← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 67

Sashe 14

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

🅿️ 30__31
*Ina maqiyan Murza ku fito wannan page* *din takuce .....ku fito ku kwashi shoki fa ....lol..*
*Ban manta dake ba my dear Hadjara* ( *Arfat.)..ina godiya da qaunarki Allah* *ya bar qauna da dankon zumunci...ina yinki sosai ...* *littafinki "AMEMAH " yana wuta gaskiya* *yana fadakardamu da nishadantar damu Allah ya* *qara basira da zakin hannu Fans kada kubari a baku labarin* *littafin Amemah dan gaskiya ya hadu sosai*
Dedicated to all my fans
31--32
```Manzon Allah(SAW) ya ce "wanda duk ya yarda da cewa ALLAH shi ne Ubangiji,ya yarda musulunci shine addini,ya yarda MUHAMMADU(SAW) manzon ne to wannan ya dandani zakin imani "
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Ta shigo kauyen cike da murna dede wata kwana ai kuwa wata motar yan kasuwa ta shayo kwanar itama ai kuwa ta kwasheta ji kake ragajaf ta zube nan kasa wanwar ...
Ta kuwa bare baki iya karfinta ta saki wani runtamemen ihu sakamakon wani bala' in zafi da taji a kafafunta ...tuni ta sume dan zafi ..kan kace mi a ka kwasheta akayi likita baban gari dake kusa da su ..amma mi daga nan ma aka turasu babar likita ta birnin Damagaram har lokacin da suka isa bata farfado ba..
Nan likitoci suka bata taimakon gaggawa .....sukayi mata allurar bacci dayake dare yayi daman ..
Dreban daya kade ta ne bayan sun koma kauye yaje ya sanarwa da Malam Musa ...be wani daga hankalinshi ba yade ce Allah yabata sauki..
Washe gari wajejen goma na safe ta farka da kadan2 take bude idon ta harta bude su ware ..dan motsa kafafunta tayi aman se taji kamar babu su ..dan danan gabanta ya bada fat .....da sauri ta yunkura zata tashi aman ta kasa ..se kawai ta fara ihu.....
Sega infirmieres"likitoci " sun shigo da gudu da kyar suka samu tayi shiru tace miya kawoni nan ne.
D'aya daga cikinsu tace ina kyautata zaton Accident ne kukayi wanda ya hadasa miki karaya har biyu a qafar dama se kuma qafar hagun da aka cire miki ita saboda gaba daya kashishuwan wajen sun ratatake babu damar dori dole seda aka cire ta
Wani ihun kururuwa da ta saki se da ta firgita su ta dunga ihu da fuzge2 kamar sabon kamu...
Wata nurse tace haba baiwar Allah kamata yayi kiyi hakuri kiyi hamdallah daba duka bane aka cire miki ko kuma ma da kika rayu baki maceba
Haba ina Murza bata ma san tanayi ba ganin abun bana qarewa bane yasa suka mata allurar bacci tukon suka samu lfy..
Se sha biyu Musa yazo likitar ..nan docteur yayi mishi bayani halin da Murza ke ciki..
Banda girgiza kai babu abunda yake....
Ya na fitowa daga office din doctor direct chambre "daki"da Murza take ya shiga wanda yayi dede da farkawarta ...
Ta bare baki zata fara kururuwa yace ke dakata bakida hankaline ?ko baki san nan likita bane da akwai marasa lfy?to walahi kiji da kyau inde kika ci gaba da wannan ihun naki to ina me tabbatar miki gidan Mahaukata zasu kaiki..
Tsit kakeji Murza tayi se wani mazurai take..
Nurse suka shigo duka dan duduba ta suka bata magani tasha ...(su Murza an zama me kafa
daya ....)
Kafin sati ya zagayo har ta fara jin sauki ....
Labari na kaiwa ga Maysam ta kuwa bi ta tada hankalinta ta ringa rokon Fulani ta barta taje ...
Da fari Fulani ta kiye mata ganin duka ma yaushe akayi aure harda zata fara futa amma irin addabar tata da tayi setace shikenan jeki tambayo mijinki inhar ya barki sekizo mutafi tare dan ban yarda da Murza ba..
Jin haka yasa Maysam ta bata rai tace haba Momy (haka itama take kiran Fulani yanzu) miye na wani tambayyarshi kawai muyi ta fiyarmu..a zahiri kuwa tsoran zuwa idan yake take..
Fulani tayi dan murmushi tace baki san mace bata futa seda izinin mujinta ba?..duk macen da ta futa bada ixinin mujinta ba to tana cikin tsinuwar malaiku .ne har ta dawo
Nan tayi tajan hankalinta....
Maysam tace shikenan bari na tambayoshi to ta fice daga palon
Fulani kuwa a ranta ba karamin dadi taji ba ganin yanda Maysam din ta dauketa kamar mahaifiyar ta...
Seda taje bangaren nashi tsoro ya kamata nan ta fara wasisin shiga..ta jima nan se kawai tayi shahada ta shiga..
Zaune yake bisa doguwar gujera a palon ya mak'ala ecouteur "earpiece "a kunne se wani karkada kafa yake...
Tun lokacin data shigo fitinenen kanshinta ya sanar mishi da zuwanta amma se yayi kamar besan da shigo warta a..
Itama tunda ta shigo kallo daya ta mishi ta kauda kai ..
Ta jima nan tsaya tana tsoran yi mishi magana tajawa kanta rankwashi dan bata manta dana waccen ranar ba..
Ta kusa rabin awa tsaye sekuma ta samu waje ta zauna a kasa ta sada kai
Ganin haka yasa ya tashi ya zauna yace ke dabbar inace daba zakiyi sallama ba ...kuma ki wani zo kisani gaba bako gaisuwa ke gaki ishashi ko? ...
Itade batace komi ba a ranta tace kai wannan mutumun komi zakayi baka yi mishi dede..
Shifa yace kada na sake gaisheshi ..amman yau kuma yana fada akan gaisuwar..
Abunda ya harzukashi menan jin tayi mishi shiru ya ce ke yaki nan na tatakaki..
Maysam da shegen tsoro har kwalla ta cika mata ido ta miki ta fara tafiya kamar hawainiya ..
Wata sangamemiyar tsawa ya daka mata. Ai kuwa bata san lokacin daya gurfana a gabanshi ba.
Yace....
Sorry fans nida kaina nasan yanxu banayin typing me yawa kuma ina ganin korafe2 ku banaki d'auka bane....de kuna muna uzuri ..am buzy kwana biyun nan ne..
Love you all fans irin sosai din nan
Fasma
Ahmed Gumel
[8/17, 1:50 PM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[8/17, 1:53 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 14 · 0% Book details