← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 67

Sashe 61

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan ina tare dake bana bukatar wani abinci dan na rayu..na saka ki kade ma a gaba ina kallon ya isheni ........kamota yayi suka zauna bakin bed ya dorata cinyarshi ko nauyinta ma bejiba.....yace '' je t'aime a la folie ma princesse d'amour...ma bouche ne peut pas dire a quel point je t'aime ni mon corps ne peut pas l'exprimer .ni mon cerveau et mon coeur ne peuvent pas compter a quel point tu compte pour moi...tout ce que je sais est que je ne peux pas vivre sans toi ..sans toi ma vie n'est rien ...''
My repiration ''je ne vis que pour toi ..si tu me quitte un jour ca sera le jour de mort j'en suis sure ma douce dulcinée ''

Ya kamo hannuta ya dora a setin zuciyar shi yace dama rabi ce to ina me tabbatar miki duk ranar da kika barni to nima a ranar za'a dauki gawata. .....''sache bien que ma vie ne depend que de toi.....je place ma vie entre tes mains..je compte sur toi pour ne pas la perdre...

Maysam kam tunda ya fara magana taji kanta ya kara girma ..gaba daya se taji kamar tafi kowa yin sa'ar miji a rayuwa ....idanunta banda hawaye dadi babu abunda suke ..duk setaji babu ya ita a duniarnan ....zuciyarta wasai takeji

Tace Mon bb cheri.ina kataba jin mutumin da yayi wasa da rayuwar shi ne ..idande har zan rasaka to kamar na rasa rayuwa tane .. ..ko mutuwa ina addu'ar idan tazo ta fara daukana dan nasan inde har kai ta fara dauka to kuwa ina me tabbatar maka da nima a ranar zan bika dan rayuwata batada wani anfani inde har baka cikin ta..son dan kemaka ya fice amisalta shi ''tu es ma raison de vivre''i love you more mijina

Da sauri ya rufe mata baki yace haba kibar zancan mutuwa in har muna tare dake..ya zaki kirawo mana ita

Dan murmushi tayi tace haba ''Autan maza '' ai ita mutuwa tana wuyan. ..kamata yayi duk wani musulmi munmuni ya dinga tunawa da ita akai2 akoda yaushe dan ita dole ce komin dadewa ..

nan fa suka shiga zuba wa juna kalaman soyyaya wanda ya karasa Murad jin shima fa wani ne ...bama da inta kirashi da 'Autan maza ba ..(😝ko ba haka ba my kawali rams😜. )Se yaji kanshi yayi wani kara girma ..nan suka lalace da kalanmansu...daga nan kuma ogan niya ta shiga mishi kalon nata pratical din da ta kara koyo ko tulelen cikinta be hanata yiba ..nace tab yarinyar nan tayi nisa bata jin kira . daman an jima ba'a jiba .kun sani ai nan naja musu kofar .kawai nayi gaba abuna.

Washe gari cike da farin ciki da annashuwa suka tashi ..
Har tara na safe sunan nan dakin sun kasa fitowa gaba daya ya dabaibaye ta kuma gashi ya kulle kofar...seda ta fara mishi kukan shagwaba kan ita yunwa take ji sannan ya sarara mata yace to mikike son ci yanzu na saka akawo miki shi. ..

Turo baki tayi cike da sangarta tace ni farfesun kayan cike nake son ci kuma kai nake so ka girka min ..

Wani waro ido yayi yace ni kuma. Yana nuna kanshi. ..

Noding din kanta tayi ta kuwa shagwabe fuska kiris take jira ta saki kuka..

Zama yayi ya dorata cinyarshi yace wify kin gane ni ko kunna gaz ma ban iya ba bare aje ga zancen farfesu ...

Ai kuwa bata bari ma ya gama ba ta bare baki ta shiga rera bishi kuka wanda daga ji kasan na jin dadin rayuwane..kawai

Shi kuwa ya lalace wurin lallashi . da kyar ya shawo kanta tare da cewa to sutafi can bangaren su se ya shiga kitchen din ya dafa mata yanzu nan yana shiga ze zama abun fadin cewa ga yarima me jiran gado can yana dafa abinci da kanshi . kinga kuma da bayi birjik zasu renani ne..

Hawayen ta goge tace shikenan to mutafi dan yau girkinka nakeson ci ....

Suna fitowa suka tarar da fulani a nan falon tana kallon tv...da dan sauri Maysam ta nufeta ..Murad kuwa se fadi yake kibi a hankali fa...

Har kasa ta duka dan gaishe da fulani da kyar ma ta dukan.
Fulani bayan ta amsa tace mata way ni Maysam bakya tausayin kanki ne kina cikin watan ki fa na takwas inake ina dukawa mafarin ki kasa tashi kisa mijinki ya daureni dan naga akan cikin nan komi ze iya yi cike da zolaya take maganar..

Gaba dayan su suka kwashe da dariya Maysam tace tab ai sede ya dauremu gaba daya dan kafarki kafata ......

Murad yana turo baki yace lovely wife mutafi mana kinga bakici komi ba kada ulcer yakamin ke da little babyna ....

Tab ai kam ba karamar kunya Maysam taji ba har jitake dama kasa ta tsage ta shige ...kanta a kasa ta kyaleshi ..

Ganin haka yasa yaje ya tallabota ta mike ai kan kace mi harta fice a palon tayi sid din su ..

Murad kam dariya ya shiga yi mata ..

Fulani tace bason haka fa kaga kasa dauther na taji kunyata ko .. ..

Murad yace to ni Momy minayi kuma kawai de ...

Kafin ya karasa tace jeka kada yunwar ta shige maka ita ..

Da dan saurinshi kuwa ya fice yana fadin haka ne.. fa

Fulani ta girgiza kai cike da farin ciki a ranta tace inde Murad ne zeyi rashin ta idon nan fiye da haka ma ..dan kuwa tun be girma haka ba bayajin kunyar kowa inde akan nuna soyyayar sweetbabyn shi ce sede kai da ake abun agabanka kaji kunyar.....

Sekuma tace Allah yaji kanki '' *MUNIRA''* ya rahamceki...(🤔🤔daman sunnan Sweetbaby *MUNIRA* kenan mujede zuwa...)

A kitchen ya tarar da ita se hada zufa take rumgumeta yayi ta baya yana shafa cikinta yace pls zoki zauna banason kina ba kanki wahala haka bayan Allah ya yaye miki ita ...duk abunda kike so kisaka bayi su miki ....

Kashe gaz din tayi dan ta gama abunda zatayi tana kallonshi tace nasan da haka aman jifa ta shafa dede wuyan shi tace yanda ka rame gaba daya ..nasan kuma harda rashin cin abinci dan kasha fada yanzu baka iya cin abinci inde har ba na Momy bane ko nawa .. ...ka barni na maka ''hangandi''(cin abinci dan yin kiba)kafin birtday dinka dan kada aga ban iya kiyo ba cike da zolaya ta karasa maganar...

Lakice mata hanci yayi yace tab ai ni kade nason iya kware warki wajen kiyo ai ko se yayi mata rada akunne wanda banjiyo mi yace mata ba yace shi kade ma ya isheni na kiyu .har na ginu..

Kirjinshi ta kaima bugun wasa tace kai ko ..ka jika da wata magana kuma ...

Ze kara wata magana tace pls yaya ni yunwa nakeji sosai da sosai fa..

Sorry yace tare da daukan kullar abinci data dafa suka fito gaba da baya ta rike kugu shi kuma rike da kullar dan gaba daya ya kore kuyangin bangaren dan acewar shi babu wanda zega shigar shi kitchen yana dafa abinci. . kuma yanzu baza ma su kara shigowa in ba aikin goge na share na safe se kuma in an kira su

Kallonta yake cike da tausayi yanda take tafiya yace aman wife cikin nan yayi miki kyau ba kadan ba ..

Murmushi kawai tayi ..a kasa suka zauna yanaci yana kuma bata a baki ..

Murad yace yauwa yama zancen birtday din nan ne ko kin fasa..

Tana kallonshi tace tana nan ya akayi ne...

Yar dariya yayi yace daman parent din Sweetbaby ne zasu zo kin san tunda akayi auren mu basu zo ba kuma dady ma yaso zowarsu lokacin bikin aman yanayi ciwonta be basu damar zowa ba ...kuma wani rashin sa'a lokacin sukazo kina england shi yasa yanzu sukacece zasu zo kodan su ganki...

Tunda ya fara magana taji gabanta na faduwa ..bayan ya gama tace Allah ya kawosu lfy yaushene zasu zo..
Inaga de ana gobe birtday din ....sukaci gaba dacin abincin su..

Can yace gaskiya wife Allah yayi miki ni'imomi iri daban2 ciki harda ta iya lafiyayen girki..

Tunda ya fara magana ta bata rai har ya gama...

Cike da kulawa yayi kalar tausayi yace mi kuma nayi my honey..

Kicin2 tayi da fuska harda yar kwallarta ta kissa tace to ni ni .se kuma tayi shiru...

Gaba daya yaji shima kwallar na famar cike mishi ido yace only one kada ki bari hawayen nan su zuba dan dede suke da sukar mashi a zuciyana...yace fadi mun miye matsalar ki ..

Bata bari suka zuboba tace to bakai bane..

Cike da rudu yace ni kuma minayi ..

Cike da shirme tace to ai naji baka taba kirana da sunana ba ...kullum sede ka kirkiro wani suna bayan ni kuma ina son jin sunana ya fito daga bakinka dan na banbantashi dana sauran mutane..kuma na lura dakai duk lokacin dana kiraka da babyna seka lumshe ido tana wani turo baki..

Seda ya sauke ajiyar zuciya dan da hankalinshi ya tashi yace sorry baby ..inada dalilina nakin fadin sunanki ..hakane kina da gaskiya aman ki mun hakuri dan sunan yana mun nauyi a bakina ne..

Cike da mamaki da al ajabi jin abunda ya fada tace why ?kozan iya sani

..yana kallonta da kamar baze ce komi ba se kuma ya daure ya cize yace Sunan BABYna shine lakanin da My Sweetbaby ta mun aduk lokacin da kika kirani da sunan ina jine kamar itace ta kira..kuma abunda yasa ban taba kiranki da sunanki ba because ''tu as le meme nom que my ,SWEETBABY''(you have the same nam of my sweetbaby) itama MAYSAM ake kiranta dashi ....to bani ba ko wani naji ya kira sunan se gabana ya fadi dan duk gani nake kamar ita zan gani dana ji sunan ....lokacin da Momy ta fara gaya mun sunanki seda nayi three days ina jinya da.zuciyata...ina son Sweetbaby ta kasance itace rabin zuciyana...aman am sorry idan kinji haushi.....
Chapter 61 · 0% Book details