← Book details Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 67

Sashe 24

Sanadin Accident Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

51__52
```Manzon Allah (SAW) yace''fiyyayen musulmi shine wanda duk musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da hannunsa''
Muslim ne ya rawaito shi```
Da ice cream dinta a hannu ta bude kofar ...wa zata gani inba Murad ba wani waro ido tayi irin na kaga abun tsoron nan tace yaya se kawai robar ice cream din ta fadi daga hannunta gabadaya ta bata mishi kafa .........
Kara zaro idanu tayi tace yaya kayi hakur........
Kafin ta gama fada ya sauke mata yatsunshi biyar a fuskarta ....har tayi taga2 kamar zata fadi ...se yayi saurin fizgota ta fada jikinshi ...
Wani mayen electric shok yaji yabi jini da jijiyarshi kamar de na kowani lokacin idan har fatar jikinsu ta hade da sauri kuma ya hankada ta yace ''comment oses tu t'habiller de cette façon ? (Waya baki izinin yin wannan shigar .).....
Hannunta dafe bisa kumcinta tace Momy ce ta say mun da muka tafi shopping
Wani marin ya sake sauke mata yace Momy ta ce ni kade sekuma sweetbaby na ....... Da gudu ta fice cikin room ta bar shi nan tsaye ......
Dadin ta daya da Kuyangi tun lokacin da sukaga Murad ne su ka ficewar su
Shima hanyar stair yayi ya shige daya daga cikin dakin sama ....koda ya shiga dakin ya jingina da kofar ya rasa miyake mishi dadi zuciyar shi na wani irin zafi sai kawai hawaye ya fara zarya a fuskar shi wanda besan dalilin yinshi ba .....nan ya tsaya ya ringa tariyo scene din su ta yanzu da yanda take kuka wanda shi yafi kona mishi rai dan koba komi bayason ya ga mace na kuka bare shine sila ...wata zuciyar tace mize hana ka tafi ka lallasheta kada ma Allah ya kamaka da laifin cin zarafin ta, gashi kuma kaikade ta sani a garin..gata yarinya ...ya tuna nasihar Fulani cewa ya daure ya kulada Maysam ya ringa tausaya mata mareniya ce.....sanin irin zafin da mutum keji idan ya rasa wani nashi dukda yasan seyakai zuciyarshi nesa sannan ze iya kula da ita amma ze kwatanta ya gani..
Da sauri ya fita ya shiga dakin dayake tunanin tana ciki ...
Yana shiga ya hangota kwace bisa gado se kwasar kuka take ....
Gefen gadon ya zauna yace ke....
Da sauri ta tashi zaune tana kallonshi fuska cike da hawaye tace na'am..
Hannu ya biko mata yace zo ...
Da sauri ta rarafa tazo
d'orata bisa cinyarshi yayi yasa hannu ya goge mata hawaye yace kukan ya isa haka nan ...
Can yace bakisan ke matar aure bace ....
Cike da shagwaba tace na sani man...
Yace to shine kike irin wannan shigar bayan da maza cikin gidan .....
Tace to ai naga basa shigowa ,ni kuma bawani futa nakeyi ba shiyasa ai .....
Ajiyar zuciya yayi yace shikenan kikiyaye kisan irin shigar da zakiyi ...ina fatan de ba haka kuke shigar nan ba a school....
Nan ma tace a'aa bayan mun yi hutu ne Momy ta say mun a matsayin gift dan nazo ta biyu ...
Yace to nima ki shirya gobe na kaiki shopping ki zabi abunda kike so dan kin yi kokari amma fa kiyi kokari ki ringacin ta daya se kuma jibe mu huce can gida...
Wata dariya ta kubce mata jin zasu taga Momyn ta fulani har yar karamar wushiryar ta tafito tare da fararen hakoran ta wanda kyawunta da tsantsar kamarta da Sweebabyn shi ta fito besan lokacin da ya rungumeta tsam a jikinshi dudda ya ji shok din amma wannan karon sema ya kara matseta a jikinshi har seda tayi yar kara tukon ya dan sassauta mata ...
Ta raba jikinta da nashi tace yaya
Jibifa kayanka sun bace bazaka canzasu bane?
Ya kalla tare da mikewa da ita a hannushi yace mutafi to na fidda...Da ita suka shiga har dakin ya ajeta ya ce ina zuwa ya dauki kayanshi yashiga tolet seda yayi wanka tare da doro alwala jin an fara kiran sallar magrib........koda ya fito ta dan gogge wurin dayayi yar kura tana ta kiciniyar sake zanin gadon amma ta kasa shimfidar kasancewar yayi mata girma se turo baki take ...dariya yayi ya kama ya shimfida ya gyara tana kallonshi se dariya take mishi yana gamawa ya yi hanyar fita tare da fadin kiyi ki gama kiyi sallah ..tace to ...
Shikam be dawo ba se bayan sallar isha'i ..a zaune ya isko ta ta saka tv gaba se kallon dessin animé take a ranshi yace i lalle yarinya ce ....direct dining yaje ya zauna kuyangi sun zube abinci iri2 table din a shake yake taf da abinci dana sha .....a raina nace mutum biyu kade fa kawai zasu ci abincin nan amma ko mutum goma aka bawa to na tabbata se sunci sunyi saura.....wani nacan kwana ma zeyi beci .ba.Allah de shi kyauta...
Ganin bata alamun zowa yace ke zonan.kiyi serving dina inke bazaki ciba ......dan shi ko a gida baya barin kuyangi su zuba mishi sede Momy ko kuma in bata nan ya jira har lokacin dazata zo ..in kuma a England ne to wannan shi ze zuba abunshi..
Cike da shagwaba tare da turo baki dan bataso ya katse mata kallon ba .....
Tana zuwa ta bude ta zuba mishi ...ta kama hanyar komawa ...yace ke zonan ...ya zare mata ido yace zauna kici maza ...ganin ta saka abincin gaba ta kasaci yace ci mana...
Dan kadan ta taba ta tashi ta koma fallon .....
Bayan ya gama shima falon ya zauna tare da canza tasha zuwa discovery ch .....tun tana kallo har bacci yayi awon ga da ita...
Shima sha daya nayi ya kashe komi tare da daukanta ya nufi daki da ita...
Love you all
Fasma
Ahmed Gumel
[9/2, 9:53 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚_*
[9/2, 9:57 AM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪
Chapter 24 · 0% Book details