← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 67

Sashe 29

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

shirin yin subutar baki ..... Gaba daya palon aka sa dariya .....nan Mahmud yayi serving dinsu efa nan suka fara santi shide yana zaune yana kallon su ...daya daga cikin su ya ce kai amma fa ka more fa irin wannan garar iya abinci.. Se yanzu ya sauke ajiyar zuciya dan shi duk atunanin shi abinci beyi ba ...kada aje yakiyin dadi ...se yaga kowa ya bude tumbinsa se durawa yake.....sosai yaji dadi a ranshi ....... ....Maysam kam tana samu ya saketa ta sulale daki ta hau buga game abunta.... Haka suka gama suka kara dan tataba hira.irin tasu ta abokai... Da zasu tafi ya kirawota sukayi mata sallama tare dayi mata godiya kudi suka aje mata kudi wai tukuicin dadin abincinta ne...tayi musu godiya tare da fatan sauka lafiya.. suna futa kowa ya shiga motarshi ya kama gabanshi... Se Mahmud da suna juyowa ya kwashe da dariya .... Murad ya kalleshi yace wai ya jikin naka ne? Mahmud dake dariya yace ba sauki ....yaci gaba da fadin wai dazun nan fa ka bani dariya yanda ka wani kasa ka tsare ka hana ta zuba mana abincin kamar ba bakin ka ba.. Bata fuska Murad yayi yace kajika da wani zance Matar t...se kuma yayi shiru... Mahmud yace karasa mana... Murad da abun ya kai mishi wuya yace kaga ya isheka haka kafa sa muna ido nida yar reno ta ehe.. Mahmud yace eee fa kace yar reno..to amman.. Da sauri ya daga mishi hannu yace ya isa mana ..ya fice bangaren shi.... Mahmud ma juyawa yayi ya fice gidansu ...yana me yiwa abokinshi dariya ganin da alama ya fara fadawa son yar renonshi ... Koda ya shigo a falon ya tarar da ita se buga game din take lokacin kuma har an kwashe an gyara wurin da sukaci abincin.....kudin da suka aje mata ya ga bata dauka ba ...ya doko ya zauna kusa da ita tare da amshe wayar ...dan karamin bakin ta turo .....yaiyai ta anshi kudin tace a'a ta bar mishi..........tace wai yaya dazu a daki me... Da sauri yace wai ke komi in baki sanshi ba se kin tambaya ne,,?( jifa to ai ko kogi yana bukatar kari bare ma be koshi ba)kul kada kuma naji kin fadawa wani wannan abun ke koda kuwa Momy ce(to fa )....gyaida kai kawai tayi ya jata zuwa bangaren sarki sukayi mushi barka da sallah nan waziri ya dinga mishi kallon zamu hadu....da ga nan bangaren fulani suka tafi inda suka rabshe se fira suke abunsu..... Washe gari kuwa ya kaita shopping ta zabi narka2n shadda da lesh .....suna dawo wa aka kaimata dumki... Kwanci tashi ba wuya yau har sauran sati su Maysam su koma school ...shirye2 take kawai .....kominta an tanadar mata na tafiya ...ranar kawai ake jira ...... Da yamma suna zaune itada Murad a bangaren shi suna kallon wani film ..can taji cikinta ya fara dan ciyo to dama tun safe tana ji amma ba sosai ba kuma yi yake se ya kwanta... Murad wanda yake lura da ita tun dazu yace wai ke lafiyar ki lau kuwa ..... Ita kam tama kasa magana Ido rufe ta kama mararta ....can daya kwanta tace mishi ba komai... A hakan ya barta ya ci gaba da kallonshi.... Ai kuwa can se ji yayi ta fado kasa tim tana murku susu har da kuka2 kasa2 ....da sauri ya isa wajen ta ya dagota yana fadin inna lillahi wa...yace ke wai mike damunki ne ...ina yake miki ciwo duk yabi ya rude.... Mararta kawai take nuna mishi amman ta kasa magana.... Yace mararki ke maki ciwo? Kai kawai ta iya daga mishi.. Iya tashin hakali ya shiga ..gashi likita amma ya rasa irin temakon da ze bata.... Love you all fans.... Fasma Ahmed Gumel [9/2, 10:00 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_* [9/2, 10:04 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹
Chapter 29 · 0% Book details