ta ..ta feshe jikinta da turare kamar yanda fulani ta koya mata ta nufi dakin Murad ...shi lokaci har ya kwanta tazo ta makalkale shi wai ita tsoro take ji be cema komi ba ya gyara mata kwanciya ...duk da har yau inde sun samu contact body tofa se yaji electric shok din nan sede yanzu ba sosai ba.....
Cikin dare biyu na dare Murad ya raba jikin shi da shimfidar ya doro alwala ya shiga nafilfili da addu'oi da godewa Allah kan wannan sauyi lamari daya samu .yasan daman addu'a bata faduwa kasa ..ko ba dade ko bajima ...
Wajejan uku na dare itama Maysam ganin shi yana salla yasa ta tashi ta doro alwala ta shiga nafila .
Ba su suka kwanta ba se bayan sunyi sallar asuba tare da yin azkar dinsu ....ta kuwa kara shige mishi jiki..bacci me dadi ya a won gaba da su
Wayewar gari lfy Maysam et Murad...
Ina masoyan Maysam ku fito mu ganku. To ..
Mi ye makomar Waziri da iyanlanshi ?kuma
Ina yinku irin totaly din nan
Fasma ce
Chapter 34 · 0% Book details