← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 67

Sashe 59

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bata san lokacin data rugumeshi ba tana zuba mishi godiya ..harda tamishi kiss a kumatu tace ''tu es le meilleur mari dans ce monde (you are the best husband in this world)...je t'aime à la folie...

Lakuce mata hanci yayi yace rigima ta kare kenan.....in sonki my beauty ,so na hakika ..kin kasance lantarki farin wata dake haskaka rawuya wata ...dan soyayyarki a hankali take shiga cikin zuciyata ..kin dasa gadargar kujerar mulkin ki a zuciya ta .....ki tausaya mun kada ki gujeni ..kamar yanda sweetbaby ta g.....

Da sauri ta rufe mishi baki tace kada kayi sabo .ba ita ta guje ka ba.Allah da ya halliceta yafimu santa.......kayi hakuri da kaddara

Nan de sukayi ta kwantarwa da juna hankali .....

🌹🌹🌹. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Bari mu leko Inna Murza..

Ita kam tun lokacin da taga Maysam da cikin nan hankalin ta ya dada tashi ..tana ganin Maysam zata kara samun wurin zama fa..dan haka ta kwallafa ran son ta zubar mata da cikin ko ta halin qaqa...shiyasa ma ta tare abangaren Fulani dan ta samu tasan irin shige da ficen Maysam din kuma .kusan kullum tana harin cikin sede bata samun nasara ..har yau Da Allah yayi Maysam ta fito daga bangaren M.Musa zata na fulani ..har ta fito hararabar gidan sega Murza da dan kofinta a hannu na jike2nta. ..ta bawa Maysam wai tasha tunda taga cikin ya tsufa ai ya kamata ace yanzu ta fara shan maganin itatawa dan haiwa tazo mata da sauki.kamar su sabulun salo ,etc.to itama haka in ka gani zaka zata shine ashe ta zuba wani maganin na zubar daciki a ciki ya narke ..

Da farko har taki amsa aman Murza se ta fara fadin dama nasan baki yarda dani ba ki amince mun babu komi ciki..

Kuyangita de suna dan gefe da su basu san mima suke cewa ba..

Amsa tayi ta kurbi kadan sau biyu sanan tace ya isheta. Tace ngd Inna

Murza ganin inta nuna damuwanta zata iya ganota yasa ta barta ..tace ba komi ai yiwa kaine a ranta kuwa fadi take zaki mun godiya me degree ....shegiya me kama da aljanu ai ayanda naga sun kwallafa rai acikin nan nasan daya zube zasu koro ki ...kizo na ci gaba daga inda na tsaya(Hum adeyi a sannu)

Maysam tayi mata sallama ta fice ....Murza se wani washe baki take..

A bangaren fulani ma fira suka sha sosai har na kusan awa guda.....

Har ta tashi da niyya tafiya cikinta ya fara murda mata ...
Fulani tace ta zauna har ya fice ai hakane daman babyn ne ke juyawa....

Aman mi ciwon kamar karashi ake tace wayoo Momy cikina zan mutu ..ai kafin ta bata wani temako tuni jini ya balle ..Allah ya temaka sega Murad ya shigo beyi wata2 ba ya ciccibeta se likitar masarauta ...

Emercency aka sata ..idanun shi sunyi wani ja ..yaso dhiga aman suka hanashi dan ayanda ya firgitar nan baze iya bata wani temako ba dan irin jinin da ke zuba da kyar ne in abun cikin ze rayu .... .. ...

Fulani ma duk tausayi danta dan dauther ta ya kamata ganin irin kinin data zubda ga kuma yanda Murad ya rikice lokaci guda ..ta ce ya Allah ya tashi kafadun ita da abunda ke cikinta.. Ameen

Seda suka shafe awa guda..sannan doctorin suka fiyo fuskarsu ba annuri...

Da sauri ya isa yana fadin how is she ...,da fatan babu abunda ya samu cikin....
Shi yama manta da shi wani yarima dan sarkine bare..
ya tuna da bayi da dogarai a wurin....shide ta yaji lfy su yake

Doctor yace follow me in my office ....da sauri suka bi bayanshi .lokacin Mahmud ma ya iso shima .

Bayan sun zauna cike da girmamawa yace am sorry t..

Buga table din Murad hayi da karfi yace you are sorry for what?se wani huci yake kamar ze daki doctor din..
Mahmud ya dafashi yace calm down mana controle your self .kaji meze fada..

Ajiya zuciya doctor din yayi yace dama ta zubar da jini da yawa ne dan haka muna bukatar jini dan babu a blood lab .. ..

Murad yayi sauri katseshi da fadin bayan karin jinin da akwai wata matsala ne ..i mean cikin be tabu ba..

Ee Alhamdullillah cikin yana nan be zube ba

Se lokacin ya sauke ajiyar zuciya
yace a dibi nawa ai group din mu daya ne ....

Seda suka gwada dan tabbatar da hakan sanan aka diba aka samata ..result din wani test da doctor din yayi yace su murad suzo office..

Yana kallon Murad yace taya ka bari hakan ta kasance agidanka a matsayinka na doctor..

Ya mutsa fuska yayi yace ka fadi abunda zaka fada mana ..

A hankali yace to matarka tasha magani zubar da ciki ne shi ya jawo kusan zubewar cikin sede Allah ya temaka bashida yawa wanda tasha shiyasama cikin be sami nasaran zubewa ba...aman akiyayi gaba ..

Wani gumi ya keto mishi ba shiri .yace what ?how dare you?.amsar result din yayi ya karanta yage haka ne..

Wani huci ya shigayi kamar wata kububuwa ya fito daga office din yanda kasan ana hankanashi haka yake tafiya direct dakin da aka kwantar da Maysam ya shiga...

_Kuyi manage da wannan ..wly dande nayi alkawari ne nayi wanan .dan kyan alkawari cikawa...am buzy kwana biyu nan ....aman zanyi kokari ganin na gamashi da wuri.a kwanakin nan...tkx for all support da kuke bani dakuma hakurinku tare da uzurin da kuke mun..Allah ya bar kauna da zumunci_ ❤ameen

Love you all irin sosai din nan😎😍😘

Fasma ce🖊(Fassouma yar mutan Zinder)
[9/14, 9:13 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/14, 9:13 AM] A A Dboy: 🌟 *STAR WRITER'S ASS* 🌟✨🖊
( _Home of spécial 🏡&extraordinary writers_ )

🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

S.W.A✍

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

~Goron barka da sallah~

*Happy Sallah to all Muslim Allah ya memeta mana..yasa munyi a dede ..barkan mu da* *sallah . ina yinku iri more totaly din nan* ❤😍😍..... *ina jiran barka da sallah na da kuma soyena na fa* 😉😉🤝

Dedicated to all my fans😍❤

🅿 107__108

```Manzon Allah (SAW) yace''dukkanin ayyukan alheri sadaka ne .
Bukhari ya rawaito shi.```

[22/08/18 à 23:30]
Yana zuwa ya banka kofar se huci yake ....lokacin ta tashi tana zaune kadan2 tke meda numpashi ..duk ta wani jeme abun lokaci guda..

Ya na shigiwa direct wurinta yayi Beyi wata2 ba ya falleta da marin da seda taga star .....ze kara mata Fulani ta rike hannunshi cike da bacin rai tace koda wasa kada ka sake ... what happen to you?ka barta taji da abunda ke damunta se kawai ka shiga dukanta ..alhali kuma da tsohon cikin nan

Momy baki san yarin yar nan mi tayi bane shiyasa kike fadin haka..

Fulani tace koma de miye ai se kabi a sannu ..ina gaya maka kullum ka dinga sawa zuciyar nan taka ruwan sanhi ..fa

Haba Momy yarinyar nan fa cikin fa taso zubarwa dan tsabar reni tasha maganin zubar da ciki dan ta barar dashi Allah ne kawai be bata sa'ar yin hakan ba..yana fadi yna maka ma Maysam harara ..

Itakam kanta a sadde yake tana zubar da hawayen...ba ta dago ba har lokacin dataji irin kazafin da yayi mata..

Da sauri ta dago kanta zatayi magana ya daga mata hannu yace kada ki ma fara bana son jin muryarki ma ....nine ma dana yarda dake bayan tun farko daman kin nuna rashin son cikin ..

Pls yaya .ka .

wata tsawa ya daka mata har seda ta firgita ..yayi kanta ze daketa..

Shima se jin Momy yayi ta daka mishi tsawar for the first time ....tace kada ka sake ka daketa ..marar tausayi da tsohon cikin nan zaka daketa dan bakada tausayi

Da mamaki yake kallonta idon nan yayi jajur ya sadda kallonshi yace Momy ni kikewa tsawa saboda wata can...

Momy ma cike da takaici tace Maysam ba wata can bace ...y'a ce kamar kowa ..tamana hallaci kuma matarka ce dan haka fita a dakin nan kafin nayi loosing din control dina..

Tsananin mamaki ya kara lullube shi yace Momy ni kike cewa na fita...

Momy tace to da wani ne bayan kai ..
Nuna Maysam yayi yace zaki gani ne..ya fice har ya kai kofar fita Fulani

tace babu abunda zata gani se alheri..sannan ina baka shawarar kada ka zartar da hukunci cikin fushi ..

Fuu ya fita ..se lokacin Mahmud ya shigo ..har kasa ya duka ya gaisar da Fulani tare da tambayar yame jiki ..se kuma ya shiga bata hakuri kan abunda Murad din yayi yanzu dan yana kofa yaji komi ..yace ayi mishi afuwa ran shine ya bace..

Itade Momy tana saurarenshi har ya gama ...tana kuma yaba hankali irin na Mahmud tare da jin dadin kasance warshi aboki ga danta..

Fulani tace yayi mata bayani .abunda ke faruwa..

.nan ya gayamata yanda sukayi da doctor ...itama bata ji dadi ba aman ba ta tsammani Maysam zata iya aikata haka ..kai ko in hakan ne ma to dawani abu akasa..

Maysam kam kara volume din kukanta tayi tana fadin walahi Momy ki yarda dani ban sha maganin komi ba....

Ajiyar zuciya Fulanin tayi tace ya isa haka to ..na yarda dake my dauther sannan kiyi hakuri kan abunda yayi miki.kinji ranshi ne ya bace . aman komi ze zama nml ..kada ki tada hankali ki mijinki yana da saurin yin fushi kuma saukarshi ma ta kankanin lokaci ne ..ki kyaleshi yanzu har ya sauko..shida kanshi zakiga ya dawo

Rumgume Momy tayi tana sauke ajiyar zuciya ..tace walahi Momy ina son cikin nan. ..taya uwa zata iya kashe danta ..
Nan de Momy tayi ta lallaba ta ..

Momy a ranta kuwa tausayin Maysam take ..gata so young aman da kaifi tunani ..shiyasa take jinta sosai a jikinta dan tana sonta ..
To inbama rashin hakuri na Murad ba ai komi tayi se kamata hakuri da izuri ka kumsawa yarinya ciki kuma harda duka ..to dami zataji ..ne.. Allah de ya kyauta...
Chapter 59 · 0% Book details