← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 67

Sashe 6

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

🅿️ 13__14
*Sakon gaisuwa ta musamman zuwa ga y'an kungiyar mu Star writer's Ass hakika ina me farin cinkin kasan cewa cikin wannan kungiya* *Allah ya qara had'a kamu* ...
*Alherin Allah ya kaimu ku a duk inda kuke* :
*Queen baby* ( *in-law d'ina* )
*Momyn Mufeeda* ..
*Ummu*
*Hadjara Arfat .. ina sokon sosai* . _Allah ya bar zumunci_
Dedicated to All my Fans
13__14
```Manzon Allah (SAW) yace''Duk wanda baya tausayin mutane to shima Allah ba zaiyi masa Rahama ba''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi``` .
Tafiyar awa biyu ta kaisu kauyen .
Maysam tunda suka tunkari unguwar su kirjinta yake ta fat2 tsoranta daya kar ace Malan Musa bayanan..
A kekenta na guragu kuyangun suka turota har tsakar gidan ...idan sukayi ta kwad'a sallama sega Musa ya fito daga bayi da buta a hunnu wanda besan lokacin data fad'i daga hunnunshi sakamakon tozali da yayi da Maysam ..
Da sauri harda d'an gudun shi ya qaraso wanjenta ya rumgumeta yan shafa kanta yana fadin yar Abba kece?ina kika shiga tsawon lokacin nan ?kisan kuwa irin wahalar neman naki danayi?
Itama qanqameshi tana kuka me game da dariya ..sun jima a haka sai da jakadiya tayi gyaran murya tukon ya san ashe da mutane a wajen.
Sakinta yayi yana kallon su yace ku kwa daga ina bayin Allah ...
Maysam tayi saurin cewa Abba ka bari ku gaisa mana ....
Taburma ya dauko ya shinfid'a musu ...ya kawo musu ruwan sha .suka gaigaisa ....
Jakadiya ce ta labarta mishi komi game da ACCIDENT d'in
Sosai ya tausayawa yar tashi har da kwalla ashe tana can tana jiyya Murza da yan qauyen sharri ne kawai suka kulla mata daman ya san haka kawai Maysam baza ta bar gida ba ...
Da zasu tafi Malam ya musu sha tara ta arziki duk da yasan sun fi qarfin abunda ya basu....
Murza na d'aka tana jin duk abunda suke fad'i a ranta tace ai walahi baza ki tab'a warkewa daga karayar nan ba ...gurguwa ma zan meda ke shegiya mayya ina jin dadi na rabu da ke ashe kika ce ina nan dawowa...tayi tsuka yafi a kirga ...(jifa se kace gurgunta mutum din a hanunta yake
.)
Wunin ranar har dare Maysam na bawa Musa labari irin kirkin da kulawar da Fulani ta bata ..shima ya labarta mata irin yawon neman daya yi mata...
Haka rayuwa tayi ta tafiya yau har tsawon wata guda idan Maysam yanzu sauki ya fara samuwa sosai ta murmure abunta har wata qiba tayi tana jin dadi rayuwarta dan kuwa Musa yanzu baya zuwa ko'ina yana zaune yana jiyyar y'ar shi har ta warke ...
Lokacin kuwa Murza had'e zuciya ne kawai batayi ba dan haushi taso yayi tafiyar kasuwancin shi dan ta samu damar idasa qafar Maysam.. ga aikin gida ita kad'e keyi Maysam na zaune sede a dafa a bata taci....
Zowan su jakadiya ma ukku dan duba lafiyar Maysam d'in....
.
Zaune yake a gaban me Martaba ya sadda kai kasa se bada hakuri yake
Fulani na gefen me martaba gefen d'ayan kuwa wata matace wacce za suyi sa'anai da Fulanin kyakyawa ce itama hjy MADINA kenan matar sarki ta biyu kishiya ga uwar gida hjy Maryama (mahaifiyar Murad) amma se wani yatsina fuska take kamar wanda taga kashi a wurin ..qasa2 kuma inta faki idon sarki seta zabgawa Murad harara..
Fulani na ganin duk abunda take yi batade ce komi ba dan idan sabo ta saba da hakan...
Sarki kuwa se fad'a yake yiwa Murad yace to walahi bari kaji na baka sati biyu ka fito da mata in kuwa bahaka ba zan aura maka wacce naga dama ..
Shide Murad hakuri kawai yake badawa..
Caraf Madina tace a d'an qara mishi lokaci de d'an nawane se da lallab'a cike da kissa tayi maganar ...
Murad beyi wani mamaki ba dan kuwa ta kware wajen makirci a gaban sarki zata nuna tafi kowa sonshi ...
Sarki yayi murmushi yace ai d'an naki ne bayaji yaune ake mishi magana d'aya ...
Ta qara cewa ayide mishi hakuri wannan gamun ze kawo ...
Kasa cewa komi yayi dan takaici ...
Bayan sun dawo bangaren Fulani nan ya dinga yiwa fulani kuka kamar qaramin yaro shifa bayason aure kuma bazeyi aure ba ...itade fulani lallashi take tare da yi mishi nasiha ranar a nan b'angaren ya kwana ...a zuwan washe gari ze koma wajen aikin shi..
.
Maysam kuwa sauki ya samu har tana d'an taka qafar ...
Ganin haka Musa yace zeyi tafiya amma a ranar ze dawo ..Maysam bataso ba amma ba yanda ta iya ..haka yayi sabko ya tafi..
Ranar Murza har zubda ruwa a qasa tayi tasha ...ko awa guda da futa beyiba Murza kwallawa Maysam kiran wanda seda gabanta ya bada ras tasan kiran Murza babu alheri cikinsa ..haka ta turo keken ta fito tace gani inna. ...
Wata dariyar mugunta tayi tace yau daga ni seke agidan nan(nace se kuma Allah ba) kiyi abunda na saki ki tsira ..bakiyishi dedeba jikin ki ya fanshe ki ...
Itade kallonta take batace komi ba..
Murza tace kaf aikin gidan nan yau kece me yinshi daga sharar garken shanu zuwa ta tsakar gida ..wanke2 girki .wanki d'oko ruwa a rafi....
Batace komi ba hakanan ta lallab'a tayi shara da wanke2 ...tana cikin jan ruwan wanki gugan ya kubce ya fad'a rijiyar ...
Wani uban dundun tayi mata wanda seda gantsare ta saki kukan wahala ..
Murza tace to kuwa tunda kika bari gugan ya fad'a seki fice rijiyar cikin gari ki d'auko ruwan..
Ta d'auko tulun kenan bisa tsautsayi shima ya kubce ya fad'i a bunka da laka daidaya tayi anan.....daman me karaya inashi ina iya dauko ruwa inba muguntaba ...
Murza bata tsaya b'ata lokaci ba ta fara jibgar ta daman da gangan tasata ..iya qarfinta take dukanta har Maysam ta fad'o daga keken aman wannan be sa Murza ta dena kishinta ba..
Cike da mugunta tasa qafa ta take qafar me karayar tana wani mummurza qafar har wani cije leb'e take irin na inkana yiwa wani mugunta ..
Wani quwa Maysam tayi se kawai tayi suman wahala ...tajata rana ta yar anan..(Allah sarki Maysam .)
Kan kace mi qafar har ta fara kumbura ...
A dede wannan lokacin sega su jakadiya suna rafka sallama a gidan jin shiru yasa suka leko daga zauren gidan ..ganin Maysam a yashe tsakar rana ga kuma babu alamun rai a tare da ita da gudu suka qaraso cikin gidan suna salati ganin irin kumburin da qafar tayi yasa suka d'auketa dan kaita likita..
Eh kuwa sega Murza nan ta fito nanfa tace babu wanda ya'isa yatafi mata da y'a ta fara musu borin hauka tare da zage2 hakan ya tunzura jakadiya ta kwallawa sarkin hukunci kira dayake tare suka zo ...
Murza na gani shirgegen qato fuskar nan murtuk ai da gudu ta shige daki ta kulle tana ihu b'arayi zasu sace Maysam wai anufinta ko makota zasuji ...
A guje suke tafiya tun a hanya jakadiya ta sanarwa Fulani abunda ya faru nan fulani ta dinga kiran doctarori kan kace mi duk wani kwararen docteur na garin me d'orin karaya ya zo clinik jiran iso warsu kawai ake...
Har suka iso Maysam bata farfad'o ba an shafa mata ruwa yafi a kilga aman shiru ....
Suna isowa aka kaita emergency nanfa doctarori suka dukufa neman ceto rayuwarta....
Seda suka shafe awanni tukon suka fito fulani na nan tana jiran fitowarsu kamar wancen lokacin....
Bayan sun kwashi gaisuwa d'aya daga cikin doctarorin yace alhadulillah munyi nasara aman a gaskiya yarinyar nan ta wahala dayawa kuma karayar ta dawo sabuwa har ma tafi ta farkon dan haka tana bukatar hutu a 100% ...yanzu haka mun mata allurar bacci ...da zasu tafi akayi musu biya me tsoka ..
.
Malan Musa kuwa be dawo gida ba se can cikin dare dan haka besan abunda ke faruwa ba .se washe gari yaga bega wulgin Maysam ba har goma tayi ya kasa hakuri yace waini Murza ina Maysam ta shigane ...
Kamar jira take ta saki kukan munafunci tace ai Maysam jiya b'arayi suka tafi da ita..
Cikin tsananin tashin hankali yace wani iri b'arayi ke dakata tun wuri kafin raina ya b'ace ki gayan inda kika kaimun diyata inba hakaba zan d'auki mummunan hukunci a kanki
Ganin ya d'auki abun da zafi yasa tace wanda suka tab'a kad'e tane sukazo suka tafi da ita wai nan bama kula da ita..
Wani mari ya kifeta dashi yace walahi inde dasa hannunki se kin yabawa ayya zakinta ya fice daga gidan kamar ze tashi sama dan sauri ...dayake masarautar sananna ce kuma wancen lokacin sun sanar dashi dan haka mota me zuwa garin direct ya shiga ..bewani wahala ba aka kaishi har kofar masarautar ....
A kofar clinik din ya gamu da jakadiya nan suka gaisa dayakesun shedi juna ..nan ta labarta mishi yanda suka tarar da Maysam da kuma dramar da sukayi da Murza ranshi ba qaramin b'aci yayi ba nan ya bata hakuri tayi mishi jagora har d'akin Maysam d'in ...
Har lokacin bata farka ba nan ya samu wuri ya zauna yana kallonta tare da rafka tagumi..
Yana nan har fulani ta shigo nan ya kwashi gaisuwa ..suna cikin haka Maysam ta farka da wani irin ihu tana fad'in dan Allah inna kiyi hakuri ba da gagan bane..bazan qaraba
Da sauri fulani ta isa kusa da ita ta riqe mata hannu ta kirayi sunanta Maysam Maysam......
Jin murya fulani yasa tayi shiru tana kallonta se kuma ta fashe da wani kukan me tsuma zuciya tace qafata zafi take mun ..
Fulani ta shafa kanta tace yi shiru ze dena kiyi hakuri kinji.....garin yaya kika bari qafarki ta sake karyewa ne ...
Tana hawaye ta labarta wa fulani duk abunda ya faru ta qara da cewa kuma fa a gaban Abba bata nuna ta tsanane aman da zarar baya nan seta yi ta muzguna mini....hakika Abbana yana sona bayason b'acin raina yana faranta min amman bansan miyasa Inna Murza ke yimini haka kodan ba'ita ta haifeni ba ne..har lokacin batasan Malan Musa na d'akin ba ....
Fulani ta share mata hawaye tace kiyi hakuri insha Allah daga yanzu Murza bazata sake muzguna miki ba..kinjiko..
Gyad'a kanta tayi tace to ..se kuma tace dan Allah a sanarwa da Abbana kada yaje yayita nemana besan ina nan ba....
Batayi aune ba taji muryashi yana fad'in Yar Abba sannu da jiki
Cike da jin dadi tace laaa Abba yaushe kazo ne...
Be bata ansa ba se cewa yayi ashe haka Murza ke azab tar dake amman baki tab'a gayamun ba?mesa haka yar Abba kina cutar da kanki ...
Sadda kai kasa tayi tace kayi hakuri Abba ina tsoran kada na gaya maka kuma daga baya Murza ta huce a kainane..
Ai kuwa ta yiwa kanta dan walahi sena d'au mummuna mataki a kanta yanda kika wahala itama seta sha..
Maysam tace a'a Abba ka kyaleta da halinta kuma ai ba'a meda sharri da sharri ....
Duk wanda ya nufeka da sharri to kai ka saka mishi da alheri ..
Nan ya rumgumeta yace shikenan y'ar Abba na hakura Allah ya isar miki ya albarkaci rayuwarki hakika ke y'a ta gari ce ina alfahari dake...ameen tace..
Ba karamin burge fulani sukayi ba bare ma Maysam gata yarinya karama aman da kaifin tunani har taji wani abu ya tsargu mata a rai..
Nan aka dinga bawa Maysam kulawa ta kirki komi se anyi mata kai hatta da cin abinci inde fulani na wurin to itada kanta zata bata wata irin shakuwace ta shiga tsakanin su ..kuyangi har mamakin wannan abu suke sunsa fulani da kirki ga tausayi amman abunda take yiwa Maysam abun azo a ganine musamman Maysam da take y'ar kauye..
Malan Musa ne zaune gaban sarki bayan ya kwashi gaisuwa ..sarki yayi gyaran murya yace to daman wata alfarma mukeso kayi mana ..
da sauri ya d'ago kanshi ya kalli sarkin se kuma ya meda kanshi kasa yace alfarma fa kuma ma a wajena?
Sarki yace ai muna nema alfarmar ka bar mana yar ka ne..
Shiru yayi bece komi ba a ranshi kuwa fad'i yake gaskiya bazan iya bar muku ita ba..
Gani shirun yayi yawa sarki yace dama jiya ne mukayi wata shawara da fulani kan inde bakayi wa yar ka mijiba to muna nemawa yarima Murad auren y'arka Maysam ... .
To fa fans kun ji wata sabuwa kuma .....
Mu had'u a shafi na gaba insha Allah .. .
Ina kaunar ku fans irin sosai d'in nan
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:25 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:27 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
Chapter 6 · 0% Book details