← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 67

Sashe 50

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dora hannu aka cikin kuka tace na shiga tsinuwa goma(10) da gomiyatara(90) ..wata zuciyar tace kuma ki duba fa yayi miki uzuri da yawa ba yau yake bibiyarki da bin bayanki ba amman kina ja mishi rai.
Wata zuciyar tace to ai ba laifinki bane tsoranshi ne kawai kike ji kada ya kareraya ki(ji fa🙄 to ya cemiki ana kareraya mitum ne.. )dan a yanda yake din nan kema kisan kukanki baze kwaceki ba sede sunan sweetbabyn shi. ..se kuma dayar zuciyar tasake tunatar da ita cewa ai hakkinshi ne dole kuma kibashi in baso kike ki kasance cikin tsinuwar malaiku kamar yanda kike ciki yanzu nan..tunawa da hakan a million ta fito ta fada dakinshi aman setayi rashin sa'a dan har ya fice a gida ....wani kukan ta sake fashewa da shi haka jikin babu kwari ta dauko waya ta danna mishi kira aman har ta katse be dagaba kai kira na biyu data sake sema akace mata wayar a kashe ....nan tashiga kuka tana fadin pls yaya pardonne moi kazo bazan kara hanaka ba .....can de ta lallashi kanta tare da alkawarin yau zata bashi hakkinshi koda be nema ba ita zata nema (tofa Maysam rigima🙆‍♀🙄) se kuma ta shiga duniyar tunani tace kai zanso sanin yaya sweetbabyn nan take koda ma photon ta tane ........itama de wanka tayi ta sauko duk jikinta yayi sanyi wurin su Mufeedah dan tasan itada ta ganshi se dare tunda yayi fushi da ita..haka suka wuni wanda Maysam ta dan sake kadan dasu suka sha firar su wanda yawancinta ta school ne .....

Tun bayan la'asr take shiga da ficen dora girki duk tabi ta gajiyar da kuyangin gidan dama su ukku kade .ne.abinci ma kala biyar tayi jus kala ukku ,banda qana nan specialites girki kamar su ''pain perdu salé, crêpe etc..

Su Mufeedah kam banda dariya babu abunda suke mata dukda sunsa daman ita takewa mijinta abinci kullum aman yau gilgilwar kan tata tayi yawa..itade bata kula su ba aikinta kawai take .......
Fans da gaske fa inaga Maysam zata bashi hakkinshi du da tana kunyar aman dan ta fita a tsinuwar malaiku zata daure dan kuwa duk wasu kayan da Fulani ta aiko mata yau seda tayi anfani dasu dan se jefi2 take aiki da su aman yau kam rankatakap ta dauko su. Kamar su kanunfari,bagaruwa,ganyan magariya..etc..
Ta jika wannan da zuma tasha in anjima tasha wani da madara...tofa abun nata yafara ruuko ido 👀kai fans ku tuna mata fa budurwatake zata sha wuya fa.. dan ni ba tama jina duk gani take kamar bana sonta da Muradinta ne🙄🙄..nide ba ruwana ehe..

Murad kam tunda ya fita ya fice office dukda babu aiki kiranta kam tun amota ya gani aman seya kashe wayar..yana nan har bayan sallar la'asr ga yunwa ta dameshi dan tunda ya fara cin abincinta ya dena cin na restaurant kona kuyangi dan baya jin dadin su kwata2 ....biscuit da madara yayi wunin sha se black tea.... ..

Kunna wayar yayi ai kuwa sega kiran Mahmud ya shigo ..bayan sun gaisane Mahmud ke sanar mishi daman Momy ce tayi ta kiranshi tun dazu aman taji akashe kuma takira matarka tace ka fita to shine fa ta tada hankalinta....

Yace am fine aman bari na kirata to..

Mahmud yayi saurin cewa ''es tu sure que tu vas bien? ''(are you sure you are fine?) dan na ji muryarka wani iri fa..

Ajiyar zuciya yayi da kamar bazece komi ba se kuma ya sanar mishi halinda yake ciki ko ze sama mishi mafita..

Mahmud ya kwashe da dariya harta kullar da Murad yaja tsaki yace kaji matsalar ka ai..in baza ka sama min mafita ba to se anjima..

Tsagaitawa yayi yace to kawai tunda de ba santa kake ba ka murkusheta ko ta karfine ka anshi hakkinka mana..

Murad yace bazaka gane ba to ai yanzu na dan fara sonta bazan iya yi muta ta karfi ba ..kawai zanta hakuri..

Mahmud yaja tsaki yace duka ma nawa Maysam din take ne kada fa ka manta yar renonka ce..

Murad yace tab ai wly yarinyar nan ta fice tunanin ka ka barta nan da wly yanzu ita ke renona dan ta fini kwarewa ta kowani fanin..yanzu ita ke renona

Mi Mahmud zeyi inba dariya ba ..can yace to kawai kasaka mata maganin bacci sekayi abunka..dan zaka cutu fa

Murad yace a'a bazan iya yi mata haka ba gwara na cutun da nabi ta haka(🙆‍♀🙄ku taya Murad da addu'a fa dan soyyaya ta mishi mugun kamu aman shi yana ganin yanzu ne ya dan fara sonta)... Yaci gaba da fadin gashi kuma bana iya jimawa ina fushi da ita ..dan ko wanan abun datayi mun kasa fushin nayi kaga harda computer da suke so na sai musu su duka ukku..

Mahmud yayi mishi godiya tareda addu'ar Allah ya kara budi se kuma nasihar da yayi mishi kan ya lallabe ta tun wuri dan kada ya kasa jurewa ya fada ga halaka dan ita sha'awa c'est naturel ..ko wani dan adam yana da ita..dan haka kayi a hankali..

Godiya yayi mishi sukayi sallama tare da jaddada mishi ya kira Momy ko hankalita ya kwanta..

Suna gamawa kuwa ya kira ta nan suka nan tattaba hira ....fulani na tabayyarshi ya akayi ya kashe wayarshi ....

Aman se ya kawar da zancen dan baze iya gaya mata ga abunda ya faru tsakanin shi da Maysam har ya kashe wayar kuma ma be taba yi mata karya ba kuma baze fara daga yau ba ..yace Momy ina maganar Ita Murza da fatan komi yana tafiya dede..

Fulani tace kwarae na saka a dunga binta duk inda zatayi ....aman de har yanzu bataje wani wurin ba..nan suka tattaba hira sukayi sallama..

Computer shi ya bude yana kallo se kuma naga yana sakin murmushi shi kade ..lekawa nayi naga miye ya saka shi dariya lokaci guda haka..

Hum 🙄photon Maysam ne da Sweetbabyn a screen din yana kallon yace tayaya zan ara miki computer na kiga photonki ne dana sweebabyna ne a screen ..ya kuma cewa kai amman fa suna tsanani kama fa. Kamar ya da kanwa.se kuma yace kai Sweetbabyna tafita kyau.se kuma yayi kalar tausayi yace miyasa ni kullum wanda nake so suke guje mun su barni ne..a lokacin danake bukatar su nan ya lalace da zancen shi shi kade...har kusan magrib ..sanan yayi alwala ya fice mosque..

Ina ganin haka nima na aje biro na dan na sauke farali...

Muje zuwa ..🏃‍♀

Ina yinku irin sosai din nan😍😘❤..

Fasma ce 🖊yar mutan Zinder.
[9/13, 9:54 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/13, 9:55 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

*Sumayya ,Iman,Maman Ss , Fatima to Maysam taji sakon ku kuma ta gode da shawarwarinku* ,😉 *tace zakuga sauyi...and tace tana yin ku irin sosai din nan😍.*

*Fans bazan gajiya da mika sakon gaisuwata zuwa gareku ba ..ina sonku irin more totaly din nan* 😍❤😘

Dedicated to all my fans😍❤

🅿95__96

```Manzon Allah (SAW) yace''wanda ya kawar da mugun abu daga hanyar da mutane ke wucewa ,to za'a rubuta masa kyakkyawan aiki ,wanda kuma aka karbi kyakkyawan aikinsa zai shiga Aljannah
Bukhari ya rawaito shi.```

[13/08/18 à 00:00]Maysam kam tun bayan sallar isha'i ta gama kominta taci uban ado ta zauna nan palon sama tana jira amma ji kake shiru kamar an aikin bawa garin su ...yau ko exercises din bata ji zata iyayiba ...suma su Mufeedah basu neme taba ...nan ta kunna tv ta kura mata ido kai kace tasan mi ake yi alhali hankalinta na can duniyar tunani ...har karfe tara babushi babu labarin shi..hakanan jiki ba kwari ta danna mishi kiran kamar da wasa ta shiga sede be daga ba ....se ana biyar ya daga ko sallama babu yace wai miye ne kin dameni da kira..

Itama a memakon ta bashi amsa se ta fashe mishi da kuka .....

Yaso kashe wayarshi ya kyaleta se kuma yaji baze iya hakan ba dan har cikin ranshi yake jin kukan nan..

Dan haka ya tausasa murya yace kiyi shiru ki fada mun mike faruwa ...waya tabaki ne...

Ji tayi wani abu yazo ya tsaya mata a makogaro a ranta tace be masan shine ya taba tan kenan wata zuciyar ta fara ingizata da cewa ai wannan ma reni ne ..bayan yasani sare bakya iya jure fushin aman yazo yana tambayar wane ya tabaki ,....hum ai duk laifin kine dakika bari har yaga damar ki haka ...duk son da kike mishi ai be kamata kiyi saukin bada kanki ba ..ko kin mata ranar da kuka fara haduwa da mari kuka gaisa ..bayan nan wace irin tsana ce be gwada miki ba ..seda ga baya kuma aman kiyi tsai ki gani yama tab'a baki hakuri kan duk irin abunda yayi ta miki ne.....sosai tayi na'am da hudubar zuciyar.. Dan haka a fili tace mishi babu komi.. Tana da share hawayenta . ....

Sun jima can babu wanda yayi magana kowa da abunda yake sakawa cikin ranshi sun kusa minti 5 a shirun kuma babu wanda ya katse layin..

Murad ya katse shirun da fadin se anjima tun da de bakida abun fadi. ....

Da sauri yace pls yaya ka dawo yanzu bana son kana cika dare a waje ..

Ajiyar zuciya ya sauke yace shikenan ganinan zuwa .to. .

Se lokacin ta sauke ajiyar zuciyar itama tace a shigo lfy..

Wani dadi taji jin gashi nan yanzu ze dawo ..
Chapter 50 · 0% Book details