Sashe 25
Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🅿️ 53__54
Story&Written
by
*FASMA*
Dedicated to all my fans
*Queenbaby ina kika shige ne kwana biyu keda Ummu Usman..?Allah de yasa all is fine....munyi* *missing dinku matuka .. pls come back soon...*
*Dubun gaisuwa zuwa ga yan kungiyar mu na STAR ,W,Ass .hakika ina alfahari daku * Allah* *ya qara hada kammu* ...
*
*Ina yinki irin totaly din nan tawan Arfat ba ....ina jin dadin yanda kike kula dani da nunan kauna Rabbi ya kara dankon zumunci** ......
53__54
```
Manzon Allah (SAW) yace''tsakanin mutum da shirka da kafirci shine barin sallah kawai''
Muslim ne ya rawaito shi.```
Da asuba ta rigaye shi tashi tayi mamakin ganinta a dakinshi ...direct tolet ta nufa ta doro alwala ta kabarta sahlan nafila dan har yanzu lokacin sallar asuba bai yiba ...
buda idonshi yayi ya saukeshi akan ta tanata lazimintz yayi matukar mamakin ..jin an fara asalatu yasa shima ya doro alwalan yayi raka'atanil fajr ya na gamawa ya nufi masallaci don yin sallar asuba
Itama tashi yayi tayi ..
Bayan ya dawo ta duka har kasa ta gaidashi
Ba yabo ba fallasa ya amsa ...nan ta fido alkur'ani ta fara tilawa tare da azkar ....shima zaman yayi sukayi tare sanan ya jata suka koma .gado dukda de kowa a sharenshi yake kwance
.
Bai bude ido ba se wajejan goma na rana ......beyi mamakin rashin ganinta ba ...wanka yayi ya fito cikin shirin shi ..
Tana zaune ita kade ta saka tv gaba ya fito .......
Kare mata kallo yayi daga sama har kasa shigar riga da wando ne a jikinta na english wear ......kayan ba karamin kyau suka mata ba .....ga ba dan kwali a kanta kitson nan ne ''tsinar shimkafa'' akanta duk ya zubo bisa kafadinta .....da sauri ya dauke kanshi jin zuviyar shi ta fara sauya kid'a ...
Direct dinning ya nufa ..ya zauna...
Tana ganin haka ta bishi itama ...
Arish da pepper soup ta zuba mishi da wainar shimkafa se ruwa tea .......ta sakashi gaba tana kallo ....
Be dago kai ba ya fara ci tare da fadin ke har kinyi break dinne ..?
Ina Maysam bata ma san yanayi ba ta tafi duniyar tunani ....a ranta tace ita bata taba ganin mutum me kyau irin yayanta Murad ba kamarsu daya da babanshi .......
Dago kan da zeyi jin bata amsa meba ai kuwa idonsu suka sarke jikin juna ...dama ya kurbi tea ne ai kuwa se ya sarke shi ya shiga tari ba shiri .........itam a kuma seta rikice gaba daya ruwa kawai ta iya bashi yasha tare da dan bubbuga bayanshi irin yanda taga anayi....
Da kyar tarin ya tsaya yace dama an zo ansaka mutum gaba ba dole ya sarke ba...
Tayi dariya tace kasan mi yayana ..........?
Ya gimtse fuska yace miye ne....?
Se jikinta yayi sanyi tace a'a bakomi shikenan ma......
'Dage kafad'u yayi irin ''je m'en fou''(i don't care)din nan.... ...a ranshi yace yarinyar nan sena dena sake mata fuska dan kada ma ta rena ni.irin wannan kallon ....
Be gama tunanin ba ta tashi ta barshi nan .....
Ya bita da kallo tare da tabe baki yaci gaba da cin abincinshi amma jikinshi yayi sanyi....
Falo ta zauna se turo dan karamin bakinta take wai ita adole tayi fushi ......
Bayan ya gama ya dawo falon ya kalleta shi abun ma dariya ya bashi yanda take turo bakin .....
Cike da wayo yace to ni natafi shopping din ........tunda kinyi fushi ai seki zauna tsaran gida yayi hanyar fita a palon ....
Da sauri ta mike tare da sakin fuskar tace kai yaya bafa fushi ne nayi ba...
Ya juyo yace to ai naga se wani turo baki kike kamar shantu...
Bubbuga kafa ta farayi akasa irin na shagwababun yaran nan ...
Ba karamin birgeshi tayi ba dan haka sweetbabyn shi keyi .....
Tsayawa yayi yana kallonta ganin abun bana karewa bane yace to shikenan jeki ki shirya kizo mutafi ....kuma cinq(5)mn na baki...
Da gudu ta fice dakin ....... Bata jima ba tafito cikin shirin ta na atampa riga da ''jupe''(sket) se dan gyale data yafa ....tana fito wa yayi mata nuni da hannu data je ta sako hijab...batayi musu ba ta koma ...hijab din ya fice gwiwar ta .....
Suna fitowa dogarai suka fara kwasar gaisuwa ansar key din yayi daga hannu driver ya shige itama tana ganin haka ta shiga ...suna gani ya shiga mota suma suka fara haramar shiga sauran motocin amma se ya daga musu hannu ya na nufin baya bukata .......
Ba karamin mamaki dogaran sukayi ba amma babu yanda suka iya haka suka dawo..
Har sun shiga mota yace ke wai bakida nikaf da safa ne?
Girgiza mishi kai tayi......
Dan jim yayi sannan ya tada suka tafi ...
Shopping mall ya kaita kayan kam babu irin wanda bata dauko ba kama daga lesh ,,,atampa ....daganan suka nufi bangaren turare da man shafawa ...ganin be dauki komi ba yasa ta dauki wasu mayun turare tare da mayyukan su da sabulunsu har kala biyar duk na maza se kuma irin set din na mata shima kala ukku...
Bayan sun gama layin nikaf da safa ya nufa ..ya jibgo mata yana fadin ko a school ne to ki tattabatar kin saka safar nan ...ehe...
Ita de to ne nata bayan sun gama ya kaita wurin wasan yara ...
Yana daga gefe se wasannita take a ranshi yace wannan ba aure ba aka mun raino de aka ban .....
Kai ranar yakaita wurare daban2 ..se la'asr likis suka dawo ..bayan sunyi sallah direct dinnig suka nufa dan sun kwaso yunwa......
Set din turaren nan kala biyu ta doko ta bashi tace naga baka sai komi ba shi yasa na dokoma...
ba karamin mamaki yayiba nan ya amsa tare da fadin ashe. de bakida rowa ..
Dariya tayi tareda rufe fuskar ta..
Shima dan murmushin gefen baki yayi ...
Washe gari kuwa sha daya na safe ma acan tayi musu inda suka bar dogarai da kuyangi zasu shigo motocin su dawo dan su jirgi suka biyo ,,,dukda yasha kauyanci wurin Maysam..dan ita jirgin ma se ranar tayi mishi kallon gaba da gaba ...
murna wajen fulani ba'a ma zancan girke2 iri2 tasa aka yi musu ...sosai taji dadin yanda Murad ya rage hantarar Maysam a daya daga cikin dakunan fulani Maysam ta sauka yayinda Murad ke nashi bangaren ...
Da dare bayan sun futa ta fito da turaren ruka ta bawa Fulani set biyun na mata da buyu na maza tace wannan naki ne keda dady ne (Sarki) se kuma wannan ta fiddo wasu set din iri daya guda biyu tace wannan kuma daya na Abbana ne dayan na inna Murza...
Zo kaga Murna wajen Fulani kamar wacce batafi karfin kayan ba ..nan ta ringa saka mata albarka..dan gaskiya taji dadi kuma ta yaba da hankalinta..
Shima me martaba ba karamin nuna jin dadin shi yayi ba tare da saka mata albarka....
Lokacin da aka jewa da Malam Musa da wannan alheri har kukan murna da jin dadi yayi ya saka mata albarka yafi cikin kwando...sab'anin Murza da bakin ciki saura kiris ya kashe ta wunin ranar tayi shine tana tunanin yanda zatayi da Maysam tsaki tayishi yafi sau a kirga a ranta tace wannan yana nufin kenan tana can tanjin dadin rayuwarta ko....?can tace kai wly da sakema wai abawa me kaza kai ....
Madina sosai ta sawa lamuran waziri ido ta baza bayinta ko ina dan ganin mi waziri ke barkatawa dan yanzu yama dena shigowa part dinta .. Aranta tace kowa yaci tuwo dani to miya yasha...
.
Su Murad kuwa Tunda sukazo tare suke yawo duk inda yayi tana binshi dare ne kawai ke rabasu ba karamar shakuwa da juna sukayi.ba....har Mahmud yana tsokanarshi da cewa kode ya fada tarkon son Maysam ne...
Shikuwa se ya yatsine fuska yace ina abunso anan dan farin nata ko dan dogon hanci da karamin bakin ze jani...yaja tsuka ...yace yarinyar da ko kirgen dangi ma bata faraba ina abunso a jikinta .....
So daya ne nakeyiwa Sweetbaby na..wannan itama tanacin alfarma fulani ne yo banda wahalar raino ma ba abunda nake....
Mahmud ya sheke da dariya yace gaskiya nawan ka iya tsara mutum .fa.....da wani ne na tabbata ze kama zancen nan...amma yo ai ko irin kallon dakake binta dashi ko makaho ze gane bare aka zo ga zancen kishi .....
Murad yayi kicin2 da fuska yace a'aa ya ishe ka hakafa inayin haka ne dan kare martabar aure tunda de an rigaya an auramin ita babu yanda zanyi ne...
.
A bangaren Maheeba kuwa ba karamin tada hankalinta ba tayi dan ita se yanzu tasan Murad yanada mata duk da taga yarinya ce karama aman kyaunta ya tsora tata...
Nan fa ta dagawa mahaifinta Waziri hankali .....babu yanda ya iya haka yayi shiri zuwa ga Murad da zancen.......
Zaune yake shida Maysam datake kan cinyarshi se wasa take da sajen fuskarshi tana dariya yayinda shikuma yake daddana waya a lambu ga kayan marmari cike a gabansu ...
Ganin waziri yasa Maysam sauka ta zauna a kasa kusa dashi...jin ta sauka yasa ya do kai ya kalleta seyabi inda take kallon ..tsinkayo waziri yayi yana magana da dogaran dake kofar shigowa lambu...
Iso akayi wa waziri ...bayan ya kwashi gaisuwa se kuma yayi shiru ...Murad ma shiru yayi mishi dan yan Mulkin sun motsa ..
Can Waziri yace ranka shi dade inason yin magana dakai ...
Hannu ya daga alamun ya fadi yana saurarenshi ...
Kallon wurin da Maysam waziri yayi ..cuwat ta mike zata basu waje..Murad ya dawo da ita kan cinyarshi ....
Waziri a ranshi yace tirkashi wata zufa ta karyo mishi .....
Can yace dama zancen wajen y'ata ne....ina son ka aureta ....
Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ta dago ta kalleshi ...Murad ma kallon nashi yayi yace....
Wash kuyi manage da wannan...
Bansan haka masoyan wannan book din keda yawa haka ba ...a gaskiya ina alfahari daku Rabbi ya bar kauna da zumuncin mussaman yan group din HAUSA YOUNG NOVEL na facebook ..ina jin dafin yanda kuke nuna kaunar ku ga book din nann...ban manta da kaiba Ahmed Gumel ...godiya me tarin yawa Alherin Allah ya kaimaka a duk inda kake......sauran groups ban manta dakuba kusan ina yinku irin dayawan nan
...
Fasma ce
Ahmed Gumel