← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 67

Sashe 47

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake yan tsubucce2 yayi yace ita kam wannan tama fishi sammun kariya dan ta rike addu'oi baza mu iya yi......ganin irin kallon da Murza ke mishi irin kallon nan ne na in bazaka iya ba kawai bari na nemi wani....a ranshi yace wannan fa batada mutunci yanzu seta tafi abunta batare da taban komi ba ...amma bari na mata irin ta mu ta yan iskan gari..

Wata dariya ya kwashe da ita lokacin har tana batun tafiyarta jin bukatar ta bazata biya ba gwara ta nemi wani gun..

Yace koma ki zauna aikin ze yiwu amma za'a kashe makkudan kudi dan wannan aiki ja ne..

Washe baki tayi tace yanzu naji zance me dadi.....to ina jinka..

Wani turare ya bata cikin kwalba yace gashi wanna asan yanda za'ayi ya shaki kamshi nan ..to ina tabbatar miki yana shaka kamshi ze gusar mishi hankali...sede wani ba shiba...

Murza jitake kamar tayi fiffike ta ganta a wurin Madina ta sheda mata wannan daddan labari .......

Tana fita bokan ya kwashe da dariya yace zaku san dani kuke aiki ... Ba'ataba kawo min aikin danaga bazanyi nasara ba se wannan .kawai har kunsa na fara ji akwai abunda ze gagaren a duniyar nan..hhhh..

Yayi wani kirarin shi can kuma yace se kai dan hatsabibi ka bita kawai tana fito da turaren ka kwabeshi ya zube sanna ka bayyana siffarka ga wanda duk ya shaki turaren nan dan suyi hauka me degree kowama ya huta..dan in shi Murad din ne babu abunda zeyi mishi ..ni kuma bazanyi asarar turaren nan ba...fuuuu ya fice dan cika umarni..

Tana zuwa direct bangaren Madinar ta fice bakin nan se wageshi take ...
Madina tace da alamade anyi nasara yau..

Murza tace kwarai kuwa dan kinga ma abunda ya bani ta fito da turaren zatayi wa Madina bayani ai kuwa Hatsabibi ya kwabeshi kwalba ta tarwatse a kasa turare ya zube anan..

Wani waro ido Murza tayi se kuma ta dauke numpashinta a million ta bar bangaren Madina dan ita tasan hukuncin wannan turaren...

Ko iida fita daga palon batayi ba taji Madina ta kwalla wani uban ihu e kuwa se takara gudun ta har seda ta fita tukon ta dedeta nutsuwarta dan kar wani ya ganta.....gidanta ta shiga can kuryar daki har da saka sakata. . jikinta banda karkarwa babu abunda yake..kamar ace mata ke ta arce se wani waware ido take.....

A bangaren Madina kuwa hauka turben takeyi kuyangi duk sunyi cirko2 a kofar dakin dan kana shiga inta damke babu me rabaka da ita dukan kawai zatayi ta lakada maka duk abunda ta rarima buga maka zatayi ..ga dariya ka-ka-ka tana fadin nice nan ajalinshi kamar yanda na zama ajalin dan uwanka da sweetbabyn ka..da waziri hhh

Walahi yau sena kashe ka ..tun kana cikin zanin goyo nake bibiyar rayuwar amma kaki mutuwa to yau sede wani ba kai ba..
Lokacin labari har ya isa ga sarki dama suna zaune ne a fada harda Musa da Murad.dakula Mahmud .ai kuwa a tare suka shigo fulani ma isowarta kenan..sukaji tana tonawa kanta asiri ..kaf makircin datayi seda ta fadeshi yau .gaba daya aka dauki kabbara tare da da fadin inna lillahi wa inna ileyhi rajou'oun.......Malam Musa duk jikinshi yayi sanyi jin harda Diyar Maysam a harinta amma se ya shiga yiwa Allah godiya daya kubutar mishi da ita....

Fulani kam har ta fara hawaye jin itace ta kashe mata danta data haifa na Fari wato yayan Murad wanda ko sunanshi ba'ayi ba ya mutu ......kasa tsayawa tayi ta koma bangarenta cike da tausayin kanta da kuma tausayin Madina jin irin rayuwar data saka kanta saboda kishi kawai.....

Murad nan ya zube ya shiga rera kuka jin da sa hannunta ya rasa rabin zuciyarshi ...,,,Mahmud ya rumgumeshu yana bashi baki tare da yi mishi yar nasiha..da kyar ya tsagaita ya rakashi har bangaren shi....

Ganin abun kara gaba yake Sarki yasa akayi mata allurar bacci shima iya tashin hankali ya shiga jin ita ta kashe mishi dan shi na fari ...ba dan yana kumyar mahaifanta ba da shi kade yansan irin hukunci da zeyi mata ..to mahaifinta sarkin garin Diffa ne duk da yanzu ya tsufa ya barwa danshi na fari to amman akwai alkunya a tsakanin su ...akwai mutunci ...dan haka ya daga waya ya sanar mishi komi ....
Mahaifinta dantakon arziki kawai cewa yayi a mata hukunci dede da abunda ta aikata ... ..

Sarki Mustapha ya roki alfarma kawai da za'akowa ta nan de..

Da kyar mahaifinta ya aminci ..aka kuwa kara mata wata allurar bacci aka sakata a jirgi han se Diffa....
Ayya munai miki bankwanan se wata rana 🤗wannan shine ake kira da kaykayi koma kan mashe kiya ..tana fatan haukata Murad gashi ta haukace ita din ...to hattara de Inna Murza abi duniyar nan a sannu .. saura ke..

'Muje de zuwa..

🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Wunin ranar babu wanda yayi shi cikin jin da dadi kowa yana jimamin abunda Madina ta aikata ..bama kamar wanda tayi wa abunba....danshi Murad ciwon shi ma yake son tashi..

Har dare Murad be kirayi Maysam ba......karfe takwas na dare ya tuna da ita har ya danna kiranta se kuma ya tuna yanzu biyu na darene acan ..har ze kashe ya ji ta daga.kiran..

Da kuka tayi mishi sallama ..seda ya sauke ajiyar zuciya yace mi kuma akayi ne kiyi shiru ki fada mun

..jin murya shi wani iri yasa tayi shiru tace yaya mi ya sameka ne bakada lfy naji muryarka wani iri..

Ya ce mata banida lfy ciwona yake son farmini ...

Wani waro ido tayi tace inna lillahi wa.....garin ya ? I mean mi ya tado maka da shi ne ..?.kamar zatayi kuka take mishi tambayar...

Da kamar baze fada mata ba se kuma ya gaya mata duk abunda ya faru yau....

Banda inna lillahi wa ... Babu abunda take fadi Duk jikinta se yayi sanyi tama rasa abunda zatace mishi ..se kawai ta fashe mishi da kuka..

Shima cikin sanyi yace haba dami kike so naji ne da ciwon dake damuna koda kukan ki ne..dan har cikin ranshi yake jin kukan nata..

Shiru tayi tana ajiyar zuciya tayi matukar tausaya mishi ..nan ta dedeta nutsuwar ta shiga yi mishi nasiha tare da kallamai masu sanyaya zuciya ......
A ranshi yace kenan de yarinyar nan ta iya kwantar da hankali dan A kashi dari yaji kashi 40 na damuwar ya rage mishi ...yace yanzu fa biyu na dare ne ki kwanta kiyi bacci kinga gobe akwai school kada ki makara...

Tace to naji amma pls kaci wani abu kafin ka kwanta dan nasan wunin ranar nan da kyar ne inka ci wani abun ..pls promise me zakaci sannan kasha maganin ka

Promise kawai yace mata....

Nan ya kashe wayar ...babu laifin ya dan ji karfin jikin shi kadan..

Tana saukawa da zumar shan koda tea ne dan itama kusan wunin yunwar tayi da kawai be kirata ba ..ga mamakinta ta tarar da Mufeedah suna hirar itada Mahmud.a waya.zama tayi tare da fadin pls kice mishi dare yayi anan gobe akwai school sannan kuma ya tafi ya kular min da mijina baya jin dadi yanzu ...

Duk abunda take fadi Mahmud na jinta sarai ..a hand free Mufeedah ta saka wayar yace to masu miji naji kada ki damu zan kula miki da shi ...

Babu ko kunya tace kai aman fa na gode nima kam zan kula maka data ajiyar ta nan.. . .
Se kuma ta jajanta mishi abunda ya faru ..daga baya sukayi sallama...

Tea tasha ta haye sama dakin Murad abunta.dan har yau taki ta koma dakin wanda take ganin na kishiyarta ne..
🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
A bangaren Murza kam jin asirin ta be tonu ba yasa ta saki jikin ta kamar bata san komi ba ..sede kallo daya zakayi mata kasan tana cikin damuwa ..duk gani take itama haukacewar zatayi....fita ma kam yanzu ya gagareta kullum kunshe cikin daki ..abun har mamaki ya koma bawa M.Musa sede beyi mata magana ba.

🌹🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹

Satin shi biyu ya fara shirye2 komawarshi ..sarki da fulani suka sakashi gaba suna yi mishi nasiha dan tunda abun ya faru mutawar sweetbaby ta dawo mishi sabuwa abu kadan se ya fara zazzaga fada ...

Fulani tace kuma wly in kasan hantarar y'ata zakayi to tun wuri ka medasu hostel dinsu ..dan kada fadan nan naka ya hanata karatu..

To kawai yace aman a ranshi cewa yayi da kinsan abunda yake faruwa da bakiyi wannan maganar ba...
Shi fa komin bacin ran da yake ciki komin fadan dayake yi inde kiran wayarta kade ma ya shigo to se yaji zuciyarshi ta sauko ..in har suna waya kusan mantawa ma yake dayana da damuwa bare inyana tsokanar ta ita kuma tana sauke mishi kwandon shagwaba..se yaji ya tafi ...ko tafiyar nan surprise ce ze mata kuma gashi ta matsa mishi da yaushe ze dawo ne..

Haka suka mishi fada da nasiha shide da to yake amsawa tare da ban hakuri...karfe goma jirginshi ya daga se England. ✈
..safe a good journey

To nima bari na daga haka nan ....

Muje zuwa fans

Love you all❤😍

Fasma ce🖊(Yar mutan Zinder)
[9/11, 8:51 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/13, 9:49 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

*Kuyi hakuri na rashin jina kwana biyu*

Dedicated to all my fans😍❤

🅿91__92

```Manzon Allah(SAW) yace '' wanda baya roko a wajen Allah to Allah yana fushi dashi.
Bukhari ne ya rawaito shi.
```
Chapter 47 · 0% Book details